Skip to content
Part 5 of 25 in the Series Bakar Kaddara by Haiman Raees

Sabon Ɓarawo 

An yi wani lokaci da aka yi tsananin talauci. Ya zamana abinda mutum zai ci ma sai an yi da ƙyar. A wanna lokaci mutum in ba noma ya yi ba abincin da zai ciyar da gidansa ma gagararsa yake yi. Noman kuma sai wane da wane saboda tsadar rayuwa ta kai intaha.

A cikin wannan hali ne Uzairu ya yi aure. Sai dai ya ci sa’a, da yake iyayen matar manoma ne sun kawo musu gara mai yawan gaske. Ba a daɗe da yin auren ba kuma sai aka sallame shi daga wurin aiki. Ya zamana kafin sisi ta shigo aljihunsa ma aiki ne. Haka dai ya ci gaba da fafutukar neman wani aikin amma bai samu ba. Ba a jima Ba kuma sai gara ta ƙare, ya zamana sun shiga cikin ƙunci ainun. Watarana ma sau ɗaya suke ɗaura tukunya. Kai aka ƙare ma dai sai su yi kwana uku wani sa’in basu ɗaura tukunya ba. Ita kuwa matar nan sai ta fara nuna masa irin halin nasu na mata. Kullum ba ta da aiki sai zagi da yi mishi gorin rashin aikin yi. To Allah ya zuba mishi son wannan mata, don haka baya iya ce mata komai.

Suna nan zaune a haka dai har ta samu juna biyu. Rannan da ta gaji sai ta ce ya fita ya je ya nemo musu abinci ko na sata ne. In kuwa ba haka ba za ta tattara ‘yan komatsanta ta koma gidan iyayenta. Cikin rawar jiki ya yi ta rarrashinta tare da yi mata alƙawarin ba zai komo ba sai da abinda za su ɗan taɓa. Fitarsa ke da wuya kuwa sai ya nufi wani shago inda ake siyar da kayan masarufi. Ya nemi taimako a wurin mai shagon da ya taimake shi da bashin abinda za su ci shi da iyali. Mai shago ya yi kinini ya ce shi ya daina ba da bashi. Ya ga yanzu in ba wannan shago ba babu inda ya sani da zai je a ba shi bashi. Shi kuma ba abin ya je masallaci ya yi bara ba a ɗauke shi a matsayin mabaraci. Shi ko ba shi ko fara komawa gida hannu rabbana, yasan ba su gamawa lafiya lau da matar nan tasa. Ko da ya faki idon mutane sai ya yi wuf ya ɗebi ledojin taliya uku ya ranta a na kare ya nufi.

To shi dama mai shago kwana biyu ya lura ana ɗan yi masa sata, don haka ko da ya hango shi lokacin da ya ɗauki taliyar sai ya yi kururuwar neman agaji. Nan da nan masu fushi da fushin wani suka tasam masa da suka bi suka buge sannan suka haushi da duka kamar ba za su barshi da rai ba. Da ƙyar ‘yan doka suka ƙwace shi a hannunsu, rotse ko’ina. Kafin su kai ga offishinsu ma har rai yayi halinsa. Ita kuwa matar aka barta da takaba tana da na sanin cewa da ta yi ko na sata ne ya kawo musu.

<< Bakar Kaddara 4Bakar Kaddara 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×