Rabon A Yi
Ladi mace ce mai son ziyarar ‘yan uwa da abokan arziƙi. Tun tana ƙarama ta saba, da wuya ta wuce kwana biyar uku ba tare da ta ziyarci wani makusancinta ba. Wannan hali nata ya sa kowa ke ƙaunarta a cikin danginsu.
A kwana a tashi ba wuya. Wannan hali na Ladi dai har ya bita zuwa girmanta. Watarana sai ta yi nufin zuwa wajen wata ƙanwar mahaifiyarta domin sun jima ba su haɗu ba. Ta shirya takanas ta Kano ta je wannan ziyara. Ta wuni musu a can. Da yamma ta yi sai ta hawo mashin da nufin ta dawo gida. Suna tafe suna hira da mai mashin ɗin har suka shigo cikin layin da ta ce mishi za ta sauka. Can kawai sai ya ji ta yi shiru. Yana ta magana ba ta ce komai ba. Amma dai ya ji ta kwanto masa a jiki. Don haka sai ya tsaya domin ya ji ko ba ta da lafiya ne. Ai kuwa yana tsayawa sai ta faɗo daga kan mashin ɗin babu rai. Ashe wannan shiru da ya ji ta yi, har an zare ran ne. Nan fa ya ruɗe ya fara kuka tare da kuruwar neman taimako.
Kafin ka ce kwabo jama’a sun taru, wasu ma har sun gane matar. Nan da nan aka kai matar asibiti. Shi kuma mai mashin ɗin sai aka tsare shi. Bayan likitoci sun yi ‘yan gwaje-gwajensu sai suka tabbatar da cewa babu wata matsala da ta same ta ko ta jawo mutuwarta. Kawai dai kwananta ne ya ƙare. ‘Yan uwan Ladi suka yi baƙin ciki sosai, suka sa aka saki mai mashin ɗin tunda ba shi da wani laifi. Aka yi ta mamakin irin wannan mutuwa da ta zo mata farat ɗaya.