Skip to content
Part 4 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Lulawa akayi dasu a sararin samaniya, addu’ar da suke ta sanya aka yo ƙasa dasu ba shiri.

Wuri ne mai tsananin huduwa da manya_manya duwatsu, ga bishiyoyi masu wata firgitacciyar suffa ko ganye ɗaya babu jikin su, sai wasu irin dogayen saiwa ajikinsu.

watsosu akayi sanyin daya fara ratsa jikinsu ya sanya su buɗe idanu suka miƙe a firgi ce.

“Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, Mi mukeyi nan?, ina sauran abokan tafiyar mu.”

Jafar ya faɗa yana mai kallon mandiya da Basma da suke rarraba idanu ido.

Hannu Basma ta ɗora akai ta fashe da kuka.
“Wayyo Ɗana wayyo Mijina ashe kallon ƙarshe nayi maka bazamu sake haduwa ba ajali ke kira na.”

Ya isa, Jafar ya daka mata tsawa, “da kukan ki zamujin ko da halinda muke ciki, harkin manta da nasihar Ammar?, babban tashin hankalinmu ayanzu shine an raba mu da abokan tafitayarmu.”

Sai lokacin su Mandiya suka lura da basu tare da abokan tafiyarsu.

Nau sawa suka ƙarayi ciki jejin suna kwalama abokan tafiyarsu kira.

Tun suna kiran sunayen su da ƙarfi har muryoyinsu suka shaƙe amma ko alamunsu babu.

Tsayawa sukayi suna mai da numfaahi sakamakon tafiyar da suka sha.

“Ni fa ina ganin an rabamu da abokan tafiyarmu ne dan ayi galaba akanmu.”
Mandiya ta fada tana fuskantar Jafar.

“Nima zuciyata ta kawo mani wannan tunanin tuni, amma duk da haka mu dage da Addu’a, Allah shine kaɗai mai iya fitar damu daga cikin wannan halin.”

Tashi sukayi suka ci gaba da tafiya, sun ɗanyi nisa da wurin da suka baro sukaji takun tafiya a bayansu.

A hanzar ce suka juyo suna dunkulewa wuri ɗaya.

Sal…Sasa..Salma!.
Baku nan su, suka furta suna in ina.

Salma dake nesa dasu takowa ta farayi zuwa inda su Basma suke.

Mandiya murnan sun fara ganin abokan tafiyarsu ya sanyata rugawa ta maƙalƙale Salma.
“Muna ta naimanku ina kuka shige Salma?.”

Shirun da taji anyi mata ne ya sanyata dago fuskarta tana kallon Salma.

Ganin fuskar Salma da ta chanza ta koma irin suffar Horror, rabin fuskarta ya kowa abun tsoro duk yayi dameji wani farin ruwa mai haɗe da jini na zuba,idanunta ɗaya babba ɗaya ƙarami ga bakinta daya rabe biyu jini na ɗiga, faratan hannuwan ta sunyi zaƙo_zaƙo irin na Horror.

Razanananniyar ƙara ta fasa tana ƙoƙarin kwace kanta a hannun Salma.

Sai da ta makaro domin Salma ta rigada ta mata kyakykyawan ruƙo.

Dariya Salma taci gaba da 6a66akawa da ta sanya dajin amsa kuwwa.

Kunyi kuskuren shigowa dajin nan yau sai dai wasu baku ba.

Ɗaga Mandiya tayi da ta wullata sama, tayi nuni da hannunta wata iska ta riƙa wulwula mandiya tamkar yadda fanka ke gudu, tun Mandiya na ihun naiman taimako harta daina motsi.

Nuna ta tayi da hannu take wannan iskar ta tsaya nan Mandiya ta faɗo ƙasa tim!.

Darita ta kuma kecewa da ita, sai da tayi mai isarta sannan ta turbune fuska, “ku masu kunnen ƙashi, yau zakuga yadda zamu ƙare daku musamman kai, tana mai nuna Jafar da yatsa.”

“Na haɗa maku tarko amma na rasa ya akayi kuka tsallake shi, kunci ƴa’ƴan itatuwanda nina san da kunci to mutuwa zakuyi, kai kasa suka furta wata kalma wadda lokacin da zakuci wadda ita ta sanya kuka tsira da rayuwarku abinda kukaci bai kasheku ba, dan haka yanzu anan take zani raba gangar jikinku da numfashinku.”

“Baki isa kiyi mana abinda Allah bai rubuta zai faru damuba, kamar yadda Allah ya tseratar damu a wanchan lokacin nan ma muna sa ran zai tseratar damu.”

Kafin tayi wani yunƙuri cikin jarumta da dakewar zuciya Jafar ya ɗaga murya ya fara karanto Ayatul kursiyu, ita ma Basma ta ɗauka sukaci gaba dayi tare.

Ƙara Aljanin yake jikinshi na tsagewa ba shiri ya zama guguwa ya bi iska ya bace.

Tsagaita karatun sukayi, suka nufi inda Mandiya ke kwance shame_shame ba alamun tana motsi…

Tunda Aljanin ya wurgar dasu, buguwar dasu kayi ta sanya su sumewa.

Rabson ne ya fara farkawa, a hankali ya matsa kusa da Audu yana bubbuga jikinshi har yayi nasarar tayar dashi.

Hayaniyar da su Rabson keyi suna naiman sauran abokan tafiyarsu ita tayi nasarar tada su Biba suka tashi.

Sun duba ko ina amma babu abokan tafiyarsu.

Tashin hankalin da suka shiga bai misaltuwa musamman su Rabson da Salma.

Ga jikin Audu sai ƙara rikiɗewa yake yana komawa green da baƙi.

Duk cikin babu wanda ya lura da halinda Audu ke ciki tashin hankalin da suke ciki yasa sun manta da komi.

Ƙara nitsawa suke cikin dajin suna naiman su Jafar, amma ina sai da suka gaji liƙis basu ga koda sawayen ƙafarsu ba.

Zama sukayi suna mai da numfashin wahala.

“Mu yanzu haka zamu ƙare acikin wahala ga rashin tabbas na zamu fita daga jejin nan, Daddy dana bi maganarka da banzo wurin bikin nan ba, Hajara ban yafe makiba duk ke kika jawoni cikin wannan bala’in, gashi nan ke kinyi aurenki nikuma gani nan cikin masifa.”
Salma ta ƙarashe maganar ta rashe hawayen fuskarta.

Jugum_jugum suka yi kowa da abinda yake tunanin.

Yana yin wurin da suke zaune bakajin motsin komi sai sautin numfashinsu dake fita.

Motsin tafiya sukaji alamun ana nufo in da suke.

Miƙewa sukayi jikina kyarma Salma ta kama hannun Biba ta riƙe gam kamar wani zai rabasu.

Motsin takun naƙara kusanto su, suna ƙara shigema junansu.

Abinda idansu ya hasko masu ne ya sanyasu suman tsaye la66ansu na makyarkyata suka furta Garrrba!

Da ƙyar suka samu Mandiya ta farka daga sumewar da tayi.

Tana tashi ta riƙa ƙwala ihu tana gasu nan gasunan zasu kasheni.

Saida Jafar ya dage mata da addu’a sannan ta dawo dai_dai.

Shawara suka yanke bazasu ƙara zaunawa wuri ɗaya ba sai dai in dare yayi su yada zango su kwana su ci gaba da tafiya in gari ya waye.

Tafiya suke baji ba gani ga yunwar da ta addabesu da ƙishirwa.

Sunyi tafiya mai nisa suka iso wani wuri mai yalwar bishiyoyi masu suffar dodanni, wasu sun rankwafa kamar zasu faɗi ga jikinsu babu ganye ko ɗaya, wasu kuma Suffar mutumce tsaye ya buɗe baki yana dariya,wata bishiyar in kayi mata kallo ɗaya bazaka kuma kallonta ba.

Tunda suka shigo wurin suka sha jinin jikinsu, ba su Basma kaɗai ba hatta Jafar sai da zuciyarshi ta buga ganin yanayin wurin, sai dai shi bai fiddo tsoranshi ba a fili, sa6anin su Basma ita da Mandiya da suka maƙale juna suna bin bayan Jafar.

Busassun ganyayen dake baje wurin suka riƙabi ta saman su suna takawa domin su fita daga wannan sarƙakiya.

Takun da suke da sauri yasanya duk busashshen ganyen da suka taka yake bada wata ƙara rumutss!

A hankali wata iska ta fara kaɗawa ganyayen wurin suka fara tashi sama.

Lokaci ɗaya wata guguwa ta turniƙe wurin, dale su Jafar suka duƙa tare da rufe idanunsu.

A hankali iskar ta fara lafawa, buɗe idanunsu sukayi dan ganin mike faruwa.

Bishiyoyin wurin suka gani da wasu jajayen idanun tamkar garwashin wuta, sun buɗe bakunan su suna wata irin dariya mai kama da kukan jarirai.

Tsoron da ya kamasu bai hanasu miƙewa su falfala da azababben guduba.

Duk bishiyar da suka gitta ƙoƙari take ta kawo masu Chafka.

Gudu suke ba ƙaƙƙautawa, suna ƙoƙarin tsira da rayuwarsu.

Wata bishiya ce tayi nasarar sanya jijiyarta ta chafko ƙafar Basma dake gudu.

Ihu take janyo ta bishiyar keyi da ƙarfi jikinta na karcewa da ganyayyakin dake ƙasa.

Ganin halin da Basma ke ciki ya sanya su jafar juyowa domin kawo mata agaji.

Gudu suke suna binta bishiyar na ƙara janta.

Jafar ne yayi nasarar danƙo sauyar bishiyar.

Ƙoƙarin kufcewa sauyar keyi amma ta kasa saboda ruƙon da yayi mata.

Da ƙyar da addu’ar dake bakinshi yayi nasarar karya sauyar.

Bata damu da ciwokan dake jikinta ba tana samu ya kwanceta ta miƙe sukaci gaba da gudu…

Garba da kamanninshi suka gama rikiɗewa jikinshi yayi fari fat, idanunshi baƙin ciki ya bace sun koma farare tas, ga farautanshi sun ƙara tsawo, duk ya zama abun tsoro.

Wasu yawu Salma da Rabson suka haɗiye atare kutt!

Biba tunda tayi mashi kallo ɗaya tashiga karanto duk wata addu’a da ta zo mata.

Kafin su ankara Garba yayo kukan kura ya turmushe Rabson yana kokawar kai mashi cizo.

Wato wani bala’in inka ganshi tsoro barinka yake ka hau ƙoƙarin ceton rayuwarka.

Rabson ƙoƙarin yakice Garba yakeyi bakinshi na karanto addu’o’in da ya koya tunlokacin da Kaka ta sanyashi islamiyyah.

Inya fara karanto kul a’uzu kafin ya ida ya kamo Walfajir, ita ma ya saki, ya kamo
Wata,ranar Rabson har addu’ar shiga kewaye (Toilet) sai da yayi.

Allah ya dubi Rabson ya bashi sa’ar wurgar da Garba ya kwasa a guje su Salma suka take mashi baya.

Miƙewa Garba yayi yabi bayansu da azababben gudu suka ƙara nausawa cikin jejin…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakar Tafiya 3Bakar Tafiya 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×