A falo ta fito suna karyawa ita da Mummy sai ga Yusuf ya yi sallama ya shigo, bayan sun gaisa ko zama bai yi ba ya nemi a ba shi abincin 'yan asibitin ya kai masu, saboda yana sauri ya wuce School. Ita ma kanta Munawwa saurin da take yi kenan saboda makarantar take so ta wuce, don kwananta biyu ba ta je ba gabshi jiya wata k'awarta ta sanar da ita akwai test ɗin da za su yi da ƙarfe tara na safe 9:00am.
Ta je ta d'auko wa Yusuf kayan, kasancewar ba zai iya rik. . .