Skip to content
Part 16 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Mallakar Miji 

“Na ce fa babu inda za ki je Talatu! Don haka kada ki sake ki fita ko ƙofar gida. In kuwa ki ka sake ki ka fita ba tare da izini na ba to wallahi sai na saɓa miki.”

Salihu ne ya yi wannan furuci. Yana gamawa kuwa sai ya fice daga gidan gaba ɗaya. Ita kuwa Talatu tuƙuƙin baƙinciki ne ya hana ta cewa uffan.

Karo na shida kenan tana tambayar shi fita yana hana ta. Ita dai ta kasa gane kan mijin nata. Duk wani abu da take so ta lura cewa ba damun shi ya yi ba. In dai za ta ca ‘a’ to tabbas shi kuwa zai ce ‘ba’. Sam ba haka ta zata ba. Ta ɗauka Salihu zai bata damar watayawa yadda ta ga dama ne, amma tun bayan aurensu ta fahimci cewa ba za ta samu wannan damar ba. Ita ba haka ta taso ta ga mahaifinta na yi wa mahaifiyarsu ba. Mahaifinta ko kara mahaifiyarta ta aje ba zai iya tsallakewa ba. Amma ita nata mijin sai ka ce saƙago, sam kamar bai da shauƙi. Tabbas ya zama wajibi ta ɗauki mataki akan shi. Ba zai yiwu tai ta faman wani bin shi kamar raƙumi da akala ba.

Bayan an samu kwanaki uku da faruwar hakan ne Talatu ta yi waya da mamanta, nan fa ta zayyane mata ƙarya da gaskiya. Ba ta kashe wayar ba sai da suka gama tsara hanyar da za su bi su ɓullo wa lamarin na Salihu. Dama mamanta ta sha gaya mata maza ba a zama musu hakanan, ita ce dai abin bai gama zama mata a rai ba. Suna gama wayar Mamanta ta kira Salihu ta sanar mishi cewa ba ta jin daɗin jikinta, kuma tana so Talatu ta zo ta ɗan zauna da ita zuwa yamma. Shi kuwa Salihu, ko da jin cewa surukarsa ce ba lafiya sai nan da nan ya amince ba tare da tunanin komai ba. Har ma guzuri ya haɗa mata da shi ta kai wa mai jikin.

Tana zuwa gidansu, abinci kawai ta ci suka tafi wurin bokan da ke yi wa maman aiki, dama ita ma akwai wani aikin da zai yi mata. Nan fa suka kama hanyar zuwa ƙauyen Tungumi, inda bokan yake. Amma da yake akwai ‘yar tazara ba su kai ba sai bayan Azahar. Da zuwan su, bayan sun sauka a ɗakin da bokan yake sun gaisa sai mamanta ta ce ta bayyana wa boka abinda ke damunta. Nan fa Talatu ta fara zabga ƙarairayin abubuwan da Salihu ke yi mata, sannan daga ƙarshe ta ce ita babban abinda take so shi ne a yi mata aikin da sai abinda ta ce ya yi zai yi.

Bayan ta gama zayyano irin abubuwan da ke ranta, sai bokan wanda ake kira da Safala ya fara bayani da cewa,

“Na fahimci irin aikin da kike buƙata. Kafin a yi miki wannan aiki, za ki bada dubu ɗari, sannan za ki yanka jajayen zakaru guda goma ba tare da bismillah ba. A ƙarshe kuma za ki bani kanki.”

Ya ƙarashe maganar yana mata wani irin mayunwacin kallo.

Ko da jin wannan batu sai Talatu ta yi zuru-zuru da idanuwa kamar wadda aka ƙure ta yi ƙarya. Nan fa ta waiga wajen mahaifiyarta don ganin ko ita ma maganar ta jijjigata kamar yadda ta yi mata. Bisa mamaki sai ta ga cewa ita kam ko a jikinta, sai ma washe baki kawai take yi. Ita kam tana son mallakar mijinta, sai dai fa ba za ta iya ba da mutuncinta ga wannan tsohon mutumin domin cimma wannan manufa ba, don haka sai ta nuna mishi gaskiya ita ba za ta iya ba. Nan take kuwa mamanta ta rufe ta da faɗa, tana ƙara zuga ta tare da ba wa boka haƙuri. Amma duk da wannan abu da ke faruwa, Talatu ba ta amince da wannan al’amari ba. Hakan ne ya sa bokan ya ce ta fita waje ta basu wuri za su yi magana.

Tun da ta fito tunani kawai take yi. Ya ma za a ce ta bada mutuncinta saboda wata buƙata ta duniya?

Sai da ta yi kusan awa guda a waje tana jiran fitowar mamanta amma shiru. Da ta ga dai shirun ya yi yawa, sai ta yanke shawarar komawa cikin ɗakin bokan domin ta yi wa mamanta magana ta fito su tafi. Ai kuwa tana shiga sai ta yi arba da abinda ya fi ƙarfin ƙwaƙwalwarta, ba komai ta gani ba face mahaifiyarta da Boka Safala tsirara haihuwar Uwarsu da Ubansu suna lalata. Nan take Talatu ta faɗi ƙasa sumammiya.

<< Bakar Kaddara 15Bakar Kaddara 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×