Skip to content
Part 9 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Basarake ya yi saurin katse wayar sannan ya danna Recording d’in maganar da ta yi. Da hanzari ya rintse idon shi tare da dafe kan shi, idanuwan shi suka yi masa jawur a cikin k’ank’anin lokaci, saboda tsananin b’acin rai.

*****

Mummy da ke k’ok’arin shigowa d’akin, wannan maganar ta Munara ta shiga kunnuwanta, a zafafe Munara ta ji saukar mari akan fuskarta. Zumbur ta juya, idanuwanta suka had’u da na Mummy, zarar ido ta dinga yi saboda yanayin da ta ga fuskar Mummyn yasa ta sha jinin jikinta. Domin zuciyarta ta tabbatar mata da ta ji lafuzzanta.

Cikin tsananin fushi har muryarta tana shak’ewa saboda tsananin b’acin rai ta ce,
“Wannan tarbiyya ta zagin manya wallahi ba a gidan nan kika same ta ba! Don ni har yanzu ina kaffa-kaffa da wanda na san ya haife ni don na samu tubarrakin tsufa. Kuma za ki ga hukuncin da zan d’auka a kanki matuk’ar gigi ya sake jan ki na koma jin irin wad’anan maganganun a cikin bakinki. Wallahi ki bi duniya a sannu Munara, saboda shi d’an hakin da ka raina watarana shi ne yake tsokale maka idanu.. ke kuma zo mu je ki bani maburkin miyata da kika ɓoye, na yi ta nema bangan shi ba.”

Tana k’are maganar ta fita cikin fushin da ya kasa b’oyuwa a kan fuskarta, Munawwa ta bi Munara da da wani kallon takaici saboda jin zafin zagin Ummin Basarake da ta yi, cikin d’aga Murya ta ce,

“Kin yi na farko kin yi na k’arshe, muddin kika sake zagar masa uwa a gabana sai na ba ki mamaki wallahi.”

Ta zo za ta fita d’akin Munara ta yi saurin shak’o wuyan rigarta ta baya, cike da masifa ta ce,

“Idan an sake me za ki iya yi?”

Cikin fushi Munawwara ta ce

“Dukan bala’i zan yi miki a cikin gidan nan wallahi.”

Munara tayi saurin sakin rigarta tana wata irin dariya tana nuna ta da hannu, saboda tsananin dariyar da Munawwa ta ba ta babu shiri. Can ta d’ago da niyyar ta k’ara yin zagin domin ta me za ta yi wayam ta ga babu Munawwa a ɗakin ta ficewarta. A ranta ta ce,

“Wai duka, abin dariya, ai wallahi da hannunki ba zai sake dukan kowa ba a duniya, don sai na kakkarya su ta yadda ba za su sake yi miki amfani ba.”

Ta koma kan gadon ta kwanta, tare da shafo gefen da Mummy ta mare ta ta ce,

“Dad’in abin dai ni na fara marin ‘yar son taki kafin ki mare Ni.”

Ta ƙare maganar tare da murgud’a baki ta janyo wayarta tana danna wa honey’nta kira, amma har ta tsinke bai d’auka ba. Ta yi kira ya fi a kirga kuma tana ringing bai d’auka ba, har sai da ta gaji ta koma tura masa saƙonnin a nan d’in ma babu alamun an duba, balle ta ga reply. Da ta k’ara gwada kiran carab ya d’auka, sai dai yanayin da ta ji muryar shi ya sa ta ji gabanta ya ƙire ya fad’i babu shiri, a cikin rawar murya ta ce masa,

“Honey lafiya.?”

Muryarsa ɗauke da tsananin b’acin rai ya ce,

“Baby yanzu Abbuna ya kira ni yana sanar da ni ya nema min mata, don haka ki yi hak’uri ki nemi wani mijin ki yi auren ki, amma ni kam ba zan aure ki ba. Sannan ya zama dole na rabu da ke ko ina so ko ba na so, domin ina so na saka hannu biyu na rungumi matar da ALLAH ya zab’a mini, wacce ita ce ta dace da ni ba ke ba. Kuma daga yau na yanke duk wata alak’a da ke tsakaninmu ko a waya kada ki yi tunanin za ki sake ji na; balle ki gan ni a a zahiri…”

Diffff! Ya kashe wayar, bakinta yana rawa saboda tsananin tashin hankali ta kurma wata uwar k’ara. Birgima ta fara yi a kan gadon tamkar taɓin hankali same ta na wuccin gadi, sai ga Mummy da Daddy da yake shigowa gidan a lokacinz Munawwa tana bayansu. Kamar an jefo su haka suka fad’o d’akin zuciyoyinsu sai bugawa suke yi da sauri da sauri, saboda tashin hankalin da suka shiga ganin yanayin da take ciki yasa suka rufo kanta kowa yana rige rigen kamo ta domin a ji me ya faru.

Daddy yana rik’ota ta yi cikin shi kamar wata kura ta gartsa masa cizo, duk da zafin ya ratsa shi amman bai bi ta kai ba, sai k’ok’arin ƙara janyo ta jikinsa yake yi. Mummy tana ganin inda ta ciji Daddyn ta fasa masa fata har da jini. Ta yi saurin d’auke ta da wani shahararren mari har sai da ta k’ara gigicewa, ta tashi sama ta fad’o kan gadon tare da k’walla wata k’arar sannan ta some musu. Nan take kumfa ya dinga fita a bakinta alamun mutuwa kusa, da k’arfi Daddy ya yi magana,

“Baby don Allah ki tashi kada ki mutu ki barni!”

Sai hawaye shaaaaa akan fuskarsa, a haka ya kinkimo ta jikin shi zai fita Mummy ta biyo bayan shi da gudu ko mayafi babu, saboda tsananin rud’ewar da ta yi. A harzuƙe ya yi saurin kallon ta ya ce,

“Taku d’aya idan kin k’ara da niyyar biyo mu a bakin aurenki, kuma ki sani Wallahi muddin ‘yata ta mutu sai na yi shari’a da ke.”

Yana k’are fad’ar maganar ya fice da sauri ya saka ta mota, Munawwa ta yi saurin shiga kafin ta rufe k’ofar ya fisgi motar da k’arfi ya fice gifan. Isah maigadi ya bi su da ALLAH ya kiyaye, cike da mamakin yanayin da ya ga Munara a cikin motar, a ran shi ya ce,

“Ita kuma uwar tsiwar me ya same ta ne?.”

A rud’e yake tuk’in wanda ALLAH ne kawai ya kai shi cikim asibitin, yanayinta da aka gani ya sa aka shiga emergency room da ita a gaggauce. Likitoci suka rufu kanta domin k’ok’arin su na son ceto rayuwarta da ke barazanar rabuwa da gangar jikinta.

Daddy sai safa da Marwa yake yi yayin da Munawwa take wani irin kuka cikin tashin hankali, domin ita ma ta ji tsoron ganin wannan yanayin da ‘yar uwarta take ciki. Saboda iya sanin ta da wayonsu ba ta tab’a shiga makamancin wannan halin ba, duk da artabun da suke sha da Mummy kullum safiya.

Har magriba ta yi amman ba a fito da Munara ba, dak’yar Daddy ya je ya yi sallah a masallacin da ke asibitin ya dawo. Ganin Munawwa a zaune, saman gyalen da ta yafo wanda alama ta nuna ita ma sallahr ta gama yi. Tashi tsaye ta yi ta kakkab’e gyalen sannan ta yafa, ta cire hijabin da ta ara ta bai wa mai shi ta zauna suka ci gaba da zaman jiran tsammani.
Mintuna aka fito da ita a kan gadon asibitin zuwa wani d’aki na musamman, wanda ita kad’ai ce a cikin shi. Munawwa da Daddy suka bi bayan nurses d’in da hanzari, Daddy sai tambayar su yake yi cikin rud’u yana faɗin,

“Ya jikin nata da sauk’i ko? Allah ya sa ta farfad’o? Numfashinta ya daidaita ko?”

Wata daga cikinsu ta ce,

“Ka yi hak’uri za ta samu sauk’i da ta farfad’o in sha ALLAH, amman ka je Dr yana son ganin ka.”

Daddy sai da ya je jikin gadon ya ri’ko hannunta ya ce,

“Sannu baby.”

Duk da ya san ba amsa masa za ta yi ba don ba ta san inda kanta yake ba har lokacin, sannan ya fice yana ta waigen ta ya nufi d’akin likitan. Wanda daman can sun saba da juna, bayan sun gaisa sama-sama likitan ya fara yi masa bayanin abin da bincikensu ya bayar dallah dallah. Kai-tsaye ya sanar da shi akwai abin da ta ji ko ta gani, wanda ya d’aga mata hankali sosai kuma ya kasa d’aukar kwakwalwarta kanta, ya yi sanadin da ta rasa hankalinta na wuccin gadi, sannan shi ne ya janyo mata gushewar numfashinta ta some cikin ƙanƙanin lokaci.

Daddy hankalinsa ya k’ara tashi, cikin rawar baki ya ce,

“Yanzu dai komi normal ko? Don ba na son na ji wata mummunar magana daga bakinka wacce ta k’unshi wata matsala ga Baby.”

Likitan yayi murmushi ya ce,

“Lafiya k’alau za ta farka sai dai…… “

Daddy ya yi saurin katse shi da fad’in,

“Sai dai me?”

Likitan ya ce,

“Rashin k’arfin jikinta, shi ma a hankali za ta warware. Don haka za mu rik’e ta tsawon kwana biyu a nan muna ba ta kulawa.”

Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce,

“Alhmdllh na gode wa Allah.”

Likitan yana dariya ya ce,

“Yau an tab’o file d’in ‘yar gaban goshi.”

Daddy yana dariyar ya ce,

“Ciyon Baby ai ciyona ne.”

Tare suka fito suka shiga d’akin da aka kwantar da Munara, ko da suka je har Nurse’s d’in sun d’ora mata gorar k’arin ruwa sun fice. Munawwa ce kawai zaune a kan kujerar roba ta yi tagumi tana kallonta, tare da shiga nazarin son sanin abin da ya janyowa ta shiga mugun hali.

Shigowar su ne ya sa ta daina tunanin da take yi, Daddy yana kallon ta ya ji ta ba shi tausayi duk da ya fi tausayin Munara sau dubu a kanta. Ta tashi ta ba shi kujerar da nufin ya zauna cikin ladabi, yayi saurin cewa da ita,

“Zo mu je na kai ki gida yanzu, ni kuma na dawo saboda sai ta kwana biyu a nan, kafin lokacin a samu jikin nata ya warware.”

Munawwa ta ce,

“Ni zan kwana da ita Daddy, kai ka je gidan ka kwanta, da safe sai ka dawo.”

Ya maka mata harara yana cewa,

“Baby a asibiti zan iya kwana, ai ke kin san ba zan iya rintsawa ba. Amma bari na je na d’auko maku abin da za ku buk’ata na dawo. Ai jinya ta same ni nida kwana gida sai an sallame ta kuma.”

Ba Munawwa ba, har likitan sai da suka yi wa Daddy dariya, saboda yanayin da ya yi maganar kamar wani zautacce. Ya fice likitan ya bi bayan shi, Munawwa ta mayar da kallon ta a kan fuskar Munara da lokaci d’aya ta rame. A ranta ta yi mata addu’ar ALLAH ya ba ta lafiya, kuma ya sauya mata wasu halayemta mara kyau, ko don a samu zaman lafiya tsakanin Iyayensu. Saboda taji tsoron gargad’iin da Daddy ya yi wa Mummy kafin su fito gidan.

*****

Ko da Daddy ya koma gida, ko kallon Mummy da ke falon zaune bai yi ba, yana hawa sama ya ce da ita,

“Ki had’o mini kayan Baby kala biyu, da abincin da zan kai musu yanzu.”

Mummy ta kalle shi jikinta sanyi k’alau ta tashi ta yi abin da ya saka ta, bayan ta had’o kayan ne ta ajiye a falon tana jiran ya sauko. Minti biyu a tsakani ya fito da alama ma wanka ya yi saboda kayan da ya shiga da su ba da su ya fito ba, yana zuwa jikinta yana rawa ta mik’a masa kayan sannan ta ce da shi,

“Ya jikin nata?”

Daddy ya karb’e kayan ya fara tafiya yana cewa,

“Wannan ba abin da ya shafe ki ba ne”

Ya fice cikin sauri, ta bishi da kallo tamkar ta kurma kuwwa saboda ta matsu ta san a wane hali ‘yarta take ciki.

Daddy yana fitowa da kayan a hannu Malam Isah ya k’araso da sauri ya rik’a masa kayan, bayan ya saka masa a bayan motar ne ya ce dashi,

“Maigida lafiya dai ko?”

Daddy ya fad’a motarshi ya tayar sannan ya ce da shi,

“Baby ce babu lafiya, ka rufe gidan a can zan kwana.”

Malam Isah ya b’ata fuska alamun jimami sannan ya ce,
“ALLAH ya ba ta lafiya, Ubangiji ya tashi kafad’unta.”

Daddy ya ji dad’in addu’ar shi ya amsa masa faranfaram sannan ya ja motarsa ya fice gidan, yana tafe yana jinjina abin da ya yi sanadin jefa Babynsa cikin wannan mawuyacin halin.

Har ya je asibitin bai tantance ba, koda ya shiga yadda ya bar ta haka ya dawo ya same ta. DA sauri Munawwara ta karb’i kayan ta ajiye sannan ta fara duba kayan abincin tana ganin hadda abincin Daddyn, ta samo plate ta zuba masa sannan ta kai masa gabansa, sai da ya kai kallon shi ga abincin sannan ya b’ata fuska yana cewa,

“Ba na ci”

Munawwa ta yi magana cikin sanyin Muryarta cike da ladabi ta ce
“Ka dauri ka ci wani abin ko da kad’an ne Daddy, tun da ma bayan tafiyarka ta farko sannan ta koma.”

Da sauri Daddy ya ce,

“Da gaske?”

Ta ce,

“Eh, sai da ma ta tambaye ka.”

Yana jin haka ya ji wani dad’i ya ziyarce shi yana murmushin jin dad’i ya ce,

“Alhmdllh ba ni abincin yanzu kam hankalina ya d’an kwanta.”

Ta yi saurin mik’a masa abincin zuciyarta cike da jin dad’in dubarar da ta yi masa, don idan ba haka ba, ta san shawo kansa ta sauki abu ne mai matuk’ar wahala. Ita ma ta zuba abincin ta ci, lokacin da ta k’are ta je ta wanko hannunta a toilet d’in da ke d’akin. Shi ma kad’an ya ci ya ture plate ɗin ya fice ɗakin, ko da Munawwa ta fito ba ta tarar da shi ba sai Munara da ta hango tana motsa k’afarta tare da yamutsa fuska alamar tana so ta falka. A razane ta bud’e idanuwanta sannan ta zabura tare da k’wallah k’ara tana fad’in sunan honey’nta na ainahi waton HAIDAR.

Munawwa ta yi saurin zuwa ta rik’e ta saboda k’arin ruwan da take k’ok’arin fisgewa, shi ma Daddy aguje ya shigo d’akin ya yi kanta yana kiran sunanta. Munara ta saka hannu ta cisge k’arin ruwan tana fad’in,

“Wayyo honeyna kar ka guje ni! Wallahi ina son ka kai ma ka sani, idan ma wasa kake to ka daina mini irin wannan zan iya rasa rayuwata a kan hakan. HAIDAR ka zo ka ce mini wasa kake ba za ka iya rabuwa da ni ba.”

Daddy ya rungumota jikin shi a rud’e ya dimga ba ta hak’uri, Munawwa ta fita da sauri ta je ta kira Nurse’s suka zo suka danna mata allurar bacci, a cikin mayen baccin da ya sake d’ibarta tace,

Daddy ka ce ya dawo gare ni wallahi ni ina so…. n…. Sh….i “

Ta k’are maganar a cikin slow saboda baccin da yaci karfinta, Daddy ya gyara mata kwanciya sannan aka sake mak’ala mata ruwan ta yi luf. Sai a lokacin hankalinsu ya kwanta dukansu, Daddy ya kai kallon shi ga Munawwa ya ce,

“Wane ne shi?”

Ta ce “Wallahi ni ma Daddy ban san shi ba, ban ma san me ke faruwa ba muna kitchen ni da Mummy, muka ji k’ararta.”

Daddy ya sauke numfashi da k’arfi yana cewa,

“Ina wayarta?”

Munawwa tace, “Tana gida.”

Daddy ya fice harabar asibitin sai kai da komo yake yi, Munawwa ta ja kujera ta zauna tana kallonta tare da nazarin maganganunta. A take zuciyarta ta ba ta honey’n nata ne ya yaudare ta, don daman ita zuciyarta ta sha ba ta ba…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 8Bakon Yanayi 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×