Skip to content
Part 3 of 5 in the Series Ba Kauyanci Ba Ne by Ummu Adam

Gidansu Zubaida

“Hello, Ahmad” Zubaida ta faɗa bayan ɗaga wayar ɗaya daga cikin samarinta. “Sai yau ka tuna dani?”

Ahmad ya yi murmushi sannan yace “wanda aka manta shi ake tunawa, ke kuwa ban manta da ke ba ballantana in tuno ki; Kawai dai yanayin aiki ne sai ahankali shiyasa ki ka ji ni shiru.

Zubaida ta ɗan juya idanu sannan tace masa “kullum dai haka ka ke faɗa amma sai a jika shuru kamar an aiki bawa garinsu, kasanfa daga cikin farillan soyayya akwai kulawa da kuma damuwa da juna.”

Ahmad yace “gaskiya ne Zuby na, ke ko dai iya hausa kamar jakar kano”

“Yanzu wannan zagi ne ko yabo?” Zubaida ta faɗa.

Ahmad yaɗan gyara zama yace “yabo kai, ke kin fi karfin a zageki ai.
Kinga mubar maganan wasa meye labiri ne, yaushe zamu hadu?

Zubaida tace “gaskiya bansan yaushe zan fito ba dan jiya ma na fita kuma cikin kwanakin nan Baba ya samun ido wai anata kawo ƙarata na cika yawo kasan mutane sun iya gulma”

Ahmad yace “to gaskiya tsaraba na kawo miki amma tunda ba za ki samu fitowa ba, ya zama ba rabonki ba kenan dan jibi zan koma wajen aiki”

Cikin hanzari zubaida tace “kamar ya ba rabona ba! kaima Ka san ai bazai wuceni ba mu hadu a inda muka saba haɗuwa gobe da yamma”

“Yauwa ‘ƴar gari, yanzu naji magana, wata wayace nagani zata dace dake na siya miki da wata doguwar riga mai bala’in kyau”

“shiyasa na ke ji da kai nawan, sai mun hadu, barin fara tunanin yanda zan ninke Inna kasanta da sauƙin kai”

“Lalle Zuby ke wato abunnaki harda mamarki ko? Ahmad ya faɗa.

Zubaida tace “manta kawai, sai goben, saura kuma ka ɗebo jamfa nasanka da san dogin kaya”

Ahmad yace “gimbiya kenan, to ai jamfa yanamun kyau, toh amma tunda ba ƙya so shikkenan bazan saka ba”

Zubaida tace “ya dai fi kam, sai anjima barin samu Inna a waje”

bayan ta katse wayar sai ta fito tsakar gida gurin Inna tace mata “Inna sannu da aiki, ai da kinbari nayi”

Inna tace mata “ke da ki ka ce za ki yi karatu, jeki abunki ba komai, ai karatunnaki yafimin komai.

Wato Zubaida karatu a wannan zamanin ba abun wasa bane, shiyasa a shirye nake ko nawa zan kashe in dai ina da shi akan iliminki kinga babanku baida hali ɗan jarinnashi ma ya karye dan sana’an ƙosan nan dashi muka dogara, dan Allah Zubaida ki yi karatu ki sharemun hawaye na kin gade ku takwas na haifa amma yanzu daga ke sai ƙaninki Abdul da ku zanyi alfahari gaba, kuma abunda nake so dake kada duniya ta ruɗeki, ki yi hakuri akan abunda bakida shi; ki godewa Allah daya baki lafiya kuma ya ba ki iyaye biyu dan su sharemiki hawaye buri na ki yi karatu ki yi aure nima naga jikokina”

Zubaida ta ɗan gintse ido tayiwa Inna kallon jeka na yi ka alamar dai abunda Inna ta faɗa bai samu gurbin zama a zuciyarta ba.

“Inna kenan bakya gajiya da wannan maganar, in sha Allah bazan baki kunyaba. Inna akwai takarda da zan karɓo daga gidan su Khadija gobe daga makaranta zan wuce gidansu in kin bani izini”

Inna tace “toh ba komai, babanki ma yaje kauye sai gobe ko jibi zai dawo, yaje maganan gonansu na gado kinsan ance fatara mai tada tsohon bashi”

Zubaida tana dariya tace “kai babama dai yanzu dan Allah mai zai samu a wannan gonar, toh Allah ya dawo dashi lafiya”

Inna dai kanta ƙasa tana aikinta tace “amin”

Bayan Zubaida ta koma ɗakinta sai ta sake ɗaukan waya ta kira ƙawarta khadija, har sau biyu tana kira bata ɗagaa ba sai a na ukun taɗaga, “wai ina kika shiga ne?” Cikin gajan hakuri Zubaida ta tambayi khadija.

khadija tace “hmm ina can inata wanki, yau sani akai agaba da fada wai na fiye ƙazanta ni kuma kin san na tsani wanki gaskiya shine mama ta kwace wayan wai sai na gama tabani”

Zubaida tace “kekam ai kin saba daman ga san wanka ga kazantar tara wanki, angirama ba’asan angirmaba”

Khadija tadan haɗa rai ta ce, “kinga yaufa nima a sama nake jina kina mun zan tanka miki, gara kibini ahankali”

Zubaida ta ce, “ke ba wannan bama dan Allah ki gogemun kaya seti daya mai kyau acikin naki, zamu haɗu da Ahmad kinsan bansan raini so nake ya ganni a haɗe daga sama har kasa”

Khadija tadan juya baki sannan tace mata “tabɗi lalle ma, sai dai in kin zo ki goge da hanunki; wankinma da yaya na yi shi gaskiya bazan iya miki guga dan ki yi wa wani ƙato kwalliya ba.”

Zubaida ta ce, “Shikkenan naji ke dama ba’a abun arziki dake.”

Khadija ta ce “Auu hakama zaki ce? sai na fasa baki aron kayan naga ya zakiyi”

“Kiyi hakuri ƙawata kema kinsan ba’ajin kanmu, sai mun haɗu goben kawai”

Khady tadanyi murmushi sannan tace “shikkenan, sai mun haɗu ki gaida inna”

Zubaida tace “to inna zataji”

Bayan tayanke wayan sai take magana da kanta kamar haka… “toh an kauda wannan matsalar barin kira khalifa ya turomin kati a waya, gida biyu maganin gobara”.

Gidansu Kamal

Cikin ɓacin rai da takaici iyayen Kamal ke zaune a ɗakin hutu, sun ɗauki aƙalla daƙiƙa goma ba wanda ya yi magana. can sai Kamal yace “dad, Mum mai yasa kuke ɗaga hankalinku ne?
Nifa abunda Salma ta mun bai dameni ba saboda na san akwai ranan da za ta zo da kanta ta roki gafara na akan abunda ta yi.”

Cikin fushi baban shi ya ɗaga murya yace “rufe mun baki! waya faɗa maka abunda Salma ta yi maka ne yake damu na?

Ni na san Salma kuma na san tarbiyyar da ta samu wajen iyayenta, ba za ta mareka acikin mutane ba tare da wani dalili mai karfi ba. Dan haka ka faɗa mun Meye ka yi wa Salma?

Kamal ya dubi mahaifiyar shi sannan yace “haba dad yanzu kuma laifi na zaka gani? ni kenan kullum bani da gaskiya a idanka baba! gaskiya ni bakamin adalci.

Nafi kowa sanin halinka Kamal dan haka ba abunda zaka faɗamun. Wai zuwa turai hauka ne duk kabi ka canja ka ɗauko dabi’ar turawa na rashin kamun kai da nitsuwa.

To bari kaji, in dai kana so mu shirya dankai to dole ka gyara halinka; ka zama mutum na gari in ko ba hakaba to zanyi maganin ka.

Hajiya Aisha ta dubi mijinta tace “haba alhaji kai kenan kullum cikin faɗa da yaron nan, yaro kwaya daya kaman rai amma duk kabi ka sa shi a gaba kanata mai faɗa. Kuma maganan Salma da ka ke yi ai dama nasan ba za ka taɓa ganin laifinta ko na mahaifiyarta ba tunda ka so maman ta a lokacin baya shi yasa yanzu ka ke kushe ɗanka na cikinka saboda ‘ƴar wata.”

Kamar sukar mashi haka baban Kamal yaji kalaman matarshi, amma sai ya juya ya kalli Kamal yace masa “tashi ka tafi ɗakin ka.” Bayan Kamal ya tafi sai mahaifinsa ya juyo zuwaga matarsa sannan yace mata “yanzu Hajiya wannan maganar ce take fita daga bakin ki kuma a gaban ɗanki? wai dan Allah yaushe zaki girma ne kisan abunda yadace?, kuma maganan Kamal ai ke ce ki ka ɓata shi shiyasa ya zama haka; amma ki sani watarana za ki yi dakin sani idan har baki gyara halinki da tarbiyar ɗanki ba”.

Yana gama magana ya juya zai fita, tare da faɗin “ni na tafi dan dare yanayi.”

“hm! ai dama na san haka za ka ce, tunda ka ƙara aure ka canza da anyi magana ka hau faɗa; Allah dai yana gani kuma yana tare da mai gaskiya”

mahaifin Kamal ya dawo kusa da ita yace “matsalarki baƙin kishi, shi yake hana ki ganin gaskiya da binta. Shekaran mu talatin da aure amma kin kasa gyara halinki, ki godewa Allah da yasa auren kawai nayi ban sallameki ba; kuma daga yau kinyi na farko kuma na ƙarshe kada ki sake kawo maganan so tsa ka nina da mahaifiyar Salma”

Bayan fitan Alhaji daga gidan sai Kamal ya dawo gurin mahaifiyar shi, cikin sanyin murya yace “mum kiyi hakuri; kada ki biye wa maganan dad kinsan kullum cewa ya ke yi wai kin ɓatani kuma shine kawai bai ja ni a jikinsa ba amma ai ni a shirye nake. kuma maganan Salma ai ramuko da daukan fansa duk lokaci suke jira, namiki alkawarin zan rama abunda ta mun da mafi munin ramuwa!”

Hajiya Samira ta dubi ɗanta da take matukar so tace “Kamal ina son mahaifinka wannan dalilin yasa na kasa jure rashin mantawa da sonda ya ke yiwa ƙawata.

Duk tsawon shekarun nan ina ƙokarin mallakar zuciyarsa amma na kasa!”

Kamal ya yi mamakin jin haka daga bakin mahaifiyarsa!

Sai yace mata “Mum ƙawarki kuma? ban gane me ki ke faɗaba, kimin bayani yanda zan fahimta dan Allah”

Bayan ta gyara zama ta dubi Kamal tace “yanda kaga Salma haka Hajiya Bilkisu take lokacin muna makaranta, dani da ita kawayene amma sam halin mu ba daya ba; Bilkisu ta kasan ce shiru-shiru ba ta da hayaniya sannan aduk makarantar uniform dinta ya fita daban dana mafi yawan ɗalibai mata.

Tsawon rigarta da girman hijabinta ya fi na ‘yan ajinmu girma, hakan yasa muke mata kallon bata waye ba domin a lokacin muna ɗan ji da kanmu harkan ado ake yi da nuna kwarewa wajen iya gaye da kwalliya,uniform dinmu duk ya kama jikinmu.

Kallon rashin wayewa da mu ke yi wa Bilkisu bai dameta ba hasali ma batamasan munayiba, lokacinda akai wa babanka canjin nakaranta ya dawo namu makarantar muna aji shida na sakandire; ya zo ne dan ya rubuta jarabawar gamawa tare da mu.

Tun daga kallon farko da na yi masa na kamu da sonsa amma shi hankalinsa akan bilkisu yake, hakan ya sa ta fita araina nafara kishi da ita; saboda na fita kyau, kuma ni ce nake zuwa ta ɗaya itakuma ta biyu.

Sannan na fita wayewa da bin zamani amma duk da haka na kasa burge shi, bayan mungama makaranta naji sai labari ya zo mun kan cewa Bilkisu da babanka suna soyayya.

Na yi mamaki!, domin lokacin muna makaranta taki yarda dashi kuma taƙi amincewa da soyayya sam.

Labarinda naji ya ɗagamun hankali kuma nabi duk hanyadda zanbi amma nakasa rabasu kasancewar halinsu yazo ɗaya kai ka ce tamkar an yi isu ne saboda juna”.

Kamal ya fahimci inda matsalar ta fara. Ya kalli manansa yace “tabdi jam! Ikon Allah kenan, mum to ya akai ki ka auri dad?

Hajiya samira tace “watarana ina zaune sai babanka ya kira ni a waya yacemun yana kofar gidanmu, cikin sauri na fita gurinshi; a lokacinne kunnuwana suka ji kalamanda basu taba tsammaniba daga bakin mahaifinka. Bazan taba mantawa da da wannan rananba kamal..

Bayan kamal ya gyara zama sai yace me dad ya fada miki a lokacin?

“I love you Samira” shine abunda babanka yace.

Nayi minti biyar ina kallonsa bance komaiba, dana bude baki zanyi magana sai ya kara da cewa “kiyi hakuri na ɗauki lokaci mai tsawo kafin na faɗamiki hakan ina sanki kuma da aure nazo idan haryanzu kina sona sai ki sanar da Baba zanturo iyyena a duk lokacinda ya shirya karbansu”

sai ya buɗe motarsa ya dauko wata chocolate wacce na saba saya lokacin muna makaranta yabani ya shiga mota ya tafi.

Bayan wasu mintuna sai na juya na shiga gida ko sallama banyi ba sai maman mu ta dan bugi jikina tace ina sallaman zaki shigo ba ita?

A lokacin ne na tabbatar ba mafarki na ke yi ba, bayan nakoma ɗakin mu na yi ta tsalle ina jin daɗi na taka rawar farin ciki; nayi kyauta da abubawa dayawa daban san adadinsu ba.

Babana yana dawowa na fadamasa abunda Samira yace, ya ji daɗi sosai kasancewar yasan mahaifin sa.

Babana ya amince, aka saka mana ranar aure.

A washe garin da nagama jami’a aka daura mun aure da baban ka kuma masoyi na, bayan shuɗewar wasu watanni sai muka tafi ƙasar amurka muka ci gaba da karatu a can; bayan mun kammla sai muka dawo gida Nigeria lokacin kana da shekara biyar a duniya.

Kamal yace to amma Mum mai sa Dad bai auri Maman Salman ba?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba Kauyanci Ba Ne 2Ba Kauyanci Ba Ne 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×