Skip to content
Part 4 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Rufe idonta tayi tana kankame jikinta tamkar za ta suma ta yi wata irin gigitacciyar ƙara.

Prince Adeel ya kalleta ya kauda kai, yaja towel din sa ya daura, yana kokarin sa kaya, ci gaba da ihun tayi kamar wacce aka sawa saban batir, har cikin dodon kunnensa yake jin saukan kararta.

Cike da takaici ya karasa inda take yana daka mata tsawa.

Maimakon ta nutsu tsawar da ya mata yasa ta ci gaba da kwallara ihu tana kokarin shidewa.

Rufe mata baki ya yi da hannunsa yana mata alamar tai shiru.

Ita kuwa ido ta kafa masa suna kallon juna, aransa yana sakawa, “anya wannan yarinyar na da hankali kuwa? Watakila ma mahaukaciya ce ga dukkan alama.”

Ita ma a zuciyarta ta ce, “cab lallai wannan ƙasurgumin ɗan ishka ne, kawai ya zauna tsirara ba kaya, Aradun Allah watarana na kara ganinsa haka nan sai na yanke masa wannan jelar mai kama da beraye.”

Kusan minti ɗaya suna haka kafin ya saketa yana sauri ya shige toilet zuciyarsa na tashi, wanke hannunsa ya yi, yana jin kyamarta dama bai kai hannunsa bakinta ba don gabadaya yanzu a tsarge da kansa yake.

Har zai fita, haka ya koma ya kara wani sabon wankan amman duk da haka hankalinsa bai kwanta ba, hannunsa ji yake kamar har yanzu da yawunta a jiki.

Ita kuwa yana saketa, ta falfala aguje ta koma bangaren Uwar Soro tana haki kamar wacce ta dibo kaya.

Da sauri ta riketa tana, “Ya Salam, Gaaji ina kika je? Ba wanda dai ya ganki ko? Ki daina fita in kina fita kamaki za a yi a kulle.”

Gaaji ta ce, “ni fa gun Yareema naje in ce masa ina Baffana ya jikinsa, shine fa kawai na gansa a tuɓe aradun Allah Yareema dan iska ne ashe, kin gansa kamar wani Dodo cab.”

Uwar Soro ta ce, “Kul kada in kara jin hakan a bakinki kinji.”

Cuno baki tayi tana, “To wayace ya zauna ba kaya, ai yan iska ne ke zama tsirara dai, ga shi fa wani katon garde da shi abun tsoro ni Allah sa ma kar nayi mafarkinsa in kasa barci.”

Ta fada tana rufe idonta.

Uwar Soro ta yi dariya kafin ta ce, “Na ji dai, daga yanzu in zaki je bangarensa kina fadamun kuma sai kin kwankwasa kofa ya baki izinin shiga kafin ki shiga.”

“Ni ban kuma zuwa masa ma inje inga abun da zai makantar dani in daina gani ana cemun makauniya, shi kenan in kasa ganin Baffana.” Gaaji ta fada tana dafe haɓa.

Rike mata hannu Uwar soro ta yi tana, “to na ji, yanzu kizo muje in miki wanka, kuma kin ga wannan kan naki ma dole a wankesa arage masa dauda a gyara sai in miki kitso.”

Take Gaaji ta bata rai tana hada girar sama da ƙasa ta ce, “ni fa nace miki bana shon wankan nan bana sho nikam fatar jikina zata zama roba, kuma ta dafe.”

Uwar Soro ta ce, “ba zata dafe ba fa zata yi kyau ne tafi yanzu haske kuma karfin ma zaki kara ne, ki zama yan mata Sosai.”

Uwar Soro ta ce, “aiko in baki yarda anyi wankan nan ba bake ba abincin rana irin me dadin nan.”

Ko magana Gaaji ba tayi ba ta fara cire kaya tukun ta ce, “mu je kin ji, Wallahi ba zan iya zama da yunwar ga ba, gwanda kawai ayi wankan nikam na hakura fatar ta ta kodewa karfin ma ya tafi amman dai abani abinshin in ci Don Allah.”

Da kanta ta shiga toilet din, Uwar Soro ta mata wanka, ta dan wanke mata gashi aka rage masa dauda dan ba za dai ace ya fita duka ba, dan kwana biyun nan har ta fara chanja kala haskenta da ya dafe dan dauda har ya fara dawowa kyanta na asalin bayyana.

Dole wasu kayan Fulani Uwar Soro tasa aka nemowa Gaaji domin duk kayan da ta bata tasa cewa take ita bazata sa ba, ba shine kayan su ba.

Yau ya kasance ranar Juma’a wacce ta kasance a kowacce Juma’a Yareema na zuwa su gana da Mai Martaba kafin su shiga Masallacin Fada suyi sallah tare.

Hakan ne ya wakana kuwa yana fitowa daga wanka ya shirya, Shamaki na tsaye yana jiran fitowarsa yana fitowa suka nufi Cikin Fada tare.

Bayan Shamaki ya raka Yareema fada dukansu suka fice waje kamar yadda aka saba.

“Barka Da Safiya Ranka ya dade.” Cewar Prince Adeel.

Mai Martaba ya ce, “barka dai Yareema, ina fatan komai yana tafiya daidai ba tare da wata matsala?”

Prince Adeel ya ce, “AlhmduLillah komai na tafiya daidai kuma abisa tsarin da ka umarta.”

Mai Martaba ya saki murmushi kafin ya ce, “Ma Sha Allah, wato kai dai ba zaka taba barin wannan shigar kasar wajen ba, ka riga ka gama sabawa da hakan ko ince kafi jin dadin hakan ko?”

Shiru Yareema ya yi kansa a kasa yana sakin Murmushi.

Mai Martaba ya ce, “kodayake nima nayi na gaji na hakura watarana da kanka zaka daina sawa har ma ka manta da yadda ake sawan.”

Shi dai Yareema bai ce komai ba sai murmushi.

Shi kuwa Mai Martaba kara jin so da kaunar ɗan nasa ɗaya tilo a duniya yake har cikin ransa, a zuciyarsa shi ma bai da muradin da ya zarce ace Yareema ya yi aure ya haifa masa jika ya gani tun yana raye, amman sam baya iya masa maganar hakan aransa ji yake cewa haka ba karamin takura bane, kuma babu abun da yafi so fiye da farincikin Yareema zai so ace da kansa ya ji sha’awar kasancewa mai iyali.

Sun dan taba hira daidai gwargwado kafin suka nufi masallaci suka saurari Huduba sannan suka yi sallah.

*****

Nasmah na Tabbatar da cewa an idar da sallah ta nufi kitchen kai tsaye ta ce wa Magajiya, “Ina abincin Yareema?”

Magajiya ta ce, “ga shi can ina jira Uwar Soro ta turo a daukan masa ne.”

“Aa ni zan kai masa yau, ya ce in kai.” Ta karasa maganar tana kada kokarin daukan abincin.

Daga nesa taji tsawar Khalesa na fadin, “dakata! Kada ki kuskura ki yi gigin daukan Abincin Yareema domin yau Ni nake da alhakin kai masa.”

Nasmah ta ce, “What? Ban gane ba, kamar ya?”

Bige hannun Nasmah, khaleesa tayi akan tiran abincin tana janyewa, “eheen abun da kunnenki suka jiyo shi nake nufi, Ai babban Ɗa Sai babbar ‘Ya kamar yadda nake Babbar ‘Ya mace a Masarautar nan haka zan kasance mata ga Yareema atakaice dai Gimbiya duk da kin sani gwanda in kara jaddada miki don kuwa na lura da cewa kunnen kashi gareki.”

Ta karasa Maganar tana kare mata kallo sama da kasa tana wani irin juyi.

Magajiya ta ce, “Amman dai dukanin ku kun san cewa babu mai alhakin kaiwa Yareema abinci ba tare da izinin Uwar Soro ba ko?”

Khalesa ta ce, “agunki kenan don ni ai a yanzu nafi Uwar Soro kusanci ga yareema zan gansa a lokacin da na so kuma nayi niya don haka ni zan kai abincin Yareema ba wanda ya isa ya hanani kaiwa.”

Nasmah ta ce, “ai bai zam mallakin ki ba a yanzu don haka kowacce na da hakkin amfani da damarta duk wacce tai nasara shi kenan.” Ta karasa magana tana kokarin fisgewa.

Wani azababben mari Khalesa ta sake mata a fuska da sauri Magajiya ta karasa inda suke daidai da lokacin da Jakadiya ta shiga kitchen din.

“Kai kai kai.. mai zan gani haka me ke faruwa ne?” Jakadiya ta fada.

Nasmah na kuka ta ce, “na zo daukan abincin Yareema ne zan kai masa Khaleesa ta kwace wai ba zan kai ba kuma ta mareni.”

Khalesa ta ce, “Karya kike karamar munafuka.”

“Aa fa ba ayi haka ba kema dai Nasmah kin fiye tsaurin ido taya Khalesa zata kaiwa Yareema abinci kice ke zaki? Ai ido ba mudu ba amman yasan kima, ita da muke fata nan da kwanaki kadan muji ta zam gimbiya, aa aa maza Khalesa je ki kai wa Yareema abinci.”

Kuka Nasmah ta kara fashewa da shi ta fice da gudu a kitchen.

Khalesa tayi tsaki tana, “kya yi kya gama Yareema dai kam nawane.” Suka hada ido da Jakadiya suna sakewa juna Murmushi.

Nasmah na zuwa ta fada jikin Hajiya Maimuna tana kuka tana fada mata abun da Khalesa da da Jakadiya suka yi mata.

Hajiya Maimuna ta share mata hawaye tana murmushi, “Hakan ne ya saki kuka? Mene ne na kuka akan haka? Lallai baki tanadi zuciyar da zaki tallafi soyayyarki ba, ki zam jaruma, mai maida komai ba komai ba koda kuwa komai dinne, ki sa aranki cewa indai Yareema mijinki duk rintsi duk wuya babu fashi sai ya kasance naki, rabon kwado ai baya taba hawa sama, ko ya hau ma dole ya fado, don haka ki kwantar da hankalinki.

Fita tayi tana tafiya tana rangwada tamkar ba zata taka kasa ba, tana zuwa tayi knocking shiga bangarensa, Shamaki ya fito ya sanar da ita yana barci ta bada abincin a ajiye masa.

Khaleesa ta ce, “ka tashesa ka ce nice ina son ganin sane don Allah.”

Shamaki ya ce, “Kin san dai in ba wani uzuri babba ba ba damar tada Yareema a lokacin da yake hutawa mussaman rana irin ta yau.”

“Ni dai don Allah yau kadai amun wannan alfarmar.”

Komawa ciki shamaki ya yi, ya yi dace kuwa yana zuwa ya tarar da Yareema zaune yana danna laptop ga dukkan alamu yana duba wani abu mai mahimmanci ne.

Shamaki ya ce, “Ranka Ya dade Khaleesa ce a waje ta kawo ma abinci.”

“To ka karba mana.”Yareema ya fada hankalin sa na kan system din dake gabansa.

Shamaki ya kara da, “Aa ta ce wai kai take son gani abata izini ta shigo.”

Da Okay kawai Yareema ya amsa, Shamaki ya fita ya cewa Khaleesa ta shiga.

Tana shiga ta ajiye Abincin kan daining sanan ta karasa daf inda yake ta zauna tana, “Good Afternoon Darling Prince.”

“Afternoon.” Ya amsa kawai.

Shagwabe fuska ta yi tana, “I Call You but you didn’t pick Why?, i just want to hear Your Sweet Voice, ni kam ko laifi nama ne?”

Tana ta surutun ta yana ji amman hankalin sa baya kanta kuma bai da niyar bata amsa.

Ta ci gaba da magana. “Wai yaushe zaka gabatar masu da cewa nice zaɓinka ne? Nikam na matsu ina so ayi a daura mana aure.”

Sai a lokacin ya juyo ya kalleta cike da mamaki ya ce, “Aure? Dawa?”

“Da kai mana, ka san dai nice babbar ‘Ya mace kamar yadda kake namiji so mu muka fi dacewa da juna ni yanzu ma da zaka barni dawowa nan part din zan yi ya yi mun kyau gaskiya in munyi aure zanji dadin zama anan sosai.”

Ganin bai da niyar kara kulata ta fara mannewa a jikinsa tana magana cikin sanyayyar murya.

Prince Adeel ya yi saurin…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.1 / 5. Rating: 15

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 3Auen Wata Bakwai 5 >>

2 thoughts on “Auren Wata Bakwai 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×