Skip to content
Part 14 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

A falo ta fito suna karyawa ita da Mummy sai ga Yusuf ya yi sallama ya shigo, bayan sun gaisa ko zama bai yi ba ya nemi a ba shi abincin ‘yan asibitin ya kai masu, saboda yana sauri ya wuce School. Ita ma kanta Munawwa saurin da take yi kenan saboda makarantar take so ta wuce, don kwananta biyu ba ta je ba gabshi jiya wata k’awarta ta sanar da ita akwai test ɗin da za su yi da ƙarfe tara na safe 9:00am.

Ta je ta d’auko wa Yusuf kayan, kasancewar ba zai iya rik’a su duka a hannunsa ba, hakan ya sa ta rik’o sauran suka fito zuwa inda ya ajiye motar shi. Yana gaba tana bayan shi cikin taku a hankali har ta kai wurin da ya ajiye motar, ta duk’a ta saka kayan a cikin boot d’in motar sannan ta d’ago tana yi masa ALLAH ya kiyaye.

Basarake kuwa da zuwan shi gidan kenan yana zaune a kan d’an teburin Baba Isah ya ga fitowarta. Amma tun da ya k’yalla ido ya hango ta nan take wani b’acin rai ya ziyarce shi babu shiri. Saboda yadda ya ga rigar da ke jikinta ta kama ta sosai, kasancewar ta roba ce, gabaɗaya k’irar jikinta ya fito rad’am a cikin rigar. Bombom d’inta sun fito b’ul b’ul da su tare da tona asirin faffad’an kunkurunta, har ta saka kayan a mota idon shi a kanta ranss a jagule. Saboda haushin YUSUF da ya cika masa ciki, da kishin ya ganta a yadda take, uwa Uba bayan ya shiga motar ya tayar ta zo gefen shi suna magana. Wanda ita ko a jikinta saboda ganin Yusuf tamkar aboki suka d’auke shi, domin tare suka taso tun suna yara a tarihi ma da ta ji an ce shekara d’aya ce ya ba su ita da Munara. shi yasa ko d’ar ba ta ji ba don ta fito a yadda take, sai gashi shi uban gayya ya ji kishin hakan sosai. Juyowar da za ta yi ta shiga cikin gidan; ta yi tozali da shi, babu shiri taji k’irjinta ya buga dam!!!

Har ta so ta wuce shi saboda saurin da take yi, sai kuma ta nufi wurin shi domin ta yi masa ina kwana. Shi ma tun da ya hango ta nufo shi ya taso don baya so Baba isah ya ji abin da za su fad’a. Ai kuwa ta tsaya k’yam ganin ya nufo ta idanuwanta a k’asa har ya k’araso inda take tsaye, sannan ta d’aga kai ta kalle shi tare da yi masa ina kwana. Ba tare da ta jira ya amsa ba ta juya ta fara tafiya, madadin ta ji amsar shi sai ji ta yi yana cewa,

“A taimake ni a sauya wannan riga plss.” Bsbu shiri ta waigo ido cikin ido suka kalli juna, saboda muryarshi da ta ji sautin a had’e, hakan ya tabbatar mata da ran shi a b’ace yake. bya tare da ta ce k’anzil ba ta yi saurin shigewa gidan, zuciyarta sai bugawa take yi dam-dam! Saboda abin da ta hango cikin k’wayar idon shi, tana tafe tana tambayar kanta.

‘Me hakan yake nufi? Ma’ana dai kishina yake yi.’

Haka kawai ta tsinci kanta da jin wani farin ciki marar misaltuwa, ranta fess ta je ta sauya rigar zuwa wata doguwar rigar atamfa. Wacce aka yi wa d’inkin A. sharp saboda ita tana da d’an fad’i ba ta kama ta ba. Sannan ta sako farin hijab wanda ake kira 3 in 1 d’an k’aramin hijab d’in ya fito da ‘yar zagayayyar fuskarta a cikinsa ma sha ALLAH.
Ta d’auko jakar makarantarta ta zuba littafan Munara a ciki, sannan ta d’auko key d’in motarsu ta fito tana yi wa Mummy sallama, Mummy ta yi mata addu’ar ALLAH ya tsare tared a nemar mata sa’a a kan text d’in da ta fad’a mata za su yi. Ta fio jakarta rataye a kafad’arta yayin da wasu littafan suke rungume a jikinta, yana ganin ta fito yanayin shigarta ta faranta masa rai sosai, shi yasa ya yi saurin zuwa wurinta yana murmushi a hankali ya ce da ita,

“Ga direbanki ya zo Hajiya.”

Ba shiri tayi ‘yar dariya sannan ta mik’a masa key d’in, wurin karb’a ya d’an ri’ko hannunta da sauri ta saki key d’in ya fad’i k’asa. Jikinta yana rawa ta zagaya ta bud’e motar ta shiga ta zauna, tar eda jingina bayanta jikin seat d’in ta rintse idanuwanta, saboda yadda take jin zuciyarta tana bugawa da sauri da sauri. Ya kalle ta dariya fal ran shi amma ya mazge ya bud’e motar ya shiga, tare da ba ta wuta a lokaci d’aya. Sannan ya yi horn malam Isah da daman yana kan bud’e gate d’in, k’arar horn d’in motar ya k’ara saka shi wangale musu shi gaba d’aya.

Hankalin Basarake a kwance ya fito da motar rumfar, sannan ya yi ribas ya doso kan motar zuwa bakin gate d’in, sai da ya zo daidai inda Malam Isah yake tsaye sannan ya d’an rank’wafo ya ce masa,

“Barka da safiya Baba.”

Baban yana d’an murmushi ya amsa, “Barka da safiya Ali, ‘yata barkar ki da wayewar gari.”

Tana murmushi ta ce,

“Barka dai Baba ina kwana?”

Ya ce, “lafiya lau adawo lafiya, ALLAH ya yi muku albarka.”

Suka amsa da Amin

Sannan suka fice ya mayar da gate ya rufe, a ran shi yana ta jinjina kirkin yaran. Kuma a take ya yanke wa ran shi Allah ya ba shi ita, saboda irin dacen ma’aurata masu kirkin da za’ayi matuk’ar suka auri junansu. Sai dai inda gizo yake sak’ar shi ne; rashin hatimin nasara da shi Alin ya rasa, ba ya da komai. Kuma abu ne mai matuk’ar wahala ta aure shi saboda tazarar da ke tsakaninsu da shi.

Basarake tuk’iin shi kawai yake yi bai ce da ita k’anzil ba, saboda har lokacin kishin yusuf ya gan ta da rigar nan bai daina mintsinin zuciyar shi ba. Ita ko shirun da ta ga ya yi ne ya sa ta ji duk ba dad’i, haka kawai ta ji kamar ba ta kyauta masa ba. shi yasa ta kalle shi a hankali ta ce,

“Ka yi hak’uri don ALLAH.”

Ba tare da ya kalleta ba ya ce,

“Hak’uri for what?”

Ta kame bakinta ta yi gum har suka kusa kai makarantar ba wanda ya koma magana a tsakaninsu, sai da ya sha round d’in da zai kai su makarantar sannan ya ce,

“Gobe ina so na je gida na gano su Ummi, saboda rikicin Kakale ya tashi a kan sai na zo na gan su sannan na dawo.”

Munawwa ta sauke ajiyar zuciya mai sauti sannan ta ce,

“ALLAH ya kai mu, amma kwana nawa za ka yi idan kaje?.”

Ya d’an sosa kan shi sannan ya ce,

“Ba zan wuce sati d’aya ba.”

Rass ta ji k’irjinta ya buga, saboda zancen ya yi kayar mata da gaba har cikin ranta, domin ta zaci ya ce kwana d’aya ko biyu sai ga shi ta ji yana zancen sati d’aya. Amma ta dake kamar ba komai a ranta ta ce,

“Me zai hana idan ka je ka yi kwana uku.”

Ya yi d’an murmushi sannan ya lank’wasa kan shi ya ce,

“Idan dai su aka ba ni ai shi kenan.”

K’are maganar shi ya yi daidai da shigarsu cikin gate d’in makarantar, Munawwa ta yi shiru ba ta yi magana ba saboda nauyin shi sosai take ji. Bayan ya yi parking ta fito ta kalle shi da kyau ta ce,

“Na gode sosai”

Har ta fara tafiya ta waigo ta k’ara da cewa,

“Ba ni key d’in idan an tashi zan dawo da kaina.”

Ya yi wani guntun murmushi sannan ya ce,

“Idan kin gama abin da kike yi ki kira ni zan dawo na d’auke ki.”

Kamar walk’iya ya bar wurin tana tsaye tana kallon motar har ya fice gate d’in makarantar. Sannan ta juya zuwa k’aton hall d’in da za su yi text d’in, amma hankalinta da tunaninta kacokam yana wurin shi. Saboda son shi ya riga da ya gama gauraye kafatanin zuciyarta, tsakanin jiya da yau ya k’ara samun wani matsayin da ita kanta ba za ta iya fassara shi ba, domin ya ci gagarumar nasarar sark’o zuciyarta da soyayyar shi mai zafi.

*****

Munara babyn Daddy kuwa, ta saki jikinta sosai ta rage wa kanta damuwa domin ita ma ta matsu a sallame ta ta huta. shi yasa ta yi ta damun Daddy a kan ita ta ji sauk’i don ALLAH su koma gida hakanan, aikuwa ya tambayi likitan ya k’ara duba masa lafiyarta za su iya tafiya gida a hakan. Likitan ya duba ta sosai ya tabbatarwa da Daddy an ysami ci gaba sosai, sai dai akwai wasu ruwa da za a saka mata zuwa marece idan ya k’are zaa sallameta. Da sharaɗin idan ta je gida ta tsare shan magungunanta.

Daddy ya ji dad’i sosai ya k’ara kwantar mata da hankali da lallami da ban baki aka mak’ala mata ruwan. Ta yi kwance lamo tana tunanin rayuwarsu ta baya lokacin da suna tsaka da soyayya tare da Haidar d’inta. Har zuwa had’uwar da suka yi da maganganun da suka tattauna a ranar da shi, a ranta ta ce

‘WALLAHAHI in dai har da gaske kake yi; ni ko sai na zame maka k’arfen k’afa mai wuyar ja, kuma k’adangaren bakin tulu. Sai na zame maka ciyon idon da ba ya da magani, sai na hana ka rawar gaban hantsi daga kai har matar da zaka aura.’

Sai ga hawaye sha suna kwaranya a kan fuskarta, da sauri Daddy ya ce,

“plss Baby ki yi hak’uri da ruwan ya k’are za mu je gida kin ji?.”

Don shi a tsammanin shi ruwan ne take yi wa kuka, saboda ba ta so aka sake d’ura mata wani ba.

*****

K’arfe uku dam! Munawwa ta kira shi yana ganin kiran ya garzayo ya d’auke ta, har sun fara tafiya ta ce da shi zai kai ta wata super market. Babu musu ya kai ta kai tsaye saboda ainahin mai super market d’in ma abokin Alhajinshi ne, akwai sanayya sosai a tsakaninsu. Yana parking ta fito ta shige cikin super market d’in ya so ya bi ta sai ya ga kawai ya jira ta fito, ai kuwa tana shiga ta fara siyayyar da ta kai ta. Waton turmi uku da hijab guda biyu, tare da sabulun wanka da na wanki masu kyau da kwalbar turare guda biyu. Aka yi mata total gaba d’aya kud’inta suka kama 18k, kasancewar Daddynsu yana saka masu kudi sosai ga account d’insu, saboda ‘yan k’ananan matsalolin makaranta idan sun taso.

Shi yasa ko d’ar ba ta ji ba ta mik’a ATM d’inta suka cire kud’insu sannan ta fito, tun daga nesa ya hango ta tana tafiya cikin natsuwa. Ya kur’e manejin kallon shi a kanta saboda yadda komai nata yake burge shi, tun kafin ta k’araso ya taysr da motar tana shiga ya hau kan titi suka nufi gida. Bayan ya yi parking da motar ta yi saurin fitowa, yana k’ok’arin fitar shi ma ta d’an rank’wafo idonta a kansa ta ce,

“Ga sak’o nan ka ajiye a hannunka, gobe idan ka je gida ka kai wa Ummi da Kakale, kace ina gaida su sosai.”

Tana k’are maganar ta rufo k’ofar kafin ya tantance ta shige cikin gidan, mamaki kwance a kan fuskar shi ya bi k’ofar shiga gidan da kallo mai cike da tsananin mamakinta.

A cikin mamakin ya dawo da kallon shi ga ledodi biyu da ke ajiye seat d’in gaba, a hanakali ya duk’a tare da janyo ledar ya fara dubawa jikin shi a mace ya d’auko ledar ya rufo motar. Key a hannun shi don ya mance shaf bai ba ta ba, ita ma kanta saboda saurin da take yi ta shiga gida ba ta tsaya ta karb’a ba.

Cikin rashin kuzari ya nufi bencin malam Isah ya zauna, tare da duk’e kan shi zuciyar shi ta shiga zurfin tunani. sayboda abin da Munawwa ta yi masa a yau ya k’ara tabbatar masa da cewa ita ta daban ce a cikin jerin mata. Haka zalika halinta ya yi wa Munara fintinkau ta ko’ina, don samun ire irenta masu kyakkyawar zuciya a wannan marra abu ne mawuyaci.

Yana nan zaune sai ga Malam Isah ya zo da buta rik’e a hannun shi, idonsa a kan shi har ya ajiye butar ya zauna ba tare da ya sani ba. Saboda ya nutsa sosai da tunanin nemo wa kan shi mafita wurin zab’in macen da ta dace da rayuwar duk wani mutumin kirki.

Baba Isah ya zauna idon shi akan ledar da ke ajiye gaban Basarake, ya kira sunan shi har sau biyu sai a na uku ya d’ago tare da bud’e idanuwanshi da suka yi jawur. Malam isah ya ce,

“Lafiyarka kuwa yau Ali? Na ga tun d’azu kake shiru ko ‘yar hirar da muke yi yau ba ka saki jiki mun yi da kai ba.”

Basarake ya sauke k’atuwar ajiyar zuciya sannan ya jawo ledar ya fara nunawa Malam Isah kayan da ke ciki, a cikin d’aurewar kai malam Isah yake bin kayan da kallo, har sai da ya k’are nuna masa sannan yace “Eh nagani ka tashi ka kai masu kayansu idan har aikenka akayi.”

Basarake ya yi tagumi da hannun shi biyu ya ce,

“‘Yarka ce ta ba da a kai wa su Ummi, saboda gobe in sha ALLAH zan je k’auyenmu na dubo su. Dalilin rikicin tsufa da kakalena take yi a kan dole sai na dawo ta gan ni ko ita ta zo.”

Malam isah yana jin haka ya fad’ad’a fuskar shi da murmushi yana ‘yar dariya ya ce,

“Lalle ka garzaya ka je ka gano Uwargida tun da sarautar ta motsa. Ubangiji ALLAH ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya. Eh lalle wannan ‘ya tawa ta yi k’ok’ari sosai, ALLAH ya ba ta lada sannan ya cika muku burinku na alkhairi.”

Basarake yana murmushin jin dad’i ya ce,

“Amin Baba, na gode sosai da addu’arka.”

Baba yana wasar baki ya ce,

‘Addu’a kam ai kullum ba mu fashin yi wa ‘ya’yanmu ita, fatar mu kawai ALLAH ya karb’a man.”

Basarake ya yi murmushi fuskar shi cike da jin dad’i, wani gefen zuciyar shi kuma cike fam da tausayin Baba Isah. Saboda ganin yadda ya yi tsaye kai da fata zuciya d’aya yana aikin shi. Domin ya tallafi iyalin shi da ‘yan uwan shi, wanɗanda nauyinsu ya rataya a kanshi. Dalilin hakan ya zab’i ya sai da ran shi domin ya faranta musu.

Ya ci alwashin duk burin shi ya cika zai tallafa masa, ko don ya daina wannan sana’ar da yake yi, don shi ma ya je gida ya zauna cikin iyalin shi ya huta.

*****
Munawwa kuwa a gajiye tib’is ta fad’a gidan, Mummy ma gaida ta kawai ta yi ta shige d’akinsu, tare da jefar da jaka ta fad’a toilet ta d’auki tsawon minti goma kafin ta fito. Ta fito towel d’aure a jikinta saboda wankan da ta yi. Sallah ta fara yi sannan…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 13Bakon Yanayi 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×