Skip to content
Part 20 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Ragon Layya 

Shekara guda kenan Malam Garba ya yi yana kiwon ragonsa. Domin tun ranar Idin babbar sallar da ta gabata ya siye shi, kuma tun daga wannan lokaci yake ba shi kulawa yadda ya kamata. Izuwa yanzu tunkiyoyin da yake kiwo duk sun samu ciki a sanadiyar wannan rago. Wasu ma har sun haihu. Rago dai kam gashi nan ya cika, kowa ya ganshi sai ya ƙara dubawa da kyau. Rago ne wanda ya amsa sunansa rago, kuma malam Garba ya ƙwallafa rai matuƙa akan shi. 

Babu shakka a duk daɗin yankinsu ya yi suna wajen iya kiwo, domin ba ya barin dabbobinsa da yunwa. Kuma kowane ƙarshen wata likitan dabbobi na zuwa ya dudduba su kuma ya basu magunguna. Babban abin burgewa da rayuwar Malam Garba shi ne irin yadda yake kula da dabbobin nan nasa. Shi ko irin noman nan ma baya yi, kiwon kawai ya sa a gaba rani da damina. Kashin dabbobin nan su yake amfani da shi wajen biyan wasu buƙatun nashi. In kuwa har buƙatar babba ce, to dabbobi na nan sai wanda ya zaɓa zai siyar. 

Baya ga raguna da tunkiyoyi, yana kiwon awaki, shanu, agwagi, talo-talo, kaji, zabbi da dai sauran abubuwan kiwo. Saboda gudun damuwa ma, gidan gonarsa a jikin gidansa yake. Kuma duk masu yin ciyawa da masu siyar da dusar da ke yankin sun san da zaman shi, domin shi ne kaɗai wanda ke siyan kayansu ya biya su a mutunce. Wani lokacin in ya samu sa’a kajinsa suka yi abin kirki, a rana sai ya yi cinikin ƙwai na dubu talatin a ɗan ƙauyen nan. 

Babbar matsalar shi ita ce, in har ya riga ya yi wa dabbarsa kuɗi, to fa babu gudu babu ja da baya, sai dai in mutum zai fasa ya fasa amma ko sisin kwabo ba zai rage maka ba. Shi ya sa kowa ya zo ya ga ragon nan in ya ji kuɗin da ya sa mai sai dai ya riƙe baki kawai yana mamaki. Malam Garba dai ya ce shi kuɗin ragon nan atafau dubu ɗari uku ne, babu ragi babu ƙari. Alhaji Aminu, wanda shi ne babban attajirin garin ya taya ragon har dubu ɗari biyu, amma Malam Garba ya ce ina! 

Ciniki dai ya yi ciniki har aka kai ga dubu ɗari biyu da hamsin, amma duk da haka ya ce ba zai rage kosisi daga cikin kuɗin nan ba. Da Alhaji Aminu ya ga ya dage haka, sai ya ce da shi, “To shikenan bari mu gani zuwa gobe, ƙila in na samu wasu ‘yan kuɗaɗe in dawo, ko kuma wataƙila kai ka sauko.”

Malam Garba bai ce komai ba sai ma kaɗa kai da yake ta yi. A haka dai aka tafi akan cewa gobe za a zo a ƙarasa cinikin. 

Washegari da sassafe, Malam Garba ya shiga cikin dabbobinsa yana dudduba su kamar yadda ya saba. Su kuwa sai murnar ganinsa suke yi. Wasu ya shafa kansu, wasu ya ƙara musu abinci. A haka dai har ya zo kan ɗakin da ragon nan yake da nufin shi ma ya duba shi. Yana shiga kuwa sai ya ganshi a sanƙame, ya mutu. 

<< Bakar Kaddara 19Bakar Kaddara 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.