Lulawa akayi dasu a sararin samaniya, addu'ar da suke ta sanya aka yo ƙasa dasu ba shiri.
Wuri ne mai tsananin huduwa da manya_manya duwatsu, ga bishiyoyi masu wata firgitacciyar suffa ko ganye ɗaya babu jikin su, sai wasu irin dogayen saiwa ajikinsu.
watsosu akayi sanyin daya fara ratsa jikinsu ya sanya su buɗe idanu suka miƙe a firgi ce.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun, Mi mukeyi nan?, ina sauran abokan tafiyar mu."
Jafar ya faɗa yana mai kallon mandiya da Basma da suke rarraba idanu ido.
Hannu Basma ta ɗora akai ta fashe da kuka. . .