Cin Amana
Shekaru shida kenan da auren Laɗifa da mijinta Sadik. Auren saurayi da budurwa suka yi da mijinta bayan an sha soyayya ta bugawa a jarida. A ranar bikinsu an sha shagalin da ko a ina ne aka yi irinsa lallai sai an daɗe ba a daina zancensa ba. Bayan shekara biyu sai Allah ya azurta su da haihuwar ɗiya mace suka sa mata sunan kakar Sadik wato Larai. Komai na rayuwa na tafiya musu daidai bakin gwargwado. Duk da yake ba a rasa samun saɓani irin na yau da kullum, wani babban al’amari dai da zai iya sa har a ji kansu bai taɓa faruwa ba.
Bakin gwargwado Laɗifa tana yi wa Sadik biyayya. Duk abin da ta san ba ya so tana kauce masa, haka kuma ko da wasa ya nuna mata baya son abu to shikenan ta bar wannan abun. Takan yi duk wani abu da ta san cewa zai faranta masa rai. Kama daga girki, tsafta, gyaran jiki da dai sauran abubuwa waɗanda ya kamata ace macen kirki tana yi wa mijinta. Wani ƙarin abun burgewa kuma game da Laɗifa shi ne irin yadda take mutunta dangin mijinta tare da girmama su kamar danginta.
A ɓangaren Sadik kuma, abin ba a cewa komai. Domin Laɗifa ba ta taɓa tunanin akwai mazaje masu kamanta adalci a duniya irin Sadik ba. Kamar yadda ba ta taɓa tsammanin za ta samu miji irinsa ba. Duk wani haƙƙi da ya rataya a wuyarsa yana ƙoƙarin sauke shi akan Laɗifa da ‘yar su. Baya taɓa tauye mata haƙƙi ta kowace fuska. Babban abu kuma shi ne, ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, kamar yadda ita ma ta yarda da shi ɗari bisa ɗari. Ma’ana dai suna zama na jin daɗi da kwanciyar hankali.
Wata rana sai mahaifiyar Laɗifa ta kwanta rashin. Jinya yau jinya gobe ciwo ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Kullum Laɗifa tana hanya zuwa duba mahaifiyar tata kasancewar ita kaɗai ta haifa a duniya. Da Sadik ya ga zirga-zirgar ta yi yawa sai ya ce wa Laɗifa, “Me zai hana mama ta dawo nan da zama kawai. In ya so kin ga sai mu bata ɗaya sashen can tunda babu mai zama a ciki ko?”
Laɗifa ta yi murna sosai da wannan jawabi, domin kuwa hakan zai sa hankalinta ya fi kwanciya.
Haka kuwa aka yi, washegari aka kwaso wa maman Laɗifa kayanta aka shirya mata su a ɓangaren da Sadik ya bata. Bayan ‘yan kwanaki kaɗan ta samu sauƙi tunda da ma ba wani tsufa ta yi ba. Kawai dai zazzaɓi ne irin na yau da kullum yake damunta. Bayan ta warke, sai ta nuna tana son komawa gida, amma sai Laɗifa ta nuna rashin jin daɗinta game da haka. Suka san dai yadda suka yi har suka shawo kanta ta amince za ta zauna a gidan.
Tun daga wannan rana duk in Sadik zai dawo gida sai ya dawo wa da Laɗifa da fura mai sanyi. Dama can tana sonta sosai, shi ya sa yake kawo mata. A cewar shi wani ne ya buɗe wajen siyarwa a kusa da su shi ne yake siyo mata. Ana nan bayan kwana biyu sai Laɗifa ta lura da duk idan ta sha wannan fura ba ta ƙara minti biyu lafiyayyu sai bacci ya ɗauke ta, wani lokaci har makara take yi. Ita kuma ba mai nauyin bacci ba ce tun da can. Kwana da kwanaki hakan na faruwa, kuma ta rasa menene dalili. Da ta yi wa Sadik magana sai ya ce ko ta samu ciki ne. Ita kuma ba ta ji wani canji a jikinta ba ko a mu’amalarta.
Da dai ta ga abin da gaske ne. Wata rana, bayan Sadik ya dawo kuma ya kawo mata furar kamar yadda ya saba. Sai ta juye a kofi ta kafa kai kamar tana sha sannan ta wuce ɗaki. Tana zuwa sai ta ajiye a firji sannan ta hau gado ta kwanta kamar ta yi bacci. Can bayan an ɗan jima sai Sadik ya shigo ya kwanta, ba a jima Ba kuma sai ya tashi yana bubbuga ta ya ji ko bacci take yi. Ita kuwa ta yi ƙumus. Da ya ji ba ta tashi ba sai ya fita. Da fari ta ɗauka banɗaki ya shiga. Amma da ta ji shirun ya yi yawa sai ta tashi ta hau dube-dube. Ta duba bayi baya nan, ta duba kitchen baya nan, ta duba waje baya nan. Sai fa hankalinta ya tashi, domin ya bar wayar shi a ɗakinta. Har za ta shige ɗaki ta kwanta sai ta ce bari ta duba ɗakin mahaifiyarta ta ga yadda take. Tana shiga kuwa sai ta yi arba da abinda har ta koma ga Allah ba zai taɓa mantuwa a gare ta ba. Sadik ta gani kwance akan mahaifiyarta suna lalata. Nan take ta zube ƙasa sumammiya.