Skip to content
Part 7 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Tana bin jikinsa.

Ya ce, “Ki dan gyara mun kwanciyar, ina so in yi barci.” Ya fada murya a ƙasa cikin yanayin galabaita.

Tallafa masa tayi ya kwanta, ruf da ciki, nan take wani irin barci ya yi awun gaba da shi, tamkar matacce.

Kamar wasa ta kwanta ita ma tana jira ya farka amman ina, babu alamun motsi bare tashi har dare ya fara tsalawa wajen karfe biyu da wani abu.

Jijjigashi ta fara yi tana, “Prince Ka tashi mana, wannan wani irin barci ne kuma, ka tashi Please.”

Bai ma san tana yi ba hasali ma nauyinsa duk ya sake yana barcin da kyar take iya girgizasa.

Ganin ba ta da yadda zata yi ga dare ya yi bata so ta kwana a samu akasi wani ya ganta haka ta tashi ta fita zuciya fal takaici da bakin ciki.

Tana shiga Motarta ta, ta nufi hanyar gida rai ɓace.

Shigar ta kenan wayarta ta fara ringing dauka tayi a dayan bangaren aka ce, “ina fatan komai dai ya tafi daidai?”

Tsaki Safina ta yi ta ce, “wani daidai? Da farko naje kamar abun arziki naga alamun ya ci abun da zai saka sa aikata abun da muke so dole, amman kuma sai barci ya dauke sa nan take ta yadda ba zan iya aikata komai da kaina ba ma, don nayi kokarin hakan amman yanayin kwanciyar da kuma yanayin yadda surar jikinsa take na gagara aikata komai, anya ba kuskure aka yi aka sa masa maganin barci madadin namu ba?”

“Ta ya zaki ce maganin barci kuma? Abun da ni da hannuna na zuba kuma ni na siyo, ni na fara tunanin kema dai kawai da naki ba kya son ayi abun nan kowa ma ya huta, kuma kin san cewa nawa mai sauki ne a karshe ke ce da reward din samun nasara in dai hakan ya tabbata.”

Cikin Fushi Safina ta ce, “Oh ka dawo da laifin gareni kenan? Duk kokarin da nake a banza? Alright shi kenan ka gwada wata mana in za ta iya har ma ta jure miskilancin wannan mutumin gwanda ma ni ai.”

Ya ce, “Na ji yanzu meye kike ganin mafita tun an kara samun wani tsaikon?”

Safina ta ce, “akwai bukatar a kara komawa ta inda aka hau domin tanan ne kadai za a sauka, yana da taurin kai sosai kuma babu shakka akwai wani abu tattare da shi da dole sai an kawar kafin akai ga cin nasara.”

“Umm tabbas yanzu nima na fahimta kuma in dai hakanne za a yi gaggawar tabbatarwa duk wannan taurin kan da duk wani abu da yake ji da shi sai ya gagaresa ba matsala ki huta yanzu kam ba za ki kara kai kanki ba har sai ya neme ki.”

Yana karasa maganar ya katse wayar.

Safina kuwa gyara kwanciya ta yi abunta sai barci.

Karfe hudun dare Prince Adeel ya farka ban da zufa babu abun da ke keto masa, ya tashi ya yi wanka sannan ya dauro alwala.

Salloli ya fara yi har sai da aka kira sallar asuba ya fita yaje masallaci ya yi.

Gaaji na tashi daga barci ta ce lallai ita baza ta yi wanka ba sai Abokinta Adnan ya zo.

Uwar Soro ta rasa yadda zata yi a karshe dai sai da ta kira Adnan suka yi waya da ita ya ce in bata tsaya an mata kwalliya ba, ba zai zo gunta ba kuma ya mata alkawarin zai fita da ita ya siyo mata kaya masu kyau abubuwan ci na dadi.

Da tsallenta ta ce, “yanzu zan yi wankan kuma zan tsaya amun da kyau in fita ka yi sauri kazo fa.”

Tunda tayi wanka ta tsaya ta window tana leken ta inda Adnan zai bullo har wajen karfe uku.

Da kyar Uwar Soro tasa ta tayi sallah da dabarar cewa in bata yi sallah ba ma Adnan ba zai zo ba.

Duk da cewa sallar ta ta ma fanko ce domin kifawa kawai take tana tashi, a hankali tana dan nuna mata wasu abubuwan tana gyarawa.

Sai wajen karfe biyar Adnan ya shigo, bai ma je gun Yareema ba gunta ya wuce kai tsaye.

Tana ganinsa ta bata rai, “Ni nayi fushi, na daina shonka kuma ma mun kunce.” Ta karasa maganar tana mika masa hannu alamar su kunce.

Durkusawa gabanta Adnan ya yi ya kama kunnen ya ce, “Afwan Gaaji Beauty kin ga na kama kunne na ko sai na mari fuskata?”

A shagwaɓe ta ce, “E amman kar ka mara da zafi a hankali kuma sai kace zaka goyani yadda Baffana ke mun, kuma zaka na zuwa guna da wuri.”

Marin fuskarsa ya yi yana dariya ya ce, “To na mara kuma zan goya ki in mun fita, sai kuma me zan yi yanzu ? Kin ga baki yi murmushi ba.”

“Umm umm ni na daina ma murmushi ai kuma?” Gaaji ta fada.

Adnan ya ce, “in dai baki yi murmushi ba, to ni kuka zanyi ma.”

Da sauri tayi murmushi tana, “tom nayi kar ka yi kuka.”

“Yauwa good girl bara in nuna miki wani abu sai mu tafi ko.”

Ta ce, “Guduo gu.”

Dariya Adnan ya yi ya ce, “ni fa ba gudou gu bane, Good Boy zakina cewa.”

“Tom Gudu bu.”

Dariya yayi kawai yana girgiza kai.

Wayarsa ya ciro ya danna video call A WhatsApp likitan da ke kula da Baffanta ne ya daga suka gaisa sannan ya bukaci da anuna masa shi.

Nuna wayar ya yi inda Baffan Gaaji yake, yana barci hankalinsa kwance jikinsa har ya fara canjawa.

Tsabar mamaki Gaaji ta kasa magana kusan minti daya kawai ta washe baki tana kallon Baffanta nan take Farinciki ya gama bayyana a fuskarta ta ce, “Baffa am Noi ɓanduma? Volwunam,. Anani koiɗum ko?a umman a vawami ko? (Ya jikinka? Ka yi mun magana mana, ka ji sauki ko? Za ka tashi ka goyani?).”

Ta ga bai yi magana ba kallon Adnan ta yi ta ce, “Ka ce ya mun magana ina sho nayi magana da shi.”

Adnan ya ce, “ba ki ga barci yake ba? Tunda aka masa aiki bai farka ba sai ya huta sosai inya farka sai mu kara kira ko.” Ya karasa maganar yana yiwa likitan Sallama ya katse wayar.

Gaaji cikin yanayin Farinciki ta ce, “Baffana zai ji sauki.”

Adnan ya ce, “In Sha Allah yanzu ta shi muje.”

Suka shiga Parlourn Uwar Soro suka mata sallama sannan suka fita tare.

A mota ya sata tana ta kalle-kalle da tabe ya koma yawa Yareema magana.

“In ba abun da kake, kadan raka ni wani waje mana?”

“Okay.” Kawai Yareema ya amsa.

Ya canja kaya ya fito.

Yana zuwa ya shiga gaban motar, Adnan ya ja su suka dau hanya.

Daga kansa da zai yi a madubi ya ga Gaaji nata washe baki.

“Adnan! Kana cikin hankalinka kuwa, Wannan yarinyar fa?”

Adnan ya ce, “za muje Shoprite ne ta sha iska taga abubuwa sannan kuma ina so in mata siyayyan kayan sawa.”

“Me zai sa baza ka bada a siyo ba har sai mun fita tare?” Prince Adeel ya fada.

Kafin Adnan ya yi magana karaf Gaaji ta ce, “Eh din sai anje dani din ina ruwanka ai shi ba dan ishka irinka ba ne, kuma ina shon shi.”

Dafe kai Adeel ya yi don takaici ya ma rasa abun fada.

Adnan ya ce, “zuwa da kanmu da itan ne zai fi wani inya fita da ita za a iya samun matsala.”

Daga nan Adeel bai kara cewa komai ba, ban da zafi ba abun da kirjinsa ke yi masa ji yake kamar ya dauki Gaaji ya jefar tsakiyan titi domin ya tsani rashin kunya a rayuwarsa, ita kuma ga bakinta kamar barin jinin magana da rashin kunya yake.

Ita kadai da Adnan suke ta surutunsu har suka isa Shoprite din.

Tare suka fita duka, suna shiga Suka fara cinkaro da irin manyan Teddies din nan da mutane ke shiga ciki.

Ganin abu kamar mutum yana motsi da rawa yasa Gaaji ta rikice tuni ta rufe ido tana ihu bata san lokacin da ta kankame Prince Adeel ba.

Saukar wani zazzafan mari kawai taji a fuskarta…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 6Auren Wata Bakwai 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×