A guje sukayo wurin Basma domin ceton rayuwarta.
Sunyi iya ƙoƙarinsu wurin fiddo Basma a cikin ruwan amma abun yaci tura, saboda ruƙon da Mandiya tayi mata bana wasa ne.
Ƙarfi suka haɗa suka fizgota daga cikin ruwan.
Tare da Mandiya da ta yi mata mugun ruƙo suka fiddota.
Ganin yadda Mandiya ta koma yasa sauran abokan tafiyar ja da baya in banda Jafar da yake naiman hanyar da zai taimaki Basma.
Tamkar yunwataccen zaki haka Mandiya tayi wurgi da Basma tayo kan Jafar gadan-gadan.
Da nufin cizonshi ta iso takamashi da kokawa sukayi ƙasa. . .