Skip to content
Part 17 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

الحمدلله!
الحمدلله!!
الحمدلله!!!

“Assalamu alaikum, kiranka nayi in sanar da kai ansamu yarinyar nan yanzu haka gamunan motar asibiti ta kwaso mu domin suna cikin mawuyacin hali.”

Cikin hanzari gami da zaƙuwa daga ɗayan 6angaren aka fara managa.

“Kuyi sauri kukaisu asibiti, nima gani nan zuwa.”

Asibiti mafi kusa Private hospital suka kai su, suna isa emergency aka nufa dasu likitoci suka duƙufa ceton rayuwarsu.

Alhamdulillah ansamu nasarar ceton rayuwarsu, anyi masu allurar bacci da sun tashi zasu dawo cikin hankalinsu.

Dukkansu a ɗaki ɗaya aka ajesu, gadajensu ajere suke.

Ƙofar ɗakin likitocin suka jawo, suna niyyar barin wurin.

Har tuntu6e yake ya kama hannun likita ya riƙe gam yafara magana muryarshi na Kyarma.

“Likita!, ina Mamana?, ina ɗiyata?, wane hali take ciki?”

Ya ƙarashe maganar cikin zaƙuwar jin amsar da zai bashi.

“Ka kwantar da hankalinka, yarinyarka tana nan lafiya Ubangiji ya taimakemu munyi nasarar ceto rayuwarsu, yanzu allurar bacci mukayi masu da sun tashi insha Allah zasu dawo cikin hankalinsu, saidai zamu riƙesu harsu dawo ciki hayyacinsu, domin yanzu suna buƙatar kulawa jikinsu ba ƙwari.”

“Zani iya shiga inganta?”
Ya faɗa a hanzarce.

“A’a, yanzu suna buƙatar hutu sakamakon allurar bacci da mukayi masu.”

“Zaniyi haƙuri harsu tashi, ina nan.”

Ranar nan Alhaji Abdallah ya yini bayan ya sallami yaran abokinshi da suka samo su Salma, tare da yima amininshi godiya.

Ɗakin yayi tsit bakajin komi sai ƙarar A.C da ta gauraye ɗakin, A hankali ma’aikatan jinya mata suka turo ƙofar ɗakin domin bin umarnin Ogansu daya umarce su suzo suka insun farka, su duddubasu sunje kan Rabson, yatsun hannunshi yafara motsawa tare da ƙoƙarin buɗe idanunshi.

Ida buɗesu yayi ya saukesu akan ma’aikaciyar jinyar dake kanshi, a firgice ya ida buɗe idanunshi tare da ƙwala wata mahaukaciyar kuwwa.

“Innalillahi, nashiga ukku, lawakiri ki taimaka kada kiyi mani komi, wayyo ashe mutuwa nayi, yau ni Rabi’u na lalace kodai lahirama akwai Horo, wayyo bunsurulle shikenan na mutu na barka.”
Yana ƙarashe maganar yayi tsalle ya diro daga saman gadon yayi hanyar ƙofa tare da cigaba da darza ƙara yana naimp..an taimako.

Sistocin kallonshi suke suna mamaki kodai baida hankali, ko kuma haɗarin daya samune ya maidashi haka.

Rabson jin ƙofa akulle babu hanyar fita ya juyo wutsiya zage yafara bin sistocin da kallo.

Wani tunani yazo kanshi, wata kujera dake nesa dashi ya raruma ya nufi sistocin da niyyar zai Make kawunansu sumutu kowa ya huta.

Ganin haka suka ƙara tabbatarwa bashakka Rabson mahaukacine, ihu suke suna naiman taimako, da ƙyar suka buɗe ƙofar suka fice a guje Rabson ya mara masu baya.

Alhaji Abdallah dake zaune yana dakon farfaɗowar Salma ganin mutane sun nufi inda yake a guje ya sanyashi miƙewa ya riƙe Rabson.

“Bawan Allah mizakayi masu daka biyosu da wannan makamin a hannu.”?

“Kada ka yarda da waɗannan Horunan a nan lahirar ma biyoni sukayi su ƙara kashewa, dan haka barni dasu yanzu inga bayansu duk in kwaɗe masu kawuna da wannan kujerar.”

Jin wannan wautar ta Rabso ba sistocin dake 6oye bayan Alhaji Abdallah ba har shi kanshi saida ya tuntsure da dariya.

“Bawan Allah waya ce maka ka mutu?, kata6a ganin wanda ya mutu yana magana har ya riƙa fallawa da gudu da ƙafafunshi, alamu sun nuna kai majinyacine ba mutuwa kayiba nan asibitice aka kawoka.”

Wata iriyar kunyace ta lullu6e Rabson jin ashe yana raye bai mutu ba.

Likitane ya ƙaraso wurin jin hayaniya ta yawaita.

Ganin Rabson tsaye yasa likita fara tambayarshi miya fiddoshi?.

Nan Alhaji Abdallah ke sanarda likita abinda ya faru.

Saida likitan yayi dariyarshi mai isarshi sannan ya lalla6a Rabson akan ya koma ɗakin da aka kwantar dashi.

Suna tura ƙofar ɗakin suka hango su Jafar duk sun farka suna jingine da gadajensu.

Salma ganin mahaifinta da tayi tamkar a mafarki yasa tayi wani tsalle ta rungumeshi batare da tunanin shiɗinne ko bashi bane.

Wani kukane ya kubce mata , ashe tanada rabon sake ganin mahaifinta, tana roƙonshi ya yafe mata ta tuba da sa6ama umarninshi, bazata sake tsallake maganarshi ba.

Rarrashinta yake yana jin wani sabon tausayinta na ratsashi.

Kowa wurin sai yanzu ya fahimci wannan shine mahaifin Salma.

Rabson da dai ya lura tabbas mutumin ɗazu shine sirikinshi,wata irin kunyace ta rufeshi, sulalewa yayi ya haye gado tare da rufe ido kamar yana bacci.

Bayan komi ya lafa, mahaifin Salma odar abinci yayi masu sukaci suka hantse, domin rabonsu da irin wannan abincin tun kafin su fara Baƙar tafiya.

Salma ita ta gabatar da sauran abokan tafiyarta ga mahaifinta bayanta ƙwashe labarin dukkan abinda ya faru a tafiyar ta faɗa mashi, yaji irin gudumawar da Jafar da Biba suka bata a wannan tafiyar.

Juyowa yayi da nufin yimasu Jafar godiya, saidai suna haɗa ido da Jafar yaji gabanshi yayi wata irin mummunar faɗuwa
Saboda kama da Jafar yayi da wani ƙanenshi daya 6ata.

Godiya yayi tare dayi masu alƙawarin zai sanar da iyayensu Halinda suke ciki zai samesu har gidajensu, suyi masu kwatancen unguwannin da suke bama yara zai aikaba shi da karan kanshi zaije.

Kamar yadda yayi alƙawari tunda safe ya fara da gidansu Jafar, ya aika ayimashi da matar gidan, ƙanwar Jafar ce ta leƙo, ya sanar da ita halinda ake ciki tare da faɗa mata halinda ake ciki, rugawa tayi ta faɗama Ummansu abinda ke faruwa.

Suna isowa har Alhaji Abdallah ya 6ace a wurin ƙurar da motarshi ta tayar kaɗai ta rage, a hanzarce suka shirya suka nufi asibitin.

Lokacinda Alhaji Abdallah ya faɗama Kaka jikanta na asibiti, kuka ta fara tana shikenan Rabi’unta zai mutu shima ya barta.

Saida Alhaji yayita kwantar mata da hankali.

Shiryawa tayi itama ta nufi asibitin.

Da habib yaji abinda ya samu Basma bai wani kaɗuba dominshi yanzu matarshi Hanan ta gama mashi komi.

Badan yasoba sai dan Hanan da ta sanya baki ta lalla6ashi akan yaje ya dubo Basma, asibitin yanufa kai tsaye yana jin wani irin haushin Basma a zuciyarshi.

Haka yabi gidajensu Kulu, Jamcy, tk, da Nas ya sanar da iyayensu.

Hanyar asibiti ya ɗauka domin sanar dasu Jafar ya cika alƙawarin daya ɗauka.

Yana isa Kaka na isowa da gudu ta shige ɗakin tana mararin ganin tilon jikanta.

“Labson ɗina, wayyo jikana sannu , haka ka koma duk kafita hayyacinka?”

Ta ƙarashe maganar batare da tasanin ko sunan Rabson ɗin bata faɗa dai_dai ba.

Hannuwanta ya kama ya riƙe gam Tamkar za’a ƙwace mashi ita.

“Da farko dai kaka yanzu Rabi’u nike ba Rabson ba, kaka ki yafeni dan girman Allah, bazani ƙarayimaki gardama ba, nabi Allah nabiki Kakata.”

“Tuni nayafe maka Rabi’u na, kullum banida gurin daya wuce Allah ya maidomani kai marayan Allah.”

Shigowar iyayensu Kulu yasa kaka yin shiru.

Su Kulu kam sunsha bala’i da masifa wurin iyayensu, dan Nas Mamanshi cewa tayi saita kwara kanshi da bango zata huce, Momyn Jamcy kuwa yi tayi kamar zata jawota daga gadon ta karya mata ƙafar da ta yi alƙawari.

Alhaji Abdallah mamakin halin iyayensu Jamcy ya bashi mashi mamaki, haƙuri ya rinƙa basu akan suyima Allah godiya da bayyanar ƴa’ƴansu basu hau bala’i da masifa ba.

Jikinsu sanyi yayi sukayi tsit.

Umman Biba ce da ƙanwarta suka iso.

Har kukan murna saida Mahaifiyar Biba tayi tare dayima Allah godiya.

Biba kuwa tsabar farin ciki jitake kamar ta koma cikin mahaifiyarta ta kama ta ta riƙe gam.

Sallamar maman Jafar ce ta sanya kowa kallon ƙofar.

Zabura Alhaji Abdallah yayi ya miƙe tare da nuna Maman Jafar ya furta Hindatu!.

Maman Jafar itama kallonshi take da mamaki ta furta Abdallah………

Juwar dayaji tana ɗibarshi ce tasashi yayi saurin zamewa ƙasa tare dayin zaman ƴan bori.

Hindu kuwa wasu hawaye ne taji sun wanke mata fuska, wai yau i ta ce take ganin Abdallah, anya kuwa ba mafarki takeba.

Jafar ganin mahaifiyarshi yasa yayi yunƙurin tashi.

Ganin haka ummansu tayi saurin ƙarasowa wurinshi cike da farin ciki marar misaltuwa.

Alhaji Abdallah hawaayen fuskarshi ya sharce, ga wani gumi daya tsatstsafo mashi ta ko ina ajikinshi.

Kallon Jafar yayi yaƙara tabbatarwa tabbas yanzu yaƙara ganin kamarsu da husaininshi.

Abdallah tashi yayi ya isa gabansu Hindatu tare da zaunawa amma bakinshi ya kasa furta koda kalma ɗayace.

“Umma! Dama kinsan Mahaifin Salma?, koɗan uwankune?”

Ya ƙarashe maganar ya mai ƙara fuskantar Mahaifiyarshi.

“Ɗana ne kai, Jafar tunda na haɗa ido dakai jikina yabani kai ɗin jinina ne, Jafar Ashe kaine ɗan, ɗan uwana Husaini daya bata, babu inda ban bancika ba domin ganin nasamuko amma abin yaci tura ban gankuba.”

Alhaji Abdallah ya ƙarasa magana muryarshi a matuƙar karye.

Hawayen dake fuskarta ta share ta ɗora da faɗar.

“Tun bayan rasuwar iyayenku, Husaini yashiga wani mawuyacin hali, saiya zaunar dani yayita yimani wasu maganganu masu kama da wasiyya, ana cikin haka Allah ya nufeshi da 6acewa inda haryau bamu ganshiba.”
Kukan da taji yana naiman ƙwace matane yasata yin shiru.

“Mahaifanmu mu biyu suka haifa taƙwaye, muntashi muna matuƙar ƙaunar junanmu, har mahaifanmu suka rasu lokacinne kuma Husaini ya bata, na nemeku lungu da saƙo amma ko labarinku bansamuba, kullum cikin yima iyayenmu addu’a nike da Husaini har izuwa yau da Allah Ya bayyana mani ku.”

Jafar ji yayi anya ba mafarki yake ba, ace wai yau shine gashi ga yayan mahaifinshi, Allah mai yadda yaso, yana ƙara roƙon Allah ya bayyana mahaifinshi aduk halinda yake ciki.

Salma wata gagarumar kunyace ta ƙara rufeta, wai yau ace wanda ta gama wulaƙantawa ashe yayantane, yanzu ta ƙara tabbatarwa ɗan adam ba abin wulaƙantawa bane, wata sabuwar nadama taji tana ƙara shigarta.

Mahaifiyar Habib da Alhaji Abdallah gaisuwar yaushe gamo suka hauyi ciki da farin ciki da ƙaunar juna.

Sallamar Habib dasukaji ta maido hankalinsu ga ƙofar.

Basma tunda taga Habib wani farin cikin marar misaltuwa ya ziyarci zuciyarta, ashe tanada rabon ganin mijinta farincikinta, tana ƙara miƙa godiyarta ga Allah.

Bayabo ba fallasa bayan gaisawarsu da ƴan ɗakin ya dubi Basma yana mata ya jiki.

Ba ƙaramin mamakin Habib Basma tayiba, ya matuƙar chanza mata sai wani shareta yake ga wani haske da yayi da wata ƙiba da yayi abinshi.

Haƙuri ta hau bashi tana kuka ya yafe mata tayi nadama, ko kallonta baiyi ba ya furta naji kanshi na sunkiye yana kallon screen ɗin wayarshi.

Tamkar Alhaji Abdallah zai maida su Hindu da Habib ciki haka ya riƙa nuna masu soyayyah.

Batare da sanin su Hindu ba Alhaji Habib yaje yasamu wasu malamai yayi masu fatawar ɗan uwanshi da yayi shekara ishirin da bacewa yabar mata shin zai iya auren matar da ya bari.?

Bayan gama tattaunawarsu sun yimashi fatawa iya iliminda Allah ya hore mashin cewar zai iya aurenta.

Farin ciki marar misaltuwa yaji acikin zuciyarshi, domin shidai harga Allah yanada gurin auren Hindatu kodan ya taimaka mata, bai da gurin ganinta cikin wahalar rayuwa.

Ba ƙaramin artabu yayi da Hindatu ba kafinta amince da auren.

Sai da suka shafe wata huɗu a asibiti lokacin kowanensu ya samu lafiya yayi ƙiba abinshi.

Soyayya mai ƙarfi ce ta ƙara shiga tsakanin Jafar da Biba har iyayensu suka fahimci abindake faruwa, sunyi murna sosai domin ba wanda zai guji haɗa zuri’a da Jafar.

Oga Rabson ma yanzu Salma ta bada haɗin kai, soyayya suke sha ba kama hannun yaro.

A yau ne likita yayi alƙawari sallamar su saboda yaga sun warke yadda yake buƙata.

Sabo shi akema kuka ba mutuwaba.

Fuskokinsu yau suna cikin damuwa da kuma jimamin rabuwar da zasuyi.

Rabson hada hawaye na rabuwarsu da abokan tafiya.

Su Kuluma hada hawaye sukayi, ana kuka suka rabu da juna tare da yima juna fatan alkhairi.

Alhaji Abdallah bai yarda Hindu tashiga gidanshiba saida igiyoyin aurenshi akanta.

Bayan su huta Salma ke tambayar mahaifinta ina mahaifiyarta?, tunda aka kai su asibiti baga tajeba.

Nan ya sanar da ita abinda ya faru.

Allah sarki ɗa da uwa sai Allah, kuka Salma ta riƙayi tana roƙon mahaifinta akan ya dawo da mahaifiyarta.

Dakatar da ita yayi, ya sanar da ita shifa yanzu yayi aure ya auri Hindu.

Jafar da Salma sunji daɗin wannan al’amari, amma Salma tana addu’ar Allah ya huci zuciyar mahaifinta ya maido mahaifiyarta.

Alhaji Abdallah da Hindu soyayyarsu sukeyi hankali kwace. Su Hajiya Zaliha ana gida ana buga zawarci.
Rabson tsabar murna da farin ciki yana Shiga gidan yayi wuf ya kwance bunsurulle ya ɗagashi rama yana hajijiya dashi yana dariya yana murna.

Bunsurulle jin wannan jijjigashi da ake ya tabbatar mashi lallai Rabson yadawo, shima kuka ya riƙayi.

“Yau ni naga lalata, Rabi’u daga dawowarka zaka dasa daga inda ka tsaya?, yanzu saika karya busurun nan, kasaukoshi nace maka.”

“Kaka kibarni yaushe rabonda in ganshi, bakiga yadda yake farin ciki ba shima.”?

“Kaci gidanku nace! Maza saukeshi.”

Yana saukeshi Bunsurulle ya manne mashi, duk inda yayi yana biye dashi.
Ba’a ɗauki lokaciba Alhaji Abdallah ya ɗauke kaka da Rabson ya basu wani haɗaɗɗen gida tare da ɗaukar Rabson aiki a kamfaninshi na sarrafa shinkafa.

Murna da farin ciki ba’a magana wurin kaka da Rabson, Kaka ƙauye taje ta sanar da ƴan uwan mahaifin Rabson sukaje naiman aure gidansu Salma.

Alhaji Abdallah ya karramasu inda yasa bikin wata ukku.

Abdallah bai manta da gidansu Biba ba, suma gida ya ƙyara masu ga kayan abinci daya loda masu a store.

An haɗa bikin su Jafar danasu Rabson nan da watanni ukku.

Da ƙyar da ji6in goshi Hindu ta samu Alhaji ya yarda zai maido Hajiya Zaliha.

Tayi matuƙar mamaki data dawo ta iske gidan da wata mata.

Salma ta kwashe komi ta sanar da Mahaifiyarta.

Kuka Hajiya Zaliha ta riƙayi tana nadamar abinda ta aikata, tana zaman_zaman ta ita ɗaya a gidan mijinta, yanzu gashi nan i ta ce hada kishiya, ta ɗauki ƙaddara tare da wata irin nadama datayi, domin yanzu ta ɗauki darasin rayuwa.

Zaman lafiya suke tsakaninta da Hindu tare da girmama juna.

Suna isa gida Basma ƙamshin wani daddaɗan abinci ne ya daki hancinta.

Abinda ya ɗaure mata kai bai wuce ita dai tasan Habib bai iya girki ba balle tace shi yake girkin.

Matashiyar budurwa da taga tafito da tsohon ciki tana tafiya a hankli, hannunta riƙe da Walid daya sha wanka ansa mashi kaya masu kyau sai ƙamshi suke zubawa.

Gabantane ya yanke yafaɗi dafe ƙirji tayi tare faɗar.

“Yau ni Basma nashiga ukku! Minike gani haka?, Habib yaushe kazama ɗan iska ka aje mace gida harda ciki dan kaga baninan.”

Kallon bakida hankali Habib yayi mata.

“In kika sake bakin ki ya ƙara faɗar kalma ɗaya mara daɗi ga mamata zani shayar dake mamaki, wannan da kike gani wallahi badan itaba da yanzu sunanki bazawara, ita taita rarrashina harna yarda inci gaba da zama tare dake, dan haka ki shiga hankalinki.”

Wata irin ƙuna taji zuciyarta nayi mata, wai yau i ta ce da kishiya, ita kam ta gama shiga ukku, rayuwa ta koyar da ita darasinda harta mutu bazata manta ba.

Hannu tamiƙa da nufin ɗaukar Ɗanta Walid, tsalle yayi ya fashe da kuka tare da maƙalƙalewa jikin Hanan yana magana cikin hausar da bai ida ƙwarewa ba.

“Wayyo Momy foyeni, wannan matar bani sonta kice kada ta ɗaukeni nidai.”
Ya ƙarashe maganar yana ci gaba da kuka.

Basma jin abinda Ɗan cikinta ke faɗa jitayi ƙafafunta sun daina ɗaukarta sulalewa ƙasa tayi tare dayin zaman ƴan bori ta saki wani marayan kuka.

Habib tsoki yayi tare da shigewa ɗakin Hanan.

Hannan bin bayanshi tayi takai walid ɗakin ta ajeshi itakuma ta fito.

Kuka Basma keyi tamkar ranta zai fita, i ta ce yau ɗan da ta haifa yake gudunta yama manta da ita, wannan duk laifintane ita tajama kanta, kuka ta fashe dashi tare da ɗaga hannuwanta sama.

“Ya Allah ka yafe mani, Allah ni mai laifice a gareka na sa6ama mijina Allah ka yafe mani.”
Kukan dayaci ƙarfintane ya sanyata yin kasa cigaba da addu’ar.

Kafaɗunta ta dafa
Cikin taushin murya ta fara mata magana.
“Kiyi haƙuri Basma, banshigo gidan nan ba dan in fiddaki ki kwantar da hankalinki, insha Allah zani shawo kan mijinki, Walid kuma sai a hankali zai saba dake.”

“Nagode maki Hanan Allah yayi maki albarka, Allah ya zaunar damu lafiya.”

Hanan tasha wahala kafin Habib ya yarda ya yafema Basma, zaman lafiya suke a gidan nan duk da a yanzu Habib ya yafison Hanan akan Basma, amma yana ƙoƙarin 6oyewa, sai dai har yanzu Walid yaƙi yarda da Basma shicewa yake Hanan ce Momynshi.

Allah ya sauki Hanan lafiya, tahaifi tagwaye mace danamiji.

Basma anata rawar ƙafa kamar ita ta haihu kullum macen na wurinta, da hanan taga soyayyar da take nunama babyn saita barmata ita.

Haka sukaci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Su Nas iyayensu yanke shawarar haɗasu aure sukayi.

Ba’a ɗauki sati biyu ba aka ɗaura aure Jamcy da Tk, Kulu da Nas, sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya.

*****
Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya.

A yau jama’a da dama suka shaida ɗaurin auren Rabi’u Mukhtar da Salma Abdallah, tare da Jafar Abdurrahman da Habiba Hashim.

Bayan anɗaura aure aka gayyaci malamai suka gabatar da wa’azi akan zaman takewar aure.

Kowace amarya an miƙata gidan mijinta.

Wani katafaren gida Alhaji Abdallah ya mallakama Jafar anan aka kai amarya Biba, sai dai muce masha Allah kwatanta haɗuwar gidan 6ata lokacine, domin ya haɗu haɗuwa mara misali.

Rabson ma Cikin gidajen Alhaji Abdallah ya mallaka mashi wani haɗaɗɗen gida nan aka mallakamashi suka tare shida amaryarshi.

Rabson bai manta da Bunsurulleba, wani wuri yaɗiba aka gyara ya kawo bunsurulle ya ɗaure ya ɗauko mai kula dashi, rayuwa tayi daɗi arziƙi ya bunƙasa Rabson yanzu yake Rabson guy.

Bunsurulle ya girma ya koma kamar bijimin sa.

In Salma naso ta tsokani Rabson saitace ita fa tana ƙwaɗayin naman Bunsurulle, nan zai tubure yace shifa shida bunsurulle mutu ka raba, nan zasu tuna da baya suci dariya abinsu.

Biba da Jafar rayuwa suke cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, ga kuɗi sun zauna masu sai da muce Alhamdulillah.

END

TAMMAT BILHAMDULILLAH.

<< Bakar Tafiya 16

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×