Skip to content
Part 15 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Biba da Kulu da sauri suka riƙo Basma da ta fara chanza kamanni.

Ganin haka yasa Jafar juyawa domin samun wani abu wanda zai iya zuba ruwa ciki, ya duba ko ina baisamu inda zai zuba ruwanba, chan gefenshi ya hango wani fasasshen ƙoƙo, ɗaukoshi yayi tare dayin basmala ya wankeshi tas, ya ɗauki ganyan Magarya guda bakwai ya zuba cikin ruwan tareda kanga bakinshi kamar zaisha ruwan ya fara karanto fatiha iskan bakinshi na bugun ruwan, saida ya karanta fatiha ƙafa bakwai, ya nufo inda Basma ke kwance batare da tasan wandake kantaba.

Biba ya miƙama ruwanya umarceta da ta bata ruwan ta kur6a sauran kuma ta shafa mata ajiki.

Kulu da Jamcy suka taimaka mata ta samu da ƙyar Basma tayi kurba biyu, sauran ruwan ajikinta ta ida shafe mata ajiki, Jafar umartarsu yayi su Kwantar da ita.

Matsawa sukayi daga inda take.

Kama an tsikareta da allura haka tayi wuf tamiƙe zaune tafara kwarara wani irin amai baƙiƙirin, tamkar zata amayo ƴan cikin ta.

Fuskarta kaɗai zaka kalla ka tabbatar ta wahala iya wahala.

Tana gama aman tayi baya luuu! Ta sume.

Biba hada gudunta zata kamo Basma Jafar yayi saurin tsaidata.

“Alhamdulillah da alamu maganin ya fara aiki, kada wanda ya matsa inda take har sai ta farka.”

Cikin jimami da matuƙar tausayin Basma su duka suke kallonta kwance kamar matatta.

Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ne ya sanyasu matuƙar kaɗuwa zuciyoyinsu suka fara bugawa da sauri da sauri.

Aman da Basma tayine ya zama wasu irin baƙaƙen tsutsotsi sunata bille_bille, lokaci ɗaya suka kama da wuta suka ƙone ƙurmus.

Jikin su yayi matuƙar sanyi, wasunsu wani sabon imani ya riƙa shigarsu.

Dubansu suka kai ga Basma dake kwance, ilahirin jikinta yadawo lafiya lau takoma ainahin Basmarta, sai dai abinda ba’a rasaba na baƙar azamar da suke sha a wannan Baƙar tafiya.

Hamdala Jafar yayi tare da kallon Salma data ke raku6e wuri ɗaya tamkar wata mairainiya.

Itama ruwan ya ɗebo yayi mata ƙwatan ƙwacin yadda yayima Basma.

Tana gama shan ruwan ta maka sauran a kanta, yana ida isowa inda Mandiya ta cijeta ta ƙwala wata gagarumar ƙara tareda faɗuwa ƙasa ta fara bille_bille tana tada ƙura tamkar ana yaƙi.

Mamaki ya kashesu Jafar ko motsi suka kasayi, su dai sunyi tsaye suna kallon ikon Allah.

Ihun da Salma ke ƙwalawa ta tsaida tare da dafe wuyanta, alamar kamar wani abu zai fito tacikin wuyanta tayi, ba shiri ta janye hannunta tare da ƙwala ƙarar da tafi ta ɗazu jin fitowar wani abu daga wurin.

Wani abu ne mai kama da maciji ya fito daga cikin wuyanta yajo kansu Rabson dake gefe tamkar yayima Salma kuka.

Ganin wannan abu yayo kansu a take suka tarwatse kowa yayi ta kanshi, Nas da Tk sune kan gaba wurin gudun.

Rabson tinti6e yayi da wani dutse atake yafaɗi ga wannan halitta tayo kanshi baki buɗe.

Ihu yake yana kuka ga hawaye ga wata majina sun wanke mashi fuska.

Ganin ya kasa tashi dagewa yayi ya miƙe tanufi inda rafin nan yake, cikin rashin sa’a yasake faɗuwa yacigaba da mulmulawa ya faɗa cikin ruwan.

Wannan halitta ita azabar da takeji ajikinta ta sanyata biyo duk wanda tagani gabanta, kamawa tayi da wuta ta fara ƙonewa tana wani irin kuka marar daɗin sauti.

Ganin wannan halitta tagama ƙonewa yasa su nufar inda Salma ke kwance, kamata Biba tayi suka miƙar da ita.

Wani baƙin ruwane ke fita awuyan Salma, saidai Biba ta yanki gefen hijabinta suka tare ruwan.

Yadda kasan fanfo inya fara zuwa kafin yayi ƙarfi yana kawo ruwa haka wuyan Salma ke tsiyayar da wannan ruwan.

Ƙallen hijabin Biba sai da ya gama jiƙewa da ruwan sannan ruwan ya tsaya, jefar da ƙyallen sukayi atake ya kama da wuta ya kone shima.

Hamdala sukayi ganin jikin Salma ya dawo dai_dai, cizon dake wuyanta kaɗai ya rage ya warke.

Lura sukayi babu Rabson, motsin da sukaga ruwa nayi ya tabbatar masu da Rabson na cikin ruwan, Jafar yayi ƙarfin halin fiddo Rabson da yayi tsamo_tsamo, da ruwa.

Jafar faɗa ya fara yimashi akanmi zai faɗa ruwa bayan yaga halinda suke ciki.

Baki yabuɗe da ƙyar ya tofar da ruwanda ya cika mashi baki yafara magana;
“Kawai sai in tsaya wannan halittar ta cijeni nima inzama Horror abanza, amma kaga inna faɗa ruwa in na mutu ciki nayi shahada.”

Ba Jafar kaɗai ba harsu Nas halinda suke ciki bai hanasu fashewa da dariyaba saboda jin abinda Rabson y faɗa.

Bayan sun lafa da dariyar
Jafar ya fara masu bayani kamar haka;

“ALHAMDULILLAH godiyata tabbata ga Allah mai fidda matacce acikin rayayye, kuma ya fitar da rayyaye acikin matacce, cikin ikonshine ya sanya abokan tafiyarmu suka samu lafiya, Muna ƙara miƙa godiyarmu ga Allah, yanzu abinda yayi saura kuma yafi komi haɗari shine mu naimo su Mandiya dasuka zama Horror suma muyi masu magani, Abinda zamuyi shine yanzu fantsama zamuyi cikin jejin mu jawosu saimu rugu izuwa wannan rafin mai ruwa mu faɗa ciki, mu kuma dama munriga da mun yima wannan rafi addu’ar da mukayimasu Salma, idan Allah ya ƙaddara suma su komo mutane.”

Ya ƙarasa maganar yana dubansu Rabson.

Kowa yayi na’am da wannan shawarar sunan sun fara shirin tinkarar su Mandiya.

Basma tunda ta farka daga nannauyan baccin daya ɗauketa take godiya ga Allah, ga wata gagarumar nadama da kewar mijinta da kuna Ɗanta, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka wanke mata fuska ba, tayi kukanta mai isarta tana mai addu’ar Allah ya maidata gida kodan ta gyara kuskuren da tayi a baya.

Kwanansu biyu a wurin jikin Basma da Salma ya warware sunji sauƙi sosai sun warke, tun bayan warkewarsu Salma ta dawo cikin hankalinta take daraja ɗan adam, wani irin girma takema Jafar da yayi silar warkewarta.

A yaune zasu fita naiman su Mandiyi, kowa ya kimtsa.

Alama sukayima rafin domin in suka jawo su Mandiya su gane wurin.

Nausawa suka ƙarayi cikin jejin suna masu addu’ar samun nasara.

*****
Cikin tsawa da hargagi yake magana tamkar zai kai mata naushi.
“Yau tsawon kwana goman dana ɗibar maki ya cika, dan haka kije gidanku na sakeki saki ɗaya, duk radda ɗiyata ta bayyana zani naimeki, yanzu zanije in samu shugaban sojoji abokina da kika sani in naimi taimakonshi atura wasu iyakar dajin koda Allah zaisa su Salma suna fitowa ayi sa’a su maido manasu gida, maganar ƙarshe da zaniyi maki i ta ce kitattara duk abinda kikasan naki ne ki bar gidan nan kafin in dawo.”
Alhaji Abdallah mahaifin Salma ya ƙarashe maganar zuciyarshi na matuƙar yimashi ƙuna.

“Dan Allah ka gafarceni wallahi nayi nadama, kada ka tona mani asiri, yanzu innaje gida muzanice?, dan Alkah ka rufa mani asiri.”
Ta ƙarashe maganar muryarta na sarƙewa saboda kukan da take cizga.

Bai ko kalli inda take ba yayi ficewarshi ya barta nan tsugunne.

*****
Basu yi nisa sosai da inda suka baroma suna cikin tafiya Jamcy taji kamar wani abu ya gilma da gudu ta bayanta.

“Wayyo Allah! Yauni Jamila nashiga ukku.”
Ta ƙanƙame jikin Tk tana ƙyarma.

“Miya faru Jamcy?, yau ke ce ke faɗar ainahin sunanki wanda kin hana mutane kiranki da Jamila sai dai Jamcy, to wai mima ya firgitaki har haka.”?
Tk ya Ƙura mata ido tare da jefo mata tambayar.

“Uhm! Ai wani abu nagani ta baya ya gilma.”

“Haba Jamcy babu komi fa, kawai tsorata kikayi.”

Jinin Jamcy kan akaifa sukaci gaba da tafiyar.

Kamar daga sama Jamcy taji an warci hannuta an jawota da ƙarfin tsiya ta faɗi ƙasa.

Ƙarar faɗuwarta ita tayi sanadiyyar jawo hankalinsu Jafar.

Ganin Jamcy ƙasa warwas ga Mandiya kuma sunata kokawa yasa Jafar fara dube_dube ko zai ga wani mabigi, sai dai duk iya dube_dubenshi bai samu komi ba.

Ganin bai samu komiba ya dunƙule hannuwanshi ya kaima Mandiya wani wawan bugunda yayi sanadiyyar rabata da jikin Jamcy ta faɗi chan gefe, ganin aka ya sa su duka suka fara gudu Mandiya ta mara masu baya.

Gudu suke suna waigen mandiya har suka iso inda rafin nan yake, basu bata lokaciba suka faɗa ciki, Mandiya da idanunta suka rufe itama bin bayansu tayi ta tsunduma cikin ruwan.

Ida isarta cikin ruwan yayi dai_dai da ƙwala wata gagarumar kuwwa da tayi ta haddasa ma wurin amsa kuwwa…

<< Bakar Tafiya 14Bakar Tafiya 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×