Skip to content
Part 30 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Mai Martaba ya ce, “Subhanallahi lafiya? Ku kaita Asibitin mana,me yasa za a kawota nan?”

Uwar Soro ta ce, “Ranka Yadaɗe ita ta nemi alfarmar afara kawota nan din tukunna kafin mu wuce asibitin.”

Tana karasa maganar Adeel na shiga cikin Fadar.

Cikin radadi da jin ciwo Safina na hawaye ta ce, “Neman gafararku ta fiye mun komai a yanzu, domin ina ji a jikina cewa mutuwa zanyi inna mutu ba tare da kun yafe mun ba shine babban tashin hankali ga rayuwata, lallai na san da cewa akwai abun da na aikata na son raina wanda na kara bawa kaina gudunmawa wajen gurbata rayuwata duk da cewa mahaifiyata da mahaifina sune silar komai amman nima ya kamata ace na rike maraicina da karban kaddarata tare da jin cewa nima zan iya rayuwa kamar kowa, ban yi amfani raunina na ‘Ya Mace a hanyar da ya dace ba ko kadan, Kuma babban kuskuren da nafi tafkawa shine kokarin ruguza rayuwar Yareema kamar yadda tawa take a ruguje,na bi son zuciya da rudun duniya, idanuna sun rufu bana ganin komai, wanda babban abun takaicin shine wai mahaifina ne ke bani kwangilar kwanciya da wani Ɗa namiji, kuma a karshe da shi na kwanta har ya mun ciki, gani da cikin Ɗana, Ɗan Mahaifina, kuma kanina.” Ta yi shiru tana kuka mai tsuma zuciya kafin ta ci gaba da fadin.

“Addua nake a kullum kan Ubangiji Allah ya yafe mun kuma suma iyayena Allah yafe masu ya ganar da su, shigowata cikin wannan Masarautar babban darasi na dauka arayuwarta, na tsorata da lamuran mutane Mussaman na mahaifiyata da take shiga ta fita ta duk wata hanya ba tare da shakka ko shayi ba, cikin jikina bana Yareema bane, Mahaifina ne ya yi mun, domin duk asirin da akai na ganin cewa Yareema ya kusanceni baya taba iyawa, Don Allah ku yafemun ko zan samu kwanciyar hankali bayan raina ina ji araina bazan ci gaba da rayuwa ba, ki yafe mun,Don Allah ku yafe mun, duk batutuwan Yareema ya mun ciki wallahi shirin Fulani Kilishi da mahaifiyata ne,ku yafe mun, Don Allah ku yafe mun.”

Tana fada hawaye na kara fita,jini na kwarara ta ƙasanta.

Kara fadi take, “Ku ce kun yafe mun Don Allah ku fada.”

Wani irin tausayi ta basu don duk wanda ya ganta sai jikinsa ya yi sanyi.

Jiki a mace Adeel ya ce, “Ni kam na yafe.”

Gaaji na kallonta ita ma ban da hawaye babu abun da take.

Mai Martaba ya ce, “Ku kaita asibiti cikin sauri,Ku yi sauri In Sha Allah zata rayu.”

Kokarin fara fita da ita sukai, jini kamar ana kara turosa kara bulbula yake harda Gudaji.

Salati ta fara tana kaiwa karshe kuwa numfashinta ya dauke gabadaya ba tare da ta haife abun da ke cikinta ba.

“Innalillahi wa inna ilahir raji’un ta rasu.” Uwar Soro ta furta.

Gabaɗaya Jikin kowa dake Fadar Ya yi sanyi ban da addua da fatan Alkairi babu abun da ake yi mata, take aka fara shirin yi mata wanka aka yi mata sallah sannan aka kaita makwancinta.

3 Days Letter

An ci gaba da shagalin bikin Suna, Adeel tun ranar Rasuwar Safina bai kara ganin Gaaji Uwar Soro ta kumsheta adaki Ana jego.

Tunda ya tashi ranar ya kudiri niyar sai ya shiga Ya ga Gaaji ta ta halin ƙaƙa ne don shi ya gaji da yin kewarta.

Yana yin Wanka ya fito ya tsaya kofar Part dinsa, har sai da ya tabbatar Uwar Soro ta shiga Part din Fulani Babba kafin ya saci hanya ya shige.

Zaune take kan gefen gado tana Feeding Princess, ji tayi kawai an cafke Breast ansa a baki.

Shagwaɓe Fuska zata yi kuka, “Don Allah ka bari wallahi na zafi suma din ya na kare bare kuma kai.”

Ya kalleta ta saman idonsa, Breast din na bakinsa ya ce, “Nina fi su bukata ai yanzu Almost 3 Days ace ko ganinki an hanani yi kuma kema tsabar bakya son ganina ne ai don mugunta, don haka abarni in sha Rabona.”

Har lokacin Breast din na bakinsa ya zame Princess gabadaya daga jikinta ya kwantar kan bed sannan ya gyara kansa ya kwantar a cinyarta.

Murya a sanyaye ya ce, “I So Much Miss You Zizi.”

Yadda ya furta maganar sai da taji a cikin jikinta ita ma jiki ba kwari ta ce, “I Miss You More.”

“Shine baki sato hanya kinzo na ganki ba ko?” Ya fada.

Gaaji ta ce, “Umm taya zan fita ko parlour fa ba a barina Inje wai kar sanyi ya shiga jikina.” Ta fada tana shafa gashin kansa.

Adeel ya ce, “To wai ba a gama wannan mugun wankan bane? Nikam fa na gaji,ko kuma inzo in sace ki mu gudu kawai,ni da matata kawai a dunga mun gadara da iko.”

Gaaji ta ce, “To ba gyara ma matar taka ake yi ba.”

“Wani gyara? Ni bana son gyaran ni abani abata in na bata ta ma zan gyara da kaina.” Ya fada.

Cikin gatsali Gaaji ta ce, “to ko za a gwada ne?”

Kafin ta karasa rufe baki Adeel ya tashi ya na bin jikinta kansa yasa daidai wajen Wuyanta yana shakar numfashi.

Yadda yake bi mata jiki a hankali take yanayinta ya canja jikinta ya mutu.

Jin hannunsa tayi yana kokarin janye mata zip har kasa.

Cikin sanyayyar murya Gaaji ta ce, ” Ruhiy Please… Tana kokarin janye jikinta

Adeel ya ce, “ni fa mijin ki ne ko kina so in shiga halaka ne?”

Gaaji ta ce, “aa, But Please kar ka…

Sai kuma ta yi shiru.

Adeel ya ce, “ni ba komai zan miki ba,inji dumin jikinki ma a yanzu kadai ya wadatar nayi kewarki sosai.”

Romance din juna suka fara yi bilhakki da gaskiya sai ga Uwar Soro ta fara Nocking kofa.

“Uwata lokacin shiga ruwanki ya yi maza bude, na san in ba na tsaya ba salamce ruwan zakiyi.”

Ido cikin ido suke kallon juna ita da Adeel duk sunyi kuru-kuru.

Uwar Soro ta kara fadin, “Kina Mene ne wai baki ji ni bane?”

Sai a lokacin Gaaji ta amsa, “Naam gani nan.”

Da sauri ta budewa Adeel Wadrope ya shige ciki Kulum ta rufe sannan ta budewa Uwar Soro ta shiga tana, “Ince barci kika fara ne?”

Gaaji kawai ta girgiza mata kai alamun mara gaskiya dai.

Suna shiga tasata ta shiga ruwan Dumi na yan mintuna sannan ta bata wani ruwan mai dumi na ganyan magarya, bagaruwa da lalle, tayi Tsarki sannan ta bata wani Pad din ta canja.”

Suka fito tana fadin, “kin ga hakan ba karamin amfani garesa ba, shi zai taimaka wajen dawo miki da martabarki, mata da yawa abun da suke sake da shi kenan in sun haihu baza su tsaya a gyara su bare su gyara kansu ,shi kuwa namiji bai san wannan ba, in yajiki ba yadda yake so ba daga lokacin zaki fara Fuskantar matsalolin gidan aure komin son da yake miki zai iya sa hakan a gefe, duk da cewa dai ba fata ake ba, don haka babban gatan da duk wata ‘Ya mace zatayiwa kanta inta haihu shine gyara ta tsaftace jikinta ba sai ta je ta yi biye-biyen kayan matan da a karshe zai iya yi mata illa ba, sannan kar kiyi wasa da shan ruwan kanun farin nan ma,basai nace miki kiyi ba ya kamata ace yanzu wani abun kafin in tuna har kinyi saidai ki ce mun ai Kinyi kawai, kayan fruit ma tun ba yanzu ba ina fada miki kada kiyi wasa da cinsu su zame miki abubuwan taba baki sosai duk jikinki zaibi kuma ya gyara miki, da juice dinki da kike sha da rana na kwakwa,Cocumber, Da Dabino, kin ga ma na mata kuma baki tuna mun ba ba ki shafa Miski dinki ba,kin ga halin naki ko? Ana ce miki a karasa katsina kina cewa ke a daura zaki zauna.”

Gaaji tayi dariya, “In Sha Allah bazan kara mantawa da komai ba daga yanzu.”

Uwar Soro ta ce, “Da dai yafi miki.” Har ta juya zata fita ta koma.

“Na manta fa dazu an kawo kayan da zakisa ranar suna kina barci nasa cikin Wadrope Bara in dauko in da gyaran da za ayi sai ki fada tun yanzu.”

Uwar Soro ta karasa maganar tana zuwa daidai Wadrope din da Adeel ya shiga.

Jiki na rawa murya na rawa Gaaji ta karasa ta tsaya bakin Wadrope din tana, “Ai…ai… Na duba har ma ….na.. ba.na..gwada.”

Uwar Soro ta kalleta cikin mamaki.

“Lafiya dai ko?”

Gaaji ta ce, “Aaaaa.eeee.”

“Kin ga komai ya yi ba matsala?”

Girgiza mata kai kawai tayi.

Uwar Soro ta ce, “Alright shikenan.” Ta nufi kofar fita.

Tana fita Gaaji ta fara wata doguwar ajiyar zuciya zata bude Adeel.

Tana sa hannu a Wadrope din Uwar Soro na kara turo kofa

Da sauri ta hankada ta kara rufewa ta jingina a jiki.

Dressing Mirrow taje ta aje kwalbar miski tana, “na manta har na fita da shi a hannuna.”

Gaaji bata ce mata komai ba.

Tana fita Gaaji ta kara doguwar wata ajiyar zuciya.

Ta bude Adeel ya fito duk gumi ya gama mamayesa.

Numfasawa ya yi,yana, “Oh Allah Nikam na shiga Ovun ni da matata amman an sani buya kamar wani kwarto.”

Gaaaji ta tun tsire da dariya, “Yoo ai kanin gwartonne tunda ba a baka ita ba ancr kayi Hakuri ka ki.”

“Au ko? To wallahi in kikai wasa sai na aikata abun da ake gudu a wannan gadon iyakaci in akazo aka gani ai dole a bani matata ko?”

Gaaji ta ce, “Aa nikam rufamun asiri ka tafi kawai.”

Adeel ya ce, “Na fasa ba inda zani yau kafarki kafata.”

Gudu ta fara yaje ya damkota.

Yana riketa sai ga Uwar Soro ta bude Kofa ta shigo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 29Auren Wata Bakwai 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×