Mai Martaba ya ce, "Subhanallahi lafiya? Ku kaita Asibitin mana,me yasa za a kawota nan?"
Uwar Soro ta ce, "Ranka Yadaɗe ita ta nemi alfarmar afara kawota nan din tukunna kafin mu wuce asibitin."
Tana karasa maganar Adeel na shiga cikin Fadar.
Cikin radadi da jin ciwo Safina na hawaye ta ce, "Neman gafararku ta fiye mun komai a yanzu, domin ina ji a jikina cewa mutuwa zanyi inna mutu ba tare da kun yafe mun ba shine babban tashin hankali ga rayuwata, lallai na san da cewa akwai abun da na aikata na son raina wanda na. . .