Daddy ya fice harabar asibitin sai kai da komo yake yi, Munawwa ta ja kujera ta zauna tana kallonta tare da nazarin maganganunta. A take zuciyarta ta ba ta honey'n nata ne ya yaudare ta, don daman ita zuciyarta tas ha ba ta ba son tsakani da ALLAH yake yi mata ba. Tun da duk tsawon had'uwarsu ya kasa zuwa gidansu ya nuna kan shi ga Iyayensu, a take ta ji wani irin haushin shi ya kamata. Cike da burin safiya ta waye taje gida.
Cikin dare ma Munara ta farka tana ta kiran sunan shi, sai magiya. . .