Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Baba Dattijo Dan Bursin by Mukhtar Sipikin

Tunda na fara aikin jarida ban taɓa haɗuwa da labari mai ruɗani da rikitarwa kamar na Baba Dattijo ɗan bursin ba. Ana zarginsa da kashe mutane har biyu a tsahon shekaru 31 a rayuwarsa.

Farkon hirarmu da shi ranar wata Asabar ne da safe, Sha-shida ga watan Janairun 1999, a gidan yarin Kurmawa da ke Kano;

Bayan mun gaisa mun ɗan yi hirar rayuwar gidan yari da shi da yadda lamura su ke, sai na karkato zuwa abin da ya kawo ni wajensa, wato labarin yadda ya tsinci kansa a halin da ya ke ciki. Nan ya faɗi wata magana mai ban mamaki da ɗaure kai, kamar haka;

“Yaro duniya an ce ta yi shekaru dubunnai, sannan an ce mutane biliyoyi sun rayu cikinta sun mutu, kuma kowa da labarinsa amma wallahi ban taɓa jin mai irin labari mai rikitarwa irin na rayuwata ba”

Na yi shiru, ina ƴan tunane-tunane da wasi-wasi akan maganar da Baba Dattijo ya faɗa, amma na yi shiru na kasa kunne don kar in katse shi.

“Ni da ka ke gani yanzu ana tuhuma ta ne da kashe wani mutumi wata ɗaya da suka wuce, kuma shi wannan mutumin kotu ta taɓa yanke mun hukuncin na kashe shi shekaru 29 da suka wuce”

Na ɗago kai cikin mamaki na fara jero masa tambayoyi kamar haka;

“Baba Dattijo ni fa ban gane wannan maganar ta ka ba? Wai kana nufin sau biyu ka kashe mutum ɗaya? Kuma shekara 29 da ta wuce ka kashe shi, sannan wata ɗaya da ya wuce ka ƙara kashe shi?” To dama ana mutuwa a dawo ne? Ni fa Baba Dattijo wannan labarin na ka, sam ban fahimce shi ba” Na faɗa cikin fushi. Fushi irin na wanda ya ke gani an raina masa hankali.

Da alama dai Baba Dattijo ya fahimci cikin fushi na ke, da kuma rashim yarda da zancensa mai kama da tatsuniyar Gizo da Ƙoƙi.

“Yaro kasa kunne ka ji yadda hakan ta kasance, sannan ina roƙonka da inna fara ba da labarin nan kar katse ni da tambayoyinku na jarida, masu hana mai sauraro fahimtar labari”

Na ce “Tohm, Baba Dattijo na yi shiru ina sauraronka, Bismillah, fara”

Nan Baba Dattijo ya yi gyaran murya sannan ya fara ba da labarin yadda aka haihu a ragaya.

Zan ɗora insha Allahu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Baba Dattijo Dan Bursin 2 >>

3 thoughts on “Baba Dattijo Dan Bursin 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×