Skip to content
Part 13 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Tsautsayi

Hausawa kan ce, ‘Biki wan shagali’

Suna kuma ƙanin biki ne.

Kamar yadda aka saba, a mafi yawancin sassan ƙasar Zazzau da maƙwaftanta, a duk ranar da ake yin suna, wato ranar da jariri ko jaririyar da aka haifa ya cika kwanaki bakwai. A kan yi fate ne da tuwo domin mahalarta taro. Sai dai yanzu da yake zamani ya canza, akan haɗa da shinkafa domin sirkawa.

Yau na dai haka abin yake. Yau ce ranar da ake suna a gidan Malam Sallau da ke ƙauyen Kyamfa. Wannan kuwa ita ce haihuwa ta farko da aka yi a gidansa, don haka batun murna da farinciki dai kam sai wanda ya gani.

Mata ne ga su nan danƙam cike da gidan babu ko masaka tsinke. Hayaniya kuwa, kai ka ce kasuwa ce ke ci a. Kasancewar ƙauyen ba wani yawa yake da shi ba, kusan duk matan garin ne suka hallara a gidan sunan. Masu gulma na yi, masu tsegumi da munafurci na yi, shewa na yi, masu guɗa na yi, masu aiki na yi, ga wasu kuma can sun kunna Mp3 sai cashewa kawai suke yi abin su. Ka san babu abinda mata suka fi so a duniya sama da bidi’a.

Ga wasu narka-narkan tukwane nan guda biyu irin wanda ake yi wa laƙabi da ‘Saka Maigida ihu’ an ɗora a wuta. Ɗaya ta tuwo ce, ɗaya kuma ta fate ce. Sai kuma wasu ƙananun tukwanen guda biyu, ɗaya ta miya ɗayar kuma ta tafashen naman suna.

Can kuma a waje, wasu mazan ne su ma suka kafa tasu majalisar, in da suke hirarraki irin na raha, bajinta da kuma jin daɗin duniya. Wasu kuma da zarar sun zo sun yi wa ‘angon ƙarni’ murna sai su wuce uzurin gabansu, wasu kuma sukan yi masa ‘yar kyauta na abinda ya sauwaƙa gare su.

A bayan gidan sunan kuwa, yaran unguwa ne suka taru maƙil suna mugun wasa. Wasan jefe-jefe suke yi. Wasu da duwatsu, wasu da itace ce ko fale-fale. A cikin irin wannan wasan ne, wani daga cikin yaran da ya yi jifa sai dutsen ya yi sama, bai sauka a ko’ina ba sai cikin tukunyar tuwon suna. A daidai wannan lokaci kuwa, ƙanwar mai jego ce akan gaba wajen tuƙin tuwon. Dutsen na faɗawa cikin tukunyar tuwon sai tafasashen talgen ya yi tallatsi, bai sauka a ko’ina ba sai kan kyakkyawar fuskarta.

Tsananin zogi da azaba ne suka sa ta kurma wani irin firgitaccen ihun da sai da mazajen da ke waje suka jiyo ta tana mai dafe fuskarta. Nan da nan hankalin kowa ya dawo kanta, ɗago hannun da za ta yi kuwa sai ta ɗago da fatar fuskar tata, ta saluɓe. Nan da nan aka fara ba ta agajin gaggawa kafin daga a kawo mashin a kai ta asibiti. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci gidan ya yi tsit kowa ya shiga taitayinsa. Su kuwa yaran tuni suka watse kowa ya kama gabansa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Kaddara 12Bakar Kaddara 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×