Skip to content
Part 16 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Tana saukowa ta fita aguje ta d’auki key d’in motarsu da ke ajiye saman teburin malam Isah ta bud’e gate da kanta ta je da sauri ta fad’a mota. Ta jawo ta da k’arfi ta fice gidan sai jin k’arar tashin motarta aka yi, Mummy ta k’ara sautin Kukanta, saboda ta kasa jure abin da yake damun zuciyarta, don tun fitar Munawwa zuwa wurin Daddy ta fara kuka saboda tsananin tausayin rayuwarsu dukansu, tun daga kan Daddyn har Munara da ita kanta Mummyn tare da Munawwarar, wanda ta fi alak’anta komai akan Daddy don a ganinta shine silar duk wani rikicin da ke faruwa a gidan.
Munawwa ko unguwa unguwa tayi ta bi inda tasan nan ne unguwannin marasa shi, saboda tsammaninta a can ne kadai za ta iya cin karo da sh. Tanyi ta yawo har ta gaji dole don kanta ta dawo gida, saboda tuno ta baro wayarta a gida balle ta kira shi ta ji unguwar da yake. Amma har lokacin ba ta daina kuka ba saboda takaicin abin da aka yi masa.

Bayan ta dawo gidan ta nufi d’akinsu ta janyo wayarta da ta bari, ta fito falo don ba ta son wata magana ta had’a ta da Munara. Ta dinga buga wayar shi amma ta k’i shiga, ana cewa line busy ta kira har sau biyu sai a na uku ta samu ta shiga, yana d’auka ko sallama babta yi masa ba ta ce,
“A wace unguwa kake yanzu zan zo na same ka.”

Basarake da Malam Isah ya gama yi masa bayanin duk abin da ya faru, cikin damuwa ya ce da ita,
“Ki jira ni zan zo k’ofar gidanku yanzu, amman fa idan kin san da matsala mu hak’ura kawai mu yi zancen a waya.”

Munawwa ta yi shiru na d’an lokaci sannan ta ce,

“Ka zo kawai babu wani abu.”

Don ta k’uduri ko da Daddy zai kashe ta sai ta je ta ba shi hak’uri, sannan ta sanar da shi ya dawo bakin aikin shi idan ya dawo ganin gida. A ganin ta kafin lokacin da zai dawo za ta shawo kan lamarin, sannan suka yi sallama ta tashi ta je d’akin mummy ta yi ramakon sallahr magriba da ba ta yi ba, sannan tabyi isha tare da addu’o’inta. Tana k’arewa ta ɗora kanta saman gadon Mummy hawaye yana zuba a gefen idonta, ta tsura wa wayarta ido tana tsumayen kiran shi kamar yadda suka yi da shi, a kan da ya zo k’ofar gidan zai kira ta.

Mintuna biyar a tsakani wayar ta fara haske alamun kiran shi ya shigo, saboda silent d’in da ta saka wayar ba ta ƙara. A zabure ta mik’e jikinta yana rawa za ta fito d’akin ta ci karo da Mummy da ke kokarin shigowa, mummy ta yi hanzarin faɗin,

“Ina zaki je kike sauri haka?”

A cikin fad’uwar gaba ta ce,

“Mummy Aliyu ne ya zo yana k’ofar gida, shi ne zan je na ba shi hak’uri.”

Mummy ta yi shiru tana kallonta tare da karantar yanayinta, fahimtar idan ta hana ta zuwa za ta k’ara wa y’arta damuwa, idan kuma ta bar ta ba ta san abin da zai je ya dawo ba, tsakaninta da Daddy, Munawwa ta marairaice ta ce,

“Plss Mummy wallahi ba zan wuce minti biyu biyar ba.”

Ta k’are maganar tare da zubowar wani hawaye a kan fuskarta, Mummy ta yi k’arfin halin cewa,

“Kin san halin Daddynku fa.”

Munawwa ta fara tafiya da sauri tana cewa,

“Just five minutes Mummy.”

Ta wuce da sauri Mummy ta bita da kallo har ta k’ule wa ganinta, sannan ta zauna tana nazarin wannan rikici da yake shirin tunkaro su, saboda jikinta ya ba ta tabbas sai an yi d’an k’aramin yak’i kafin daddy ya amince da wannan had’in, duk da ko ita abin bai kwanta mata a rai ba, don dai kawai yadda ta ga ita Munawwar ta damu da shi ne.

Ko da ta zo fita Malam Isah yana cikin d’akin shi, har lokacin yana jimamin abin da Daddy ya yi masa. Don ya k’uduri niyyar barin aikin ko don tsira da mutuncinshi, duk da Aliyu ya yi ta bashi hak’uri a kan ya zauna ya k’ara ba su lokaci kafin ya bar aikin. Saboda shi Basaraken bai so Baba ya ajiye aikin a lokacin don tafiyar da zai yi yana son ya zamo idanuwan shi a kan duk abin da za a yi baya nan. Ya fi son har sai maganarsu da Munawwa ta kankama sannan ya ba shi abin da zai tallabi kan shi.

Sai da ta d’an lek’o sannan ta hango shi a cen nesa da gidan, da taimakon hasken nefar da ya haskake k’ofar gidan, sannan ta fito ta tsaya shima ya tako a hankali zuwa daidai inda take sannan ya tsaya idonshi akanta yace

“ALLAH ya sa lafiya ranki ya dad’e wannan nema cikin dare?. “

Munawaa ta sauke ajiyar zuciya ta ce

“Hak’uri na zo ba ka a kan abin da Daddy ya yi maka don ALLAH ka yi hak’uri, kuma idan ka je ganin gidan ka dawo aikinka yana jiran ka.”

Basarake ya fara girgizar kai alamun ba zai yiyu ba, a cikin sarkewar murya ta yi saurin fad’in

“For my sake.”

Ya yi murmushin shi na yake, sannan ya magantu da cewa,
“Zan jure komai ma in dai a kanki ne, amma kin ga Daddy da kan shi ya sallame ni, idan na dawo with out parmission zai ga kamar na raina shi ne. Ki yi hak’uri in sha ALLAH zan dinga lek’owa muna gaisawa a duk lokacin da na samu lokaci.”

Hawaye mai zafi ya gangaro mata a cikin shauk’in son shi da ya taso mata, wanda ta kasa controlling d’in kanta cikin dusashiyar muryar da ta sha kuka ta ce,
“Idan na rasa ka ban san ina zan saka rayuwata ba, ka yi hak’uri ka dawo aikinka. Wallahi zan shiga damuwa sosai idan na bud’e ido ban gan ka cikin gidan nan ba.”

Basarake wani dad’i ya lullube shi, cikin wata muryar da ba ko yaushe yake yi mata magana da ita ya ce,

“Munawy base on yanda ki ke treating d’ina, sai na ga kamar na fi kowa sa’a. Amma idan na tuna har yanzu ban tab’a jin kalmar ina sonka Aliyu ta fito daga bakinki ba, sai na yi ta ganin kamar ban kai matsayin ba. Saboda haka ba zan juri zama a hakan ba gasky, tun da har yanzu ina under probability. Don haka ki yi hak’uri kawai idan na dawo zan dinga samun lokaci ina zuwa muna gaisawa bye sai watarana.”

Yana k’are maganar ya juya zai fara tafiya jikinta ya d’auki rawa, kirjinta ya fara dakan lugude yana bugawa fat! fat! fat! A hankali ta furta masa,

“Aliyu I love u morethan anything in dis world Aliyu, I don’t have any word to describe how i feel when I see u, i love u so much my one and only .”

Basarake ya yi wani juyi kamar wani zautacce a zabure ya isa wurinta tare da ri’ko hannunta kamar ya rungumeta saboda farinciki, bakinsa yana rawa ya ce,

“Da gaske?”

Ta d’aga masa kai kamar wata k’adangaruwa, a hankali ya rungumota jikin shi tare da sauke ajiyar zuciya ya ce,

“Am so happy Munawy, much luv u my beautiful baby. I luv u so so much my angel.”

Ita ma ba ta san lokacin da ta ce,

“Me too my HAIDAR.”

Munara da ke bayansu tsaye zuciyarta cike da tsanarsu tana jin munawwa ta ambaci HAIDAR ta yi saurin fitowa ta tsaya kansu k’erere tana yi masu wani kallo.
Tana k’are masu kallo tun daga sama har k’asa zuciyarta cike fam da tsanarsu a cikin tsawa tace “Waton daman cen kun saba tanbad’ewarku ashe?”

Munawwa da Aliyu kam sai k’ara nanukar juna suke yi a cikin wani shauk’in so suna furta wa juna kalamai masu k’ara tabbatar da son da suke yi wa junansu suke. Sun manta da kowa da komai sai kansu kawai, ba su ma san tana wurin ba, har sai da ta saka hannu ta fara k’ok’arin raba su tana zazzaga ruwan masifa. Sannan hankalinsu ya dawo jikinsu da sauri Basarake ya sake Munawwa, yayin da ita ma ta shiga taitayinta babu shiri ta gayyato natsuwa tare da jin kunyar abin da suka yi. Jikinta sai rawa yake yi saboda ganin Munara a wurin.
Shi ko yana ganin Munara a kansu k’irjin shi ya buga saboda yana jin tsoron ta sake k’ulla masa wani sharri wurin Daddy. Don ba ya son duk wani cikas da zai kawo masa ziyara wurin neman auren heart beat d’in shi Munawy. A hankali ya juyo ya ce da Munawwa,

“Ki shiga gida na gode sosai zan tafi sai mun yi waya i love u bye!”

Yana tafiya yana d’aga mata hannu ita ma hawaye suna kwaranya a kan fuskarta tana d’aga masa hannu. Saboda bakinta ya kasa furta wata kalma tsananin kukan da yake taso mata tana dannewa.

Tana tsaye har ya kule wa ganinta, yayin da Munara ta kafe nata idanuwan a kan Munawwara. Saboda mamakin da ya cika mata ciki wanda ya sa ta kasa cewa da Basarake k’anzil har ya bar wurin., Sai bayan ya tafi ta ji haushin da ba ta yagalgala shi ba domin ta tara musu mutane.
Munawwa ta saka gefen hijabin dake jikinta ta goge ruwan hawayen da ya b’ata mata fuska, sannan ta juya da nufin ta shiga gida Munara ta jawo hijabin nata ta baya. Babu shiri Munawwa ta tsaya cak har Munara ta zagayo ta gabanta, har lokacin idanunta ba su daina mamakin abin da ta gani ba. Ta kwashe da wata arniyar dariya ta ce,
“Gaske kike damuwa a kan an kore shi, ashe ke kin san me kuke yi shi ya sa kike damuwa. Yanzu saboda ALLAH don kawai kina son ki zubar mana da mutuncin gidanmu kike soyayya da wancan bak’in bakauye, matsiyaci, d’an talakawa?WALLAHI mu dai kin cuce mu, yanzu a ce gida irin wannan ki rasa wa za ki yi soyayya da shi sai irin wancan bak’in kuturun? Cabɗijam! Wallahi dai an ji kunya idan an san ta.”

Munawwara ta maka mata wata shahararriyar harara da jajayen idanuwanta, cikin fushi ta fisge hijabinta daga rik’on da ta yi mata tare da nunata da d’an yatsa bakinta yana rawa ta ce,

“Ki kiyayi fad’in miyagun kalamai ga Aliyunah! Idan ba haka ba wallahi yanzu zan had’a miki jini da majina. Kuma rayuwata ce ba taki ba, ni shi na gani, kuma shi nike so. Haka zalika shi na mallaka wa zuciyata, kuma shi ne mijina uban ‘ya’yan da zan haifa a duniya. Halittar shi da komai na shi ba damuwata ba ne, ni shi d’in nike so ba wani abu na shi da zai mallaka ba. Kud’i kyau ko dukiya ba su isa su kai darajar son da nike yi masa ba, don haka ki rubuta ki ajiye ALIYU HAIDAR BASARAKE mijin Munawwara ne wanda duk bai so sai dai bak’in ciki ya kashe shi. No going, backward ever, ki bud’e kunnuwanki da kyau ki ji kuturun nan da kike fad’a i luv him. Duk da bak’ar fuskar shi da talaucin duka na ji na gani ina son abuna a haka. Kuma zan aure shi a yadda yake saboda wannan ba damuwar ki ba ce tawa ce ni da HAIDAR d’ina.”

Tana k’are fad’ar abin da ke zuciyarta ta ture Munara ta shigo gidan, Mummy da ke tsaye tana sauraron su tashin hankalinta ya karu. saboda lafuzzan da ta ji Munawwa ta fad’a, wanda ko tantama babu daga cikin zuciyarta suke fitowa.

Dalilin zuwanta shi ne saboda ita ta turo Munara ta kira ta, da ta gaji da jiran tsammani ta biyo bayansu. Saboda tana jin tsoron Daddynsu ya san ta fito gidan, ashe da rabon ta ji abin da zai k’ara d’aga mata hankali. Don kam Munawwa ta tabbatar mata da yadda take son wannan mutumin.
Kafin ta tantance abin yi Munara ta k’ara jawo wa Munawwa hijabi ta shake ta iya k’arfinta ta matse ta jikin k’ofar gate. Tare da nuna ta da d’an yatsa kamar za ta kai mata naushi ta ce,
“Bakinki ya kiyayi fad’in sunan HAIDAR d’in nan tun kafin na sauya miki kamanni wallahi.”

Da sauri Mumny ta k’araso wurinsu tare da katsa masu tsawa tana bai wa Munara umurnin ta sake ta, ganin yadda ran Mummy ya b’ace ya sa ta sake ta tana huci. Munawwara kam duk da ta ji zafin shak’ar amma hakan bai hana ta yin murmushi mai sauti ba ta sake cewa,
“HAIDAR is my own not u, because naki na bugi ne nawa ne real don ga shi kin gani da idonki.”

Munara ta yi cikin Munawwa kamar wata zakanya ta kai mata duka, Mummy ta d’aga hannu ta d’auke Munara da wani bahagon mari cikin tsananin fushi ta ce,

“Ke wace irin kangararriyar yarinya ce ke da ba kya jin magana? Sh ikenan ni ba za ki tab’a bari na na huta ba? Masifar safe daban ta dare daban, to wallahi na fara gajiya sai na bar muku gidanku tun da ba kwa son ganin farin cikina.”

Ta k’are maganar tare da fashewa da wani kuka mai tsanani, Munawwa ta yi saurin zuwa wurinta ta rungumeta ita ma sai kukan take yi cikin tashin hankali. Saboda kukan da ta ga mummy tana yi ya d’aga mata hankali matuk’a.

Munara kam tana jin zafin marin babu shiri ta k’walla k’ara tare da kiran sunan Daddy, tana fad’in,
“Daddy ka zo za su kashe ni tun da kai kad’ai ne mai sona a gidan. Wayyo Daddy ka zo ka gani saboda Munafukar ‘yarta za ta cire mini kunne.”

Aikuwa sai ga Daddy afujajan ya katse kallon news d’in da yake yi ya fito saboda jin k’arar muryar shalelen shi da ya jiyo, yanayin da ya fito kamar wani wanda zai yi fad’a da k’atti goma. Amma yana yin arba da Mummy dake ta kuka gwanin ban tausayi dole jikin shi ya yi sanyi, duk da kai tsaye wurin ‘yarsa ya nufa. Amma ya ji zafin kukan da ya ga tana yi a ransa, shi ya sa bai ce k’anzil ba ya ja ‘yar shi suka shige cikin gida yana rarrashin ta, zuciyar shi a cike fam da jin zafin kukan da Mummy take yi.

Bayan shigewarsu ne Baba Isah da ke tsaye k’ofar d’akin shi ya k’araso wurinsu Mummy ya fara ba su hak’uri cikin lafazi mai dad’i. Mummy ta tsayar da kukanta ta koma rarrashin Munawwsra, sannan ta ja ta suka shiga cikin gida, Malam Isah ya bi su da kallo gwanin ban tausayi. Saboda duk abin da aka yi kuma aka fad’a a gaban idon shi.

****
B’angare Basarake kuwa, yana tafe iska yana kwasar shi, saboda yadda jikin shi ya yi sanyi k’alau. amA kan matsananciyar soyayyar Munawwa da ta saka shi kasala. Musamman idan ya tuno da kalamanta inda take cewa,

‘Aliyu i love u morethan anything in dis world, i don’t have any word to describe how…’

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 15Bakon Yanayi 17 >>

1 thought on “Bakon Yanayi 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×