Tsananta Bincike
An yi wasu abokai guda uku a wani gari daga cikin garuruwan arewacin Nijeriya. Guda ana kiransa Sa’idu, guda kuma Basiru sai ɗan ƙaraminsu Aminu. Waɗannan abokai sun kasance sa’o’in juna ne, kuma unguwarsu guda ne, hasali ma dai wuri guda suke kwana. Ko da yake masu iya magana kan ce ‘Sai hali ya zo ɗaya ake abota’ su waɗannan abokai ba haka suke ba, domin kuwa sun sha bamban a halayyarsu. Shi dai Sa’idu mutum ne mai yawan Surutu da zafin rai. Shi kuwa Basiru mutum ne mai shisshigi da son jin abinda bai shafe shi ba. Shi kuwa Aminu mutum ne shiru shiru wanda ko yatsa ka saka mishi ga baki ba ya ciza ba. Kai ko da ganin shi ma kana iya fahimtar sanyin ransa ba sai an ce maka ga yadda yake ba. Saboda wannan sanyi nasa da kuma biyayya da yake da ita fiye da ya sauran abokansa yasa mutane suka fi sonsa. Su kuwa kullum cikin kushe shi suke, kullum sai su yi ta cewa ‘Ai shiru-shirun shi na munafunci ne, wa ya san abinda yake aikatawa a ɓoye?’
Haka dai sukan faɗi duk kuwa da cewa basu taɓa ganin ya aikata wani mummunan aiki ba. Shi dai ko sun faɗi hakan sai ya yi murmushi kawai ya sadda kai ƙasa. Wata rana sai Aminu ya kwanta ya mutu. Mutane suka yi baƙin ciki sosai, musamman abokansa. Domin ko da yake basu da aikin yi kullum sai kushe shi, hakan bai sa ya guje su ba. Haka dai aka haƙura da wannan rashi aka yi wa Aminu wanka, aka suturta shi domin a kai shi makwancinsa.
Kawai sai wata shawara ta zo wa Basiru; me zai hana su saka rediyo mai rikoda a cikin kabarin Aminu domin su ji irin tattaunawar da za su su yi da mala’iku? A tunaninsa hakan zai kawo ƙarshen zargin da suke yi wa Aminu. Saboda haka sai ya jawo Sa’idu ya shaida mishi wannan dubara. Da fari kamar ba zai amince ba, amma da Basiru ya yi ta kawo mishi misalai iri-iri sai ya amince. Don haka sai suka samo ‘yar rediyo mai rikoda, sannan suka nufi maƙabarta inda za a binne Aminu. Da isar su sai suka nuna su suke so su saka shi a makwancinsa na gaskiya. Ganin irin kusanci da kuma sabo da suka yi ya sa babu wanda ya kawo wani abu a ransa. Garin saka gawar nan fa a cikin kabarin ne Basiru ya san yadda ya yi ya saka wannan ‘yar rediyo bayan ya kunna ta. Bayan an kammala janazar an yi addu’o’i sai kowa ya watse. Su Sa’idu ne gaba-gaba wurin amsar gaisuwa, amma in a zuciya duk sun ƙosa su samu damar da za su koma su tono wannan ‘yar rediyo su ji yadda aka yi tsakanin Aminu da mala’iku.
Damar da suke nema ba ta samu ba sai da aka yi addu’ar uku tukunna. A wannan dare ne suka je kabarin, dama sun yi mishi shaida. Suka tone kabarin suka zaro wannan rediyo suka maida ƙasa suka rufe. Ko da suka dawo gida sai suka shiga cikin ɗaki suka rurrufe ƙoda da taga sannan suka kunna wannan rediyo domin su ji hirar Aminu da mala’iku. Ko da suka kunna wannan rediyo, sai wata irin ƙara mai matuƙar muni ta bayyana. Ƙarfi da munin wannan ƙara ne ya sa nan take Basiru da sauran mutanen gidan duk suka mutu. Shi kuwa Sa’idu nan take ya haukace ya hau sambatu. A cikin wannan sambatu nasa ne yake faɗin irin abinda suka aikata. Ba don ya faɗa ba, da babu wanda zai san haƙiƙanin abinda ya faru. Haka aka yi wa ‘yan gida ɗayan nan jana’iza su ashirin da biyu reras. Mutanen wannan gari basu taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba. Shi kuwa Sa’idu ya yi ta yawo yana sambatunsa har ya koma zuwa ga Allah.