Skip to content
Part 10 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Daddy ya fice harabar asibitin sai kai da komo yake yi, Munawwa ta ja kujera ta zauna tana kallonta tare da nazarin maganganunta. A take zuciyarta ta ba ta honey’n nata ne ya yaudare ta, don daman ita zuciyarta tas ha ba ta ba son tsakani da ALLAH yake yi mata ba. Tun da duk tsawon had’uwarsu ya kasa zuwa gidansu ya nuna kan shi ga Iyayensu, a take ta ji wani irin haushin shi ya kamata. Cike da burin safiya ta waye taje gida.

Cikin dare ma Munara ta farka tana ta kiran sunan shi, sai magiya take yi masa a kan don ALLAH kada ya guje ta, haushi ya k’ara turnuke Munawwa tamkar ta rufe ta da duka.

Safiya tana wayewa ta ce da Daddy za ta je gida tayi wanka, sannan ta karb’o masu abun break fast. Daddy ya ba ta key d’in motar shi ta ja ta yi gida, yanayin da ta iske Mummy ciki ya sa ta jin k’afafuwanta sanyi. Saboda ramar da ta yi a dare ɗaya idanuwanta sun yi zuru zuru, a kan kukan da ta sha tare da fargabar da take ciki na rashin sanin halin da Munara take.

Da sauri Munawwa taje wurinta tana ba ta hak’uri hawaye yaa sauka fuskarta, bayan ta yi mata bayanin ta ji sauk’i anjima ma za a sallamo su. Ta dinga kwantar mata da hankali cikin dad’ad’an kalamai, sai a lokacin hankalin Mummy ya kwanta ta yi mata addu’ar k’arin samun sauk’i.

Sannan Munawwa ta nufi d’akinsu ta d’auko wayar Munara da ta jefar a k’asan carpet d’insu. ALLAH yasa ba ta yi komai ba ta kunna da wayar saboda ta san security d’in da take sakawa. Sannan ta shiga Gallery ta goge duk hotunan Basarake da ke cikin wayar gabadaya, har wanda suka yi da Munara duk ta goge kuma ta d’auki lambar shi ta saka a wayarta, bayan ta goge ta cikin wayar Munara tareda saka shi a black list.

Sannan ta zauna ta kira shi amma wayar ta yi ringing har ta k’are ba a d’aga ba. K’arshe ma ta ji wayar a switch up, Uban tsaki ta buga cike da jin haushin shi ta ce,

“Bak’in mayaudari, sai Allah ya saka mata a kanka, na so ya d’auka da na shuka masa rashin mutuncin da ban tab’a yi wa kowa irin ba ba a duniya, bak’in mugun banza ɗan iskan kawai.”

Ta k’are maganar cikin fushi, ita ma ta goge lambarsa a wayarta, sannan ta fad’a toilet tana wanka tana k’ara tsine mashi masa a ranta.

*****
Basarake kuwa yana shirin zuwa gidansu Munara yavga kiran Munawwa ya shigo wayarsa, kasancewar ya yi saving d’in lambobinta duka a layukansa. shi ya sa yak’i d’aukar wayar, don ya san ba ta san shi da lambar ba, a take zuciyar shi ta ba shi cewa a kan case d’insu da Munara ne ta kira shi. Yana kallo har wayar ta ringing har ta katse bai d’aga ba, saboda har lokacin ran shi a b’ace yake, saboda tsinuwar da ya ji Munara ta yi wa Ummin shi. Shi ya sa zuciyarsa ta k’ara k’arfafa masa gwiwa a kan ya cusa wa Munawwa soyayyar shi ta k’arfi, saboda ya ɗauki niyyar d’aukar fansar a kan Munara. Ko don ta rage hayak’in da ke fita saman kanta, wanda a d’an zaman da ya yi da su ya fahimci Daddynsu ne ya yi silar b’ata mata tarbiyya. Saboda yadda a fili yake fifita son ta a kan na kowa, haka ma shi ya ba ta dama a kan ta yi duk abin da take so ba kyara babu hantara.

*****
Munawwa tana k’are wankan a gurguje ta shirya ta kwashi wayoyinsu ta zuba a jaka, sannan ta fito ta karb’i abin karin nasu da Mummy ta kammala tun asuba. Ta zuba a cikin food flak’s ta ajiye, saboda rashin baccin da idanuwanta suka kasa yi a kan ciwon Munarar.

Bayan ta karb’a ta yi sallama da Mummy ta fito, tana sauri ta nufi motar Daddy da ta zo da ita, ta bud’a seat ɗin baya ta saka kayan. Ɗ’agowar da za ta yi ta yi ido biyu da Basarake, wanda ke k’ok’arin zuwa wurinta. Domin shigowar shi kenan a gidan shima yana gaisawa da Malam Isah ya hango ta, da fara’ar shi ya nufo ta yayin da ita kuma tata fuskar babu yabo babu fallasa. Duk da ta ji gabanta ya fad’i lokacin da idanuwanta suka hango shi, musamman da ya ce,

“Ranki ya dad’e barka da safiya, yau lecturer d’in ba ya wasa kenan? Tun da na ga wannan fita ta sassafe.”

Ya k’are maganar da murmushin shi na yak’e, ita ma ta yi d’an murmushin ta ce,
“Ba makaranta zan je ba ai, Munara ce ba lafiya tana asibiti an kwantar da ita tun jiya.”

Basarake yaji k’irjin shi ya buga dam! dam! Cike da jimami kamar gaske ya ce,

“Subhanallah ALLAH ya ba ta lafiya”

Munawwa ta ce “Amin.”

Sannan ta shiga motar ta fara ba ta wuta, da sauri BASARAKE ya duk’o cikin ladabi ya ce,
“Ranki ya dad’e zan iya zuwa mu je na duba ta?.”

Munawwa a cikin ko in kula ta ce da shi,

“Babu damuwa shigo mu je.”

Ya bud’e sit d’in gaba ya zauna sannan ya kira sunanta cikin wata siririyar murya, ba shiri ta kai kallonta gare shi idanuwansu suna had’uwa ta ji k’irjinta ya buga. Da sauri ta janye nata ba tare da ta ce da shi k’anzil ba, shima ya yi kamar bai gano yanayin da ta shiga ba ya ce da ita,

“Idan babu damuwa ki ba ni na yi driving d’in, na ga kamar ke ma ba kya da lafiyar.”

Munawwa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ribas ta doshi bakin gate, wanda tuni Malam Isah ya wangale mata shi. Tana zuwa daidai wurin shi ta tsaya sannan ta d’an rusuna ta ce

“Mun tafi Baba, sai mun dawo.”

Malam Isah bakin shi a washe ya ce,

“ALLAH ya tsare hanya ‘yar albarka, muna gaidata da jiki. ALLAH ya ba ta lafiya.”

Munawwa tace “Amiñ.”

Basarake ma ya d’aga masa hannu yana cewa,
“Sai mun dawo Baba.”

Malam Isah ya kalle shi cike da mamakin gamin zak’ewarsa ta yi yawa, sannan ya ce
“To Ali sauka lafiya.”

Bayan ta fito ne ta hau kan titin, sannan ya k’ara cewa da ita,

“Me ke damunta?”

Cikin sanyin muryar shi ya yi maganar ba tare da ta kalle shi ba ta ce,

“D’an zazzab’i ne ya buge ta.”

Basarake ya kai kallon shi gare ta, ya so ya k’ara yi mata tambaya dangane da ciyon Munarar, amman yanayinta da ya gani ya sa ya fake da fad’in,

“To ke fa? Don yanayinki ya nuna kamar ba ki da lafiyar ke ma”

Munawwa ta d’an yi murmushin yak’e sannan ta ce,
“Lafiyata k’alauz zuciyata ce kawai babu dad’i.”

Ta k’are maganar cikin muryar Kuka, wanda duk k’ok’arinta na son ta danne damuwar da ke ranta amman ta kasa. Sai da hawaye ya gangaro kan fuskarta ta yi saurin saka hannu ta share, hankalinshi a tashe ya zaro idanuwa cike da jin zafin hawayen da ya ga tana zubarwa ya ce,

“Plss ranki ya dad’e, don ALLAH ki yi parking ki ba ni tuk’in nan plsss kin ji?”

Ta gangara gefen titin ta tsaya, sannan ta fito ya zauna mazaunin direba ta zagaya ta zauna gaba. A take ya tayar da motar cike da k’warewa ya harba ta kan titi sannan ya ce,

“Duk da bansan abunda ke damunki ba, amman na san abin da duk ya saka jarumar mace irinki kuka; to tabbas abin ba kad’an ba ne. Sai dai ki sani komai ya yi tsanani yana tareda da sauk’i, ki yi hak’uri sannan ki rok’i ALLAH ya yaye miki abin da ke damunki. Kuma ya sanya alkhairi a cikin lamurranki, daman ita rayuwa haka ta gada yau fari gobe bak’i. Amma idan aka yi hak’uri sai ki ga komai ya zo ya wuce kamar ma ba a yi ba, saboda haka kisa a ranki, ALLAH yana ji kuma yana gani. Sannan kuma ma ji rok’on bayinsa ne idan suka mayar da lamurransu gare shi, da sannu zai yaye miki damuwarki matuk’ar kika jingina al’murranki duka gare shi.”

Munawwa ta share hawayenta da har lokacin bai daina zuba ba, sannan ta ce,

“Na gode sosai.”

Dukansu suka yi shiru kowa da abin da yake sak’a wa a ranshi har suka isa Asibitin. Da kan shi ya ri’ko mata kayan abincin suka nufi d’akin da aka kwantar da Munara, wanda tun kafin su k’arasa d’akin suka jiyo sautin kukanta. Jiki babu kuzari Munawwa ta tura k’ofar d’akin ta shiga, Basarake ma kan shi tsaye ya bi bayanta da sallamar shi. Tozalin da ya yi da Daddy ya sa gaban shi ya fad’i zuciyarshi ta shiga bugawa da sauri da sauri, a haka dai ya daure ya je ya ajiye kayan abincin sannan ya zo ya fara gayar da Daddy cikin ladabi. Kafin ya kai duban shi ga Munara da take jikin Daddyn tana rera masa kuka tamkar wata k’aramar yarinya. Daddy sai aikin rarrashinta yake yi, ko zama Munawwa ba ta yi ba ya ce da ita,

“Ina wayar Baby? Kin zo da ita?”

Munawwa ta ce, “Eh, ga ta a jakata.”

Ta ciro wayar ta mik’a masa, ya tayar da Munara da ke kwance jikin shi ya ce,

“Karb’i wayar kira shi yanzu mu ji, don na san wasa ce yake yi miki kawai don ya gwada ki, ke kuma kin zo kin tayar da hankalinki a banza.”

Munara jikinta har rawa yake yi ta fara laluben lambar a, amman har ta kai k’arshen list d’in sunayen contacts bata ga sunan da ta saka masa ba waton HONEY, hankalinta a tashe ta shiga messages nan ma wayam babu saƙo ko ɗaya. Daga nata wanda take tura masa har nasa wanda yake aiko mata. Jikinta yana rawa ta shiga whatsapp ta k’are bincikenta kat ba ta ga chatt d’in da suka yi ba, sannan ta koma face book a nan ma wayam babu komai, babu shiri ta dafe kanta tareda k’walla wata k’ara tana cewa,

“Daddy na shiga uku komai na HAIDAR d’in ma ya goge a wayata. Wallahi Daddy mutuwa zan yi idan ba a nemo mini shi ba! Wayyo Daddy ka taimake ni rayuwata za ta salwanta idan na rasa shi .”

Ta diro daga kan gadon ta nufi k’ofar fita ɗakin da gudu za ta fice, Daddy da Munawwa suka damk’o ta cikin sauri. Sai fisge fisge take yi a kan sai an bar ta taje nemo masoyinta da kanta, a k’arshe ma da ta ga sun hana ta a nan sai ta some musu. Daddy hankalin shi a tashe yake kiran sunanta, a firgice Munawwa ta yi waje sai ga ta ta dawo tare da wani Dr, bayan an kwantar da ita ya ce da su su fita waje Munawwa da Basarake suka fito. Amma Daddy kafewa ya yi ya ce sam ba inda zai je, dole likitan ya fara aikinsa cikin minti biyar numfashinta ya dawo, aka k’ara yi mata allurar bacci domin zuciyarta ta sami relief. Sannan likitan ya yi warning a kan cewa kada a koma d’aga mata hankali, saboda zuciyarta tana cikin mugun yanayin da idan aka bari ta sake somewa a karo na uku, to a wannan lokacin l zata buga gaba d’aya.

Hankalin Daddy yayi k’ololuwar tashi ya fara zirya a cikin d’akin, hannun shi duka biyu nad’e a bayan shi yana nazarin wace irin musiba ce wanann ta ruguzo masu da rana tsaka.

‘Wai ko dai HAIDAR d’in ba mutum ba ne?’

Babu shiri ya kai zaune don shi wannan so da Munara take yi wa yaron ya ba shi tsoro sosai. Domin idan har mutum ne shi to ta ya za a yi komai nasa ya goge cikin wayarta. A ran shi ya ce,

‘Ko dai Munawwara ce ta yi wannan aika-aikar?’

zumbur ya mik’e tsaye ya fito waje inda Munawwa da Basarake suke zaune kan wasu kujerun da ke facing da k’ofar d’akin. Yanayin da ta ji Daddy ya kira sunanta daga zuwan shi ya sa gabanta fad’uwa babu shiri. Cikin tsawa ya ce da ita,

“Wa ya goge abubuwan da ya shafi HAIDAR a wayar Baby?”

Cikin rawar murya ta ce,

“Nice Daddy na zaci idan na goge za ta yi saurin manta shi ko da za ta samu natsuwa a rayuwar…”
karaffffff ta ji saukar wani bahagon mari akan fuskarta ba tare da ta kai k’arshen zancenta ba. Da sauri ta dafe gefen da tasha marin wani sabon hawayen yana sauka kan fuskarta. Zuciyarta cike da bak’in cikin abin, saboda yafda hankalin mutane da yawa ya dawo kansu. Amma shi ko a jikin shi sai ma d’aga muryar da ya yi ya ce,

“Kin goge kam, amman ki sani kin goga muna bala’i, ke wace irin dak’ik’iya ce da kika rasa gano aibin da hakan zai janyo daga baya? Ba ni key d’ina tashi ki bar asibitin nan, tun da na gano ke sakarya ce kar na sake ganin k’afarki a nan. Bak’ar munafuka sum-sum da ke amman kin iya mugunta, b’ace mini daga nan da shegun idonki tun kafin na kakkarya ki.”

Basarake k sai hak’uri yake ba shi, amman ko kallo bai ishe shi ba ya koma d’akin fuuuu ya barsu a nan. Tare da cin alwashin duk inda HAIDAR yake sai ya nemo mata shi a fad’in duniya.

Munawwa ta bi da Daddy da kallo hawaye yana kwaranya a kan fuskarta, saboda bak’in cikin abin da ya yi mata a gaban mutane. A ranta ta furta cewa,

‘Me ya sa Daddy a kullum kake fifita son Munara a kaina ne? Daga taimako sai abu ya juye mini? To ai ba ni na kar zomon ba.’

Ta saka hannu ta share hawayen sannan ta mik’e tsaye jiki a sanyaye ta nufi d’akin, Basarake ya bi ta da kallo a cikin tausayawa har ta tura k’ofar ta shige.

Idanuwan Daddy a kan fuskarta, fuskarsa a murtuk’e har ta k’araso wurin shi ta durk’usa, hawaye yana zuba a fuskarta tata ce,
“Don ALLAH ka yi hak’uri, Wallahi ban yi da wata manufa ba, na yi ne kawai domin ta manta da shi Daddy, saboda na dad’e da gano ba son gaskiya yake yi mata ba, sabo…… “

“Get out…. “

Ya katse ta ta hanyar daka mata wata k’atuwar tsawa, wacee garin k’ok’arin tashi tsaye sai da ta fad’i. Sannan ta mik’e tsaye da saurinta jikinta sai rawa yake yi saboda tsananin tsoron fushin Daddy. Domin tsawar da ya yi ta sa Munara farkawar a firgice tare da kiran sunan Daddyn.
A zabure Munawwa da Daddy suka yi kanta, shi kanshi Basarake da ke waje sai da ya shigo. Saboda tsawar da ya ji Daddy ya yi, yana shigowa ya yi arba da Munara da ke ta kuka jikin Daddy, duk da kirjin shi da ke ta bugawa amman bai hana shi k’arasawa wurin ba. Saboda ko kad’an bai ji tausayin ta ba, domin…

<< Bakon Yanayi 9Bakon Yanayi 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×