Skip to content
Part 11 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Kaddarar Zainab 

Jarabawa riga ce ta duk wani mai imani, kuma ita ce ke fayyace shi a mizanin rayuwa.

Zainab Yusuf, wata baiwar Allah ce wadda jarabawar rayuwa ta zo wa a baɗe. Zainab ta fuskanci wata irin jarabawa ce wadda ƙalilan ne daga cikin mutanen duniya suka taɓa fuskantar irinta.

Lamarin ya fara ne a ranar 5th/05/2005. Rana ce wadda Zainab ba za ta taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwarta. Domin a wannan rana ce Allah ya azurta ta da samun ɗiya mace bayan ta haifi ‘ya’ya maza har guda uku. Farinciki a wurin Zainab a wannan rana ba zai iya misaltuwa ba.

Sai dai farincikin nata bai daɗe ba, domin a wannan rana ne Allah maɗaukakin sarki Ya ɗauki ran mahaifinta wanda kusan shekaru biyu kenan yana jinya. Zainab ta yi kuka sosai kamar ranta zai fita, saboda ta shaƙu sosai da mahaifinta. Dole ce kawai ta sa ta dangana, don ta san cewa babu abinda za ta iya yi. A ranar 12th/05/2005, wadda ta zamo ranar sunan ɗiyar da Zainab ta haifa kuma ranar sadakar bakwai ɗin Malam Yusuf, watau mahaifinta. Kwatsam kuma sai ga wani sabon tashin hankalin ya sake afkawa ahalin su Zainab.

Ƙanin Zainab, wanda Injiniya ne a wata ma’aikatar sarrafa ƙarafa da ke Niamey, babban birnin Nijar ya samu labarin rasuwar mahaifin nasu. Don haka ne ma ya kamo hanya da nufin ya zo tun ranar uku. Sai dai tun ranar da aka faɗa mishi rasuwar ba su ƙara samun shi a waya ba. Sai yau ranar bakwai kawai wani abokinsa da suka yi firamare tare ya kira su yake shaida musu cewa ya ga gawar ɗan uwansu a cikin gawarwakin da mahara suka kashe a hanyar Katsina kwanaki biyu da suka gabata.

Wanda duk ya ce ma zai iya misalta irin tashin hankali da baƙin cikin da su Zainab suka shiga a wannan lokaci daidai yake da wanda ya shuka gasasshiyar masara yake ba ta ruwa tare da sa ran za ta tsiro.

Haka aka je aka ɗauko gawar aka kawota gida aka yi masa sutura aka binne shi.

Kasan mata ba a rasa su da tsegumi da ‘yan gulmace-gulmace. Don haka nan da nan sai wasu suka fara cewa ‘ai wannan jaririya ce da aka haifa ke da ƙashin tsiya, shi yasa mutanen gidansu ke ta mutuwa.’ Wasu suka ce mayya ce, wasu kuma suka ce ai aljana ce.

Ita kuwa, Zainab babu abin ɗa take yi face kuka. Jaririyar kuwa, wadda aka sa wa suna Safreen, sai ta zamo wata irin yarinya mai haƙuri na ban mamaki. Yarinyar ko kaɗan ba ta da rigima. In dai ka ji tana kuka, to ko dai ta yi bayan gida ne ba a canza ba, ko kuma yunwa take ji. Kuma da zarar an kula da ita shikenan. Haka dai aka yi jana’iza aka ƙare, kowa ya tafi yana faɗin albarkacin bakin shi.

Sai dai kuma, tashin hankali bai barin Zainab a daidai wannan lokaci ba, da alama akwai sauran zumuncin da yake son ƙullawa a tsakanin su. Sati biyu bayan rasuwar mahaifinta, sai ‘ya’yanta maza guda biyu Kabir da Usman, mota ta buge su a hanyar su ta dawowa daga makaranta duk suka mutu. A wannan rana sai da Zainab ta yi ‘yar ƙaramar hauka, domin ji ta yi kamar duk duniyar babu mai sonta a wannan ranar. Da ƙyar aka samu aka lallashe ta ta ɗan nutsu, amma duk da haka ba ta daina sambatu. Haka dai akai ta mata wa’azi da nasiha.

Sai dai kwana uku da yin haka ne kuma mijin Zainab shi ma ya kwanta dama. Wannan mutuwa ba ƙaramin girgiza kowa ta yi ba. Domin abun ma ya zama tamkar a fim yake faruwa. Kafin wani lokaci, ‘yar ƙaramar hauka ta kama ta. Abu ya ta’azzara har sai da aka kai ta asibitin mahaukata. Sai da ta yi kusan shekaru biyu a can kafin aka sallamo ta. Amma wani ikon Allah, a cikin haukar nata haka nan ta dinga shayar da ɗiyarta har ta kai minzalin yaye. Da fari likitocin sun so su raba ta da ita, amma da suka ga irin artabun da ake yi da ita in aka amshe yarinyar da kuma irin yadda takan nutsu in yarinyar na tare da it’s sai suka ƙyale ta.

Amma saboda abubuwan da suka faru, sai zaman gidan ya gagareta. Domin yana tuna mata da abubuwa da yawa game da ‘ya’yanta da kuma mijinta da ta rasa. Saboda haka ne ma ta siya wani ƙaton gida a Bauchi da ke kusa da Kawunta suka koma can da zama ita da ɗanta guda da ya rage Jibrin, da kuma Safreen.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 10Bakar Kaddara 12 >>

3 thoughts on “Bakar Kaddara 11”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×