Skip to content
Part 8 of 31 in the Series Auren Wata Bakwai by Xayyeesharthul-Humaerath

Marin ya shiga jikinta sosai sai da taji canji tun daga kwakwalwar kanta har kafa, wani guntun suma ne ya risketa take hannunta rike da kumatu ban da hawaye ba abun da take kwalalarwa, tuni fuska ta damule da hartsin majina da hawayen dake artabu, tsigan jikinta duk ya tashi daga nesa ana iya fahimtar cewa ta shiga wani yanayi da ya firgitar da ita.

Adnan ya ce, “haba Prince? Wai me yasa kake yiwa yarinyar nan abubuwan da basu kamace ta ba, don kawai ta rike ka sai ka mareta?”

Prince Adeel Muhammad Rohaan Idanunsa sun fito sosai wanda ya kara bayyanar da bacin ransa karara wanda ana iya jiyo sautin bugawan zuciyarsa.

Kau da kai ya yi ba tare da ya takanwa Adnan ba ya koma mota kawai.

Yana shiga ya dafe kansa yana wani irin huci kaman bijimin Sa.

Adnan ya kalli Gaaji tausayinta ne ratsa masa zuciya a sanyaye ya ce, “ki yi hakuri kin ji ba zai kara marinki ba, bude idonki.”

Ya karasa maganar yana miki mata hankicif ta goge fuska.

A hankali ta bude idanun domin har yanzu taurari basu daina yi mata shawagin zafin marin da taji ba.

Cikin shashshekar kuka ta ce, “Mugu ne, kuma Allah zai saka mun, mai idon kuliya kawai ni ba ruwana da shi.”

Adnan ya ce, “na ji dai yanzu share hancinki muje ciki in siya miki kayan kawai sai mu koma gida ko?”

Ta girgiza masa kai tana share hanci, tana gamawa suka shige cikin shoprite din, tare suke Adnan ne da kanshi ke zaɓa mata kaya, tana bin bayansa da kalle-kalle, Wani Pad ta gani kato ta dauka ta na, “Aboki ka siya mun wannan burodin zai yi dadi ko? Baba Uwar Soro na ba ni irinsa ai.”

Adnan na karba ya ga Pad ne maimakon Bread din da take fada ya ce, “Aa fa wannan ba Bread bane Gaaji wani abun ne daban.”

“To mene ne in ba burodi ba? Aradun Allah burodine ai ko lokacin ma da Baffana yana siyomin in ya shigo birni ni dai ka siya mun.” Ta fada tana taɓe fuska.

Adnan ya karba kawai yasa cikin besket din ba tare da ya ce komai ba.

Kara dauko wasu guda biyu tayi ta ce, “Yo ai Aradu wa inshen sun mun kadan akara wa innan su zama uku yau inta shin abuna in ji dadi.”

Shi kam dai bai ce mata komai ba tasa a ciki.

Kaya ya zaɓa mata daidai wa inda zasu mata dogayan riguna da wasu mini hijab, chocolate, sweet da su biscuit ma kamar wa inda zasu bude provisions ban da washe baki ba abun da take tana jin dadi.

Sai da suka gama tas kafin suka koma mota, Prince na ciki yana danna waya, sai da Adnan ya budewa Gaaji ta shiga sannan shima ya shiga, tana shiga tayi tsaki da kwafa, ganin Adeel bai ma san tana yi ba ta dunga dage tana harararsa da murguda masa baki.

Kamar ance ya kalli morrown gaban motan suka hada ta takarkare tana murguda masa karamin bakinta ta ko ina a fuskarta ba inda baya motsi.

Kawar da kansa ya yi kamar bai ganta ba don ya fara fahimtar indai ya biyewa wannan yarinyar sai ta mai dashi karamin mahaukaci.

Kan su isa Fada an fara kiran sallan magriba, haka yasa Adnan ya na aje mota ya bude mata cikin sauri ya ce tazo ya maida ta ciki gun Uwar Soro tun kafin wani ya gansu.

Ita kuwa Gaaji tsayawa tayi lallai fa sai ta ci gaba da murgudawa Adeel baki kan ya fito a motar taje tana kokarin tura kanta daidai da lokacin da yake kokarin turo kofar ya fito bai ma ganta ba.

Da sauri Adnan yaja hannunta yana, “kina so muyi fada ko? Baki ga lokacin sallah ya yi bane? Oya muje ki shiga ciki muma zamu shiga Masallaci.”

Shigewa tayi da tarin ledar kayanta guda biyu tana juyowa tana daga masa hannu a dole bye bye.

Aiko tana shiga ciki ta baza kayan nan kaf a kasa tana murna take ta cire kayan fulaninta tasa wata Abaya ta mata kyau Sosai, Uwar Soro kuwa binta da kallo take kawai na mamaki ganin yau da kanta ta cire kayan gadonta tasa wani ah lallai Gaaji an fara canjawa.

Ita kadai tana ta sambatu, “Ai aradu ba a tabani a zauna lafiya she na gyarawa mutum hankali tunda shi an ishka ne kuma mugu, shi kam Abokina ba ruwansa ɗan albarka she siyamun kaya yake.”

Pad dinnan ta ciro ta jera gabanta tana, “Yauwa wannan Burodin zanci yau Baba ba zan ci abinshinki ba abokina ne ya sayo mun mai dadi.”

Uwar Soro ta ce, “Mu ga Burodin naki Gaaji.”

Tashi tayi tana yage ledar ta ce, “Kadan fa zan sammaki ba duka ba, zan shi abina duka ni kadai.”

Uwar Soro na karba ta ce, “Wannan ai Audugace ba burodi ba.”

Gaaji ta karbe abunta tana, “Audugar me? Burodi ne fa aboki ya siyamun.”

Dariya Uwar Soro ta yi ta ce,” na san dai kin fara al’ada to da kika fara jini na fito miki da me kike amfani lokacin kina Ruga?”

Gaaji ta ce, “Ni tsumma nake sawa in tare sai ranar da naga jinin ya dauke sai in Jefar a shara.”

Da sauri Uwar Soro ta riketa ta ce, “Subhanallahi to wannan abun ake sawa ba tsumma ba, kin san tsumma kuwa cuta yake sawa? Zai saki ki yi tsutsa, yana fito miki kuma kina wari a karshe ma ki mutu.”

Nan take Gaaji ta gwalalo ido tsoro ya gama cikata.

Uwar Soro ta ci gaba da cewa, “kin ga shi wannan kullum ma in kina yi a kalla sau biyu ko sau uku ake so kina canja wani, da zaran ya baci ko ya dan dau lokaci ake cirewa saboda gujewa shigar wata cuta kinji ko?”

Jikinta ya yi sanyi ta ce,” ni kam ba zan kara sa tsumma ba kar inyi tsutsa yashin ba ruwana na daina, tun yanzu ma zansa wannan din ya fara tare mun kafin ya zo.”

Uwar Soro ta yi Murmushi tana, “Aa ai sai ya zo ake sawa yanzu zan boye miki kinji baza ki yi tsutsa ba In Sha Allah.”

Sai da Adnan ya dawo ya mata tatsuniya kafin tayi barci kuma ya tafi.

Khalesa ban da zabga kira a waya ba abun da take yiwa Adeel ya ki dauka da ta gaji kawai sai ta nufi bangarensa tana zuwa ta tatarar da shi tsaye da Nasmah suna magana.

Wani irin kallon raini ta bi Nasmah da shi, ita ma ta maida mata da kallon tara saura kwata.

Karasa tayi daf da Adeel ta ce, “Prince na zo gunka ne fa kuma na ga wata.”

Adeel ya ce, “Nasmah ce ai dukan ku ɗaya ne.”

Cikin bacin rai Khalesa ta ce, “Aa wallahi ni da ita ba ɗaya bane kama daina haɗamu ko a shekaru na fita bare kuma batun kasancewa gareka muna da tazarana matsayina daban nata daban, so ta ba ni waje ina so in yi magana da kai.”

Nasmah tayi murmushi kawai tana kallonta.

Prince Adeel ya yi shiru shima ba tare da ya ce komai ba sun maidata fanko kawai.

A harzuke ta kara fadin, “magana fa nake, ke Nasmah wai ba kya ji ne? matarsa na son yin magana da shi?”

“Matata?” Yareema ya fada cike da mamaki fal a fuskarsa.

“Eheen ko ka manta ne?”

Khalesa ta fada cikin isa.

Ya ce, “ke da ita duk daya ne duk abun da zaki fada ki fada gabanta zai fi miki.”

Wani irin fusata Khalesa tayi tana sakin tsaki ta kara bin Nasmah da wani kallo tare da yin kwafa, ita kuwa Nasmah gwalo ta mata da wata irin dariyar mugunta.

Nasmah na ganin Khalesa ta tafi murya a raunane ta ce, “na dameka ko Prince? Sorry Gudnyt ka je ka kwanta ka huta gobe kawai mayi maganar ko lokacin da kake free ka kula da kanka.”

“Alright thanks.” Ya fada kawai ya shige.

Sai da taga shigewarsa sannan ta tafi tana sakin murmishin da ita kadai ta san dalilin sa.

Misalin karfe Tara na safe Gaaji ta sha wanka ta karasa kaya da ɗaya cikin wanda Adnan ya siya mata sau juyi ake, ranar ba fada ta tsaya aka mata wanka tayi brush da kanta, wanke dambun gashin ta ne dai har yanzu taki Yarda Uwar Soro ta taba bare a wanke mata shi.

Daukan hanya tayi bijigun-bijigun zata fita, Uwar Soro ta ce, “Ina zuwa?”

Tunani ta tsaya yi ta tana sakawa a zuciyar ta indai ta fadawa Uwar Soro asalin abun da zata yi ba zata barta ba, can sai ta washe baki ta ce, “zan ni in nunawa abokina Adona ne na irin kayan yan birnin da ya shiyamun inshe mishi na gode.”

Uwar Soro ta ce, “to kar dai kiyi wani gun kina fita ki shiga can in ba haka ba ana kamaki yanki ki za ayi na fada miki.”

Gaaji ta ce to sannan ta fice.

Bin bayanta Uwar Soro tayi sai da ta tabbatar ta shiga bangaren Yareema kafin ta dawo nata bangaren.

A hankali ta tura kofar ta shige.

Tana shiga kuwa taga Yareema na barci hankalinsa kwance daga shi sai gajeran wando.

Ta ce, “Ji an ishka barcin ma ba kaya yake yi, aiko yau zaka shi gidanku aradu.”

Ta karasa gabansa a hankali tana zuwa ta sake masa mari a kumatu tauuu ta kara sake wani tauuu.

Yareema ji ya yi kamar a maraki ana zabga masa wasu irin zafafan maruka.

Ya yi saurin bude idonsa ya ganta tsaye kansa amman ya kasa gasgata hakan.

Rike hannu tayi a kugu tana fadin, “Kalle ni da kyau mai idon mage nishe nan Zainabu Gaajin Baffa ramawa na zo yi na rama marin da kamun ehee kai ma ka ji inda dadi ai da wani wandon ka kamar nafkin.”

Sai a lokacin ya tabbatar da a zahiri yake, kokarin tashi ya fara a fusace.

Ai Gaaji da taja dogayen kafafunta masu kama da sandar sunuka sai waje.

Tashi ya yi ya…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Auren Wata Bakwai 7Auren Wata Bakwai 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×