Skip to content
Part 6 of 17 in the Series Bakar Tafiya by Amina Abubakar Yandoma

Ganin sun tserema Nura ya sanya Mandiya faɗuwa ƙasa tana maida numfashi.

Dafe ƙafarta dake yi mata raɗaɗi tayi.
“Wayyoh ni Mandiya na bani na lalace, yanzu shikenan nima Horror zani zama.”
Sauran maganar maƙalewa tayi saboda kukan da yaci ƙarfin ta.

Matsowa sukayi fuskokinsu da matuƙar tausayi suna mata sannu.

Ƙafar suka kallah, abin mamaki jinin dake zuba ya tsaya, wurin yayi wani irin green da baƙi.

Su kansu sun san nan da lokaci ƙanƙani itama zata zama Horror.

Allah sarki Jafar duk halin tsananin da suke ciki zuciyarshi tana wurin Biba kullum cikin tunaninta yake zuciyarshi tana hasko mashi hoton fuskar Biba.

Basma ta taimaka ma Mandiya sukaci gaba da tafiya har duhu ya farayi.

Ƙarƙashin wata itaciyar Kuka suka yada zango, daji Jafar ya shiga ya samo masu ƴa’ƴan itanuwa sukaci.

Fuskokin su duk cikin tashin hankali suke, kowa da irin tunanin dake cikin zuciyarshi.

Motsin da sukajine ya sanya su dawowa daga duniyar tunanin da suke.

Tamkar walƙiya haka sukaga wani farin abu ya gilma ta gabansu.

Basma da Mandiya rirriƙe juna sukayi ido ya raina fata.

Miƙewa Jafar yayi a hankali cikin sanda ya dudduba ko ina amma bai ga komi ba.

Dawowa yayi ya zauna zociyarshi cike da tunane_tunane.

“Jafar ka duba sosai kuwa?, ni fa kamar fatalwa nagani wallahi baka gani ta gifta tanan.”
Basma ta ƙarashe maganar tana ƙara dudduba wurin.

“Tabbas nima ita na gani, amma komiye mu dage da addu’a babu abinda yafi ƙarfin Allah.”

A ɗarare suke jininsu kan akaifa.

Dare yayi dare bakajin motsin komi sai kuka tsuntsaye da wani irin gurnani da suka rasa gane namiye.

Jafar gani yayi zaman zugum ɗin yayi yawa nan ya buƙaci jin miya fiddo da su daga gida.

Basma ta fara basu labarin abinda ya fito da ita, Jafar ya girgiza sosai dajin labarin yayi mamakin yadda ta bijirema umarnin miji ta taho biki, wai kuma bikin ma na ƙawa.

Nan itama Mandiya ta fara bada labarinta kamar haka;

“Kamar yadda kujaji da farko nidai sunana Mandiya, garinmu ɗaya daku wato gefen Kai kazo, na taso babu uwa babu uba, natsinci kaina a gidan karuwai hannun wata mata mai suna Uwar Daba, tun da na taso banida kunya ko kaɗan ga taka mutane da bi ta saman duk wanda ya so kawo mani raini, tun ina da shekara 20 Uwar Daba ta ɗorani a hanyar karuwanci, in da ni dana tashi sai karuwanci na yayi zarra saboda rashin kunyata nayi suna duk inda kashiga indai gidan karuwai ne to an san da zamana, abinda yayi sanadiyyar fitowata wannan tafiyar Magajiyar karuwai tai ta kwaɗaita mani inzo garin kai kazo zani tara dukiya mai tarinn yawa, domin chan karuwanci yafi tsada, kunji abinda ya fiddoni, har yanzu ina dana sanin fitowata da kasancewata karuwa ina nadamar rayuwar da na tsinci kaina ciki.”

Kukan dayaci ƙarfinta ya sanyata kasa ida maganar.

Sun tausaya mata halinda ta tsinci kanta.

Nan Jafar ya ƙara jan hankalinta Allah gafurun rahimun ne, ta tuba har cikin zuciyarta Allah yana karbar tuban bawanshi madamar baizo gargara ba.

Nan shima Jafar Ya basu labarin abinda ya fito dashi gida, sun jajantama juna suna addu’ar Allah ya fitar dasu a wannan jejin.

Tsit! Wurin yayi kowa da abinda yake tunani, Jafar yana gefensu ya takure wuri ɗaya yana addu’a a zuciyarshi.

Dariya aka kece da ita wadda ta tilasta masu toshe kunnuwansu da duka hannayensu biyu.

“Hhh! Wane ganganci da ƙarar kwana yayi Sanadin kawoku cikin jejin nan, kamar yadda muka rasa rayuwarmu muka koma fatalwa haka kuma zaku rasa taku rayuwar bazaku taba fita a jejin nan ba.”

Kawunansu suka ɗaga suna ƙarema halittar kallo, sanye take da farar riga da tayi face_face da jini, ilahirin jikin ta farine sol idanuwanta babu ɗugon baƙi ko kaɗan ga dogayen hannuwa masu ɗauke da farata dogaye masu tsananin tsini, doguwace sosai tsaye take saman iska kamar tsuntsu doguwar rigar dake jikinta dogowace har ƙasa shiyasa ko ƙafafunta baka iya hangowa.

Jikin su Mandiya da Basma tuni ya hau mazari.

Jafar ji yayi kamar an sanya sarƙoƙi an ɗaure bakinshi addu’ar ma ya kasafurta koda kalma ɗaya.

Wannan damar Fatalwar ta samu ta nunasu da yatsa wani farin hayaƙi yafito ya zama guguwa yayi sama dasu Jafar.

Tamkar yadda fanka ke wulwulawa haka aka riƙa wulwula su Mandiya tun suna ihu har ƙarfinsu ya ƙare sukayi tsit iskar ta watsar da su wani bangare daga cikin jejin batare da sun san mike faruwa ba.

*****
Kamar yunwa taccen zaki haka Audu yayo kan Salma da tayi mutuwar tsaye.

Tariga ta bada sadaƙar yau kwananta ya ƙare jira kawai take ya kasheta ta huta.

Kamar daga sama sukaji ƙarar wani abu kamar an buga bindiga.

Mace da namiji suka gani tsaye gabansu da wani abu kamar sanda a hannunsu.

Dubansu suka kai ga audu dake kwance ƙasa yanata bullayi da alamu ƙoƙarin tashi yake.

Mace tace dasu Biba mubar wurin nan kafin ya tashi domin gaf yake da miƙewa.

Su duka suka bar wurin suka yi wata siririyar hanya da guda.

Gudu suke ba ƙaƙƙautawa tamkar bazasu tsaya ba.

Ganin sunzo wurin wata gadar icce suka ja suka tsaya suna maida numfashi.

Rabson da sai yanzu hankalinshi ya dawo jikinshi ganin bakin fuska ya sanyashi yin tsalle ya koma gefe.
“Innahu min sulaimanu…., bayin Allah mutane ko aljannu, daga ina kuke mijya kawoku jejin nan?, ko dai kuma Horror ɗinne sukazo mana da taku salon yaudarar?”

Namijin daya gama ƙuluwa ya watsama Rabson kallon zaka gane kurenka.

Macen tayi ƙarfin halin fara magana.

“Tsautsayi ne da rabon wahala ya fiddomu daga gida har muka tsinci kanmu cikin Wannan halin, ni sunana Kulu amma ana kirana Kulu ganin ƙwam, sai abokin tafiyata sunanshi Nasir, sai kuma abokan tafiyar mu su biyu da suka bace mana Jamcy da Tukur muna kiranshi Tk, mun kasance masu son kallon abubuwar mamaki ne, Rannan malamin mu na mana lecture yake sanar damu wannan jajin da haɗarindake tattare dashi, da kuma abubuwan mamakin dake cikinshi tundaga lokacin muka yanke shawarar guduwa daga gidajenmu domin muzo ganin abubuwan Al ajabi, mu hudu haka muka shigo dajin nan bala in da muka shiga ya sanya muka rabu da abokan tafiyarmu batareda mun saniba.

Halin da suke ciki bai hana Rabson fashewa da dariya jin waɗan da suka fisu gantalewa, Nas a fusace ya taso ganin Rabson ya raina masu wayo, cikin hanzari kulu ta tareshi tana bashi haƙuri.

Rabson kallon Salma yayi ganin yadda bakinta yayi Suntum ya haye ga goshinta daya yi ranƙwalele.

Sake fashewa yayi da dariya yana riƙe ciki, yana nuna Salma da hannu yanaci gaba da dariya.

Tamkar zata kai mashi bugu haka Salma tayo kan Rabson, Biba tayi saurin riƙeta tana bata haƙuri, ashar kawai take dannoma Rabson amma bai daina dariyar ba.

“Haba Rabi’u! Miye haka Kana ta taƙular mutane bakaga halin da muke cikiba amma har kuke ƙoƙarin fada?.”

Bai daina dariyarba yaci gaba da magana”Habibalo kiyi haƙuri wallahi inna kalli bakin Salma yadda yayi tsawo kamar shantu bani iya danne dariyata, masoyiyita Salma kiyi haƙuri kinji nifa tunda muka shigo jejin nan nike jin ƙaunarki na ratsa jinin jikina.”
Ya ƙarashe maganar yana dariya.

Salma kamar ana zugata haka ta riƙa zagin Rabson tana fadar tafi ƙarfin tayi soyayyah dashi, da Ƙyar Biba ta shawo kan Salma tayi shiru.

Gurnanin da sukaji bayansu ya sanya bashiri suka fara bi ta saman gadar katakon ba shiri.

Doguwar gadace wadda aka ƙerata da katako gefe da gefe kuma iggiyace wadda zaka riƙe hangu da dama, kasanta ramine mai tsananin zurfi baka iya hango ƙarshenshi.

Tafiya suke da sauri Rabson na taka wani katako ya balle yayi ƙasa , lokaci ɗaya gadar ta fara karairayewa ta yin ƙasa, hankulansu atashe wasu suka fara ihu, wasu suna addu’o’i.

Rabson atake ya fara bada wasiyyah yana;
“Salma masoyiyata inkin samu komawa gida kice ma Kaka na barmata ɗan bunsuru na duniya da lahira ta yafe mani , wayyoh kaka lokacin mutuwata yayi.”

Igiyoyin gefen gadar suka rirriƙe suna gudu gadar na ƙara karairayewa………

<< Bakar Tafiya 5Bakar Tafiya 7 >>

1 thought on “Bakar Tafiya 6”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.