"Insha Allahu matsalarmu tazo ƙarshe da izinin Allah." Jafar ya faɗa yana fuskantarsu Rabson.
Cikin zaƙuwa suka fara tambayarshi ta yaya matsalarsu tazo ƙarshe?.
"Haƙiƙa Alƙur'ani cikinshi akwai waraka, ubangiji ya sanya na tuno da wani malami na daya koyar damu yadda ake karya sihiri da wasu daga cikin ayoyin Alƙur'ani mai girma, domin wannan annobar ta zama Horror da wasun mu suka yi sihirine, kuma da izinin Allah zamu karyashi, dan haka yanzu wasu daga cikinmu zasu tafi naiman ganyen magarya wasu kuma su tafi naiman ruwan da zamuyi amfani dashi. . .