Skip to content
Part 14 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

“Insha Allahu matsalarmu tazo ƙarshe da izinin Allah.” Jafar ya faɗa yana fuskantarsu Rabson.

Cikin zaƙuwa suka fara tambayarshi ta yaya matsalarsu tazo ƙarshe?.

“Haƙiƙa Alƙur’ani cikinshi akwai waraka, ubangiji ya sanya na tuno da wani malami na daya koyar damu yadda ake karya sihiri da wasu daga cikin ayoyin Alƙur’ani mai girma, domin wannan annobar ta zama Horror da wasun mu suka yi sihirine, kuma da izinin Allah zamu karyashi, dan haka yanzu wasu daga cikinmu zasu tafi naiman ganyen magarya wasu kuma su tafi naiman ruwan da zamuyi amfani dashi, dan haka yanzu Rabson da Salma ku zaku naimo mana ganyan magarya guda bakwai.”

Rabson wata irin miƙewa yayi jin ance su biyu zasu tafi.
“Kwarankwatsi dubu babu inda zani, yoce maku akayi Kakata bata sona zaku turamu mu biyu aradu babu inda zani, haka kawai so kuke inje acinyeni shikenan Bunsurulle ya zama maraya.”
Ya ƙarashe maganar yana zare idanu kamar ankama 6era a buta.

“Kai dai kam anyi ragon maza lusari marar amfani, to nida Tk zamu tafi tare daku munzama muhuɗu ko.”
Jamcy ta ƙarashe maganar tana hararar Rabson.

“To masha Allahu, yanzu cikinku wayasan yadda ganyar magaryar yake.”?
Jafar ya jefo masu tambayar yana mai ƙare masu kallo.

“Ni nasani saboda nata6ayin projet akanshi.”
Tk ya faɗa yana hura hanci.

“Ku tabbata kunyi addu’a kafin kubar wurin nan.”

Jafar ya faɗa cikin taushin murya.

Su duka kowa yayi addu’a musamman Rabson a bayyane ya ƙwararo abunshi, Salma ko bata ce uffan ba tana hura hanci tana taka ƙasa da ƙyar haka suka nausa cikin jejin naimo ganyan magarya.

Sunyi tafiya harsun gaji amma basu samu koda itaciyar da zusu tsuguna susha inuwa ba bare kuma ta ganyen magarya.

“Wash!”

Rabson yafada yana riƙe ƙugu kamar zaiyi kuka.

“Ka taka ƙafa muyi gaba yanzu ba lokacin lalaci bane, in kuma kasake muyi gaba mubarka.”

Salma ta ƙarashe maganar tana aikama Rabson kallon banza.

Murmushi Rabson yayi, “to masoyiya Matar Rabson mu tafi.”

Daddagewa tayi ta danna mashi wata gagarumar ashar taɗora da faɗar
“In ka sake kirana matar ka tsaf zani biyemaka mu dambata a wurin nan, maye sai naci saikace talauci Mtssw.”

Fashewa da dariya yayi “in kina tunkuɗo bakin nan sai yayi yanayi da in tsohuwa zata kira tukurr.”

Ya ƙarashe maganar yana kwaikwayar ta.

“Kutt! Amma gayen nan nikake zagi ka kira sunana kana iya shege, yanzu ko zani tumurmusaka ka gane shayi ruwa ne.”
Tk yayo kan Rabson gadan_gadan.

Ruƙoshi Jamcy tayi cikin matuƙar 6acin rai ta fara magana;

“Yanzu naiman abinda muka fito kenan?, kun rinca6e da faɗa, so kuke ayita yimana dauki ɗai_ɗai saboda mugun hali irin namu muntsaya faɗa amaimakon naimo abinda aka aikemu naimowa.”

Kowa tsit yayi suka ƙara gaba naiman abunda suka fito.

Sun ƙara tafiya mai nisan gaske sannan suka iso inda ya kasance ga ganyayen magarya birjik aƙasa.

Hamdala sukayi wani irin farinciki ya ziyarci zuciyoyinsu.

Tsugunawa Tk yayi ya tsinci guda bakwai.

Yajuyo yace masu suyi gaba su koma wurinsu Jafar kawai.

Ihun da Salma ta ƙalla ne yayi sanadiyyar janyo hankalinsu, abinda suka gani ne yayi sanadiyyar daskarewarsu suka kasa koda ƙwaƙwƙwaran motsi.

Mandiyace tsaye cikin mummunar kama, jikinta yayi kacha_kacha da jini, tazarar dake tsakaninsu da Salma batafi taku biyu ba tsakaninsu.

Kafin Salma ta ankara tuni Mandiya tayi wawan tsalle ta dira gabanta, wuyanta ta raruma sukayi ƙasa atare.

Zafi gami da azabar cizon da Mandiya tayima Salma a wuya yasanyata fasa wata mahaukaciyar kuwwa.

Wannan mummunan gani da Rabson yayi yasanya shi sakin wani zazzafan fitsari yana kuka yana kiran “Salma masoyiya shikenan bakida rabon ganin bunsurulle, naci gurin yanka maki shi in munyi aure muci amarci dashi.”

Ganin surutan bazasu fishsheshi ba yasanya shi runtse ido ya ɗauki wani reshen iccen magarya daya karye ya faɗo.

Mandiya da ta riƙe da wuyan Salma jini nata tsiyaya.

Shammatar Mandiya yayi ya buga mata iccen a tsakiyar baya, sakin wuyan Salmatayi tare da fasa wata firgitacciyar kuwwa.

Ganin haka yasa Rabson fizgo hannun Salma data galabaita ga jini na ɗibarta, ganin haka yasa su Jamcy maramasu Rabson baya sukaci gaba da gudu.

Gudu suke na ceton rayuwa ga Rabson guy riƙe da hannun Salma.

Da ƙyar da ji6in goshi suka isa inda su Jafar suke, suna isa Salma ta zube ƙasa tana maida wahalallen numfashi kamar ranta zaifita.

Ganin irin jinin da Salma ke zubdawa yasa Biba cire kingin gutsuren ɗan ƙwalinta ta ɗaurema Salma wuyan.

Ganin taimakon da Biba tayima Salma ya sanya Salma jin wasu hawaye sun wanke mata fuska, yanzu gashi mutanen data gama wulaƙantawa hartana iƙirarin inta koma gida saitasa an ɗauresu, yau sune ke taimakonta, lallai duniya kabita sannu ba matabbata bace.

Jitayi wuyanta kamar ana hura mata wuta ansa wuƙa ana daddaka mata a wuya.

Jin wannan sabuwar azaba ya sanya ta fasa wata ƙata tareda faɗuwa ƙasa tana harbe_ harbe.

Sunyi matuƙar mamakin baƙon yanayin dake shirin samunsu, sudai iya saninsu sunsa ko harror yacijeka baka abinda Salma keyi.

Babban abinda ya ƙara tayar da hankalinsu bai wuce ganin cikin lokaci ƙanƙani jikin Salma yafara komawa green wasu jijiyoyi naƙara bayyana.

Ganin haka yasa Jafar umartar matan dasu danne mashi Salma, haka akayi suka danneta da ƙyar tana fizge_fizge ya fara yin auziyyah yayi basmala ya fasa karanto suratul baƙara cikin daddaɗar muryarshi.

Jitayi karatun da yake mata tamkar yana watsama wuta feturne tana ƙara ƙonata, ƙoƙarin fizgewa take ganin haka yasa Rabson riƙe hannuwanta gam.

Jafar bai tsaya da karatun ba face ƙara himma da yayi wurin rero karatun.

Lura sukayi Salma ta daina motsi, hankalinsu yayi mummunan tashi sun ɗauka mutuwa tayi, saida Jafar yace masu bacci ne ya ɗauƙeta sauƙi ne taji.

Fuskar kowa ka kalla wurin jimamin wannan al’amari yake.

Jafar ne yayi ƙarfin halin fara masu bayani kamar haka;

“Tabbas wannan al’amari sai mun tashi tsaye mundage da addu’a, lokacinda zaku tafi gudun faruwar haka saida nayi maku tuni da kuyi addu’a, inagani kowa yayi amma Salma taƙiyi, to kunga abinda ake gudu gashinan yadda ta kasance da ita, jikina nabani in bamu gaggauta naiman ruwaba mukayi mata addu’a da ganyen magaryar nan ba to bashakka bazata ɗauki lokaciba zata zama horror.”

Sunyi na’am da wannan shawara sun jinkirta Salma ta tashi daga bacci su ƙara gaba su naimi ruwa.

Anɗauki lokaci sosai sannan Salma ta fara buɗe idanunta da take jin sunyi mata nauyi.

Tana ida buɗesu ta sauje su kan Rabson da tun lokacin da yaga ta fara motsi ya kafeta da ido.

Abinda Rabson yagani cikin idanun Salmane ya sanyashi miƙewa jikinshi na mazari.

Idanunta wannan baƙin na idonta ya rikiɗe ya koma green.

Ganin wannan al’amari Jafar ya umarcesu suyi azamar tashi su samo ruwa.

Salma kallon jikinta tayi da tufafin harsun fara yagewa, ga ƙasar da ta kwanta ƙasa duk ta ida bata jikinta ta koma kamar wata mahaukaciya, hawayen dake jerangiya afuskarta ta sharce, wai yau i ta ce ahaka, Salma da take ƴar gayu mai ƙwalisa bashakkayanzu ta koyi darasin yadda rayuwa take.

Nas da Kulu ganin yadda Salma ta koma yasa suka matsa daga inda take cike da tsoronta azuciyoyinsu.

Ganin su Nas sun matsa daga inda take ta sakejin wani sabon kuka ya kufce mata, wai yau i ta ce ake gudu, lallai rayuwa ba tabbas.

Biba ce take kwantar mata da hankali ta ɗauki Ƙaddara musulmi da ɗaukar ƙaddara mai kyau ko akasin haka aka sanshi.

Wata soyayyar Biba ce Salma taji ta ƙara shigarta da kuna nadamar abubuwanda ta aikata masu a baya.

Biba ita ta kama kannun Sallam ta ranƙwafo ta aza wuyanta bisa kafaɗar Biba sukaci gaba da tafiya.

Sunyi tafiya mai nisa sosai suka isa wani wuri da ruwa ke gudana ta cikin wani dutse.

Su duka nan suka zube suna masu kamfatar ruwan da hannayensu tare da bismala suna kaiwa bakunansu.

Basma jitayi wani jiri na ɗibarta, bashiri taji ta kaima Jafar karo tayi ƙasa tareda dafe kanta dake bara zanar tarwatsewa, ga jikinta da saura kaɗan ya ida komawa green……….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Tafiya 13Bakar Tafiya 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×