Sabon Ɓarawo
An yi wani lokaci da aka yi tsananin talauci. Ya zamana abinda mutum zai ci ma sai an yi da ƙyar. A wanna lokaci mutum in ba noma ya yi ba abincin da zai ciyar da gidansa ma gagararsa yake yi. Noman kuma sai wane da wane saboda tsadar rayuwa ta kai intaha.
A cikin wannan hali ne Uzairu ya yi aure. Sai dai ya ci sa'a, da yake iyayen matar manoma ne sun kawo musu gara mai yawan gaske. Ba a daɗe da yin auren ba kuma sai aka. . .