Iskar lokaci ɗaya ta tsaya tamkar anyi ruwa an ɗauke.
Ganin waɗannan halittu ba ƙaramin dugunzuma hankalinsu Basma yayiba.
Jamcy da Basma tuni suka runƙunƙume juna jikinsu na mazari.
Wata mahaukaciyar dariya suka fashe da ida, wadda ta haddasama dajin. Girgiza."Kun ɗauka zaku iya guje mana ne,kunyi kuskure yanzu zaku girbi abinda kuka shuka."
A suƙwane suka yo kan su Jafar tamkar yunwatattun zakunan da suka shekara basuci abunci ba.
Muggan makaman dake hannuwansu Suka fara kaima su Jafar hari da su.
Kowa kagani wurin takanshi yake yana ƙoƙarin ceton rayuwarshi.
In suka. . .