Skip to content
Part 20 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Kakale ma da taga sak’on ta ji dad’i sosai, amman fa zuciyarta tak’i kwantawa da budurwar da yake son, saboda ita dai da zai bi ta tata; da ya rabu da tagwayen duka ya je ya nemi wata ya aura. Saboda samun nutsuwar auren shi, don ita ma ta hango akwai matsala cikin wannan tafiya, duk da bai fayyace mata komai ba, amma a ɗan abin da ya sanar da su ta hango matsala, don Hausawa sunce abin da babba ya hango yaro ko ya hau sama ba zai iya hango shi ba. Ita ma ya had’a ta da Munawwa ta yi mata godiya tare da d’an barkwanci sannan suka yi sallama.

Sannan ya fito ya je wurin Abbansa, sun dad’e suna tattauna matsalolin kasuwancinsu da ci gaban da suka samu, tare da shawarwarin hanyoyin da za su bi su k’ara fad’ad’a shi a fad’in Nigeria da k’asashen ke’tare. Basaraken ya fara sanar da shi akwai yarinyar da yake so amma ba su kai k’arshe ba, ALHAJI Dikko ya yi murna sosai kuma ya yi masa fatar alkhairi.

Munawwa da Mummy kam suna jin ya ce zai zo, amma sai nan da kwana biyu, hankalinsu ya k’ara tashi. Saboda su a son ransu ya zo ranar don kawai ya warware wa Daddy komai da bakinsa a huta. Mummy ta ce da Munawwa ta je inda ta ce tana ganin motarsa ta tambayi mai shagon ta ji gaskiyar komai, tun da ba zai rasa sanin wane ne shi ba, aikuwa tana k’are shirin makaranta ta bar wa Munara key d’in motarsu ta hau napep ta nufi wurin d’an Liti mai shago. Bayan sun gaisa take tambayar shi

“Don ALLAH malam wani bawan ALLAH nake tambaya”

D’anliti yana auna wa wani yaro sugar ya ce,

“Ina sauraron ki ‘yanmata! ALLAH ya sa dai na san shi”

Munawwa ta ce, “Ka san shi ma ai, domin a nan unguwar taku yake”

D’anliti ya mik’a wa yaron sugan sannan ya mayar da hankalinsa a kanta ya ce,

“To wane ne a cikin unguwar nan?”

Munawwa ta gyara tsayuwarta ta ce,

“Ina wata mota da ake ajiyewa a gindin wannan bishiyar dalbejiya?”

D’an liti ya d’aga kai alamar ya gano, ta ce,

“Yawwa to don Allah ka san mai motar?”

Gaban D’anliti ya fad’i, saboda ya ji tsoron ka da a ce wani abu Aliyu ya aikata, cikin sanyin jiki ya ce “Eh na san shi sosai ma, me ke faruwa?”

Munawwa ta yi saurin fad’in,

“Eh to ba abin da ya yi mummuna gaskiya! Kawai dai ina son na san mene ne sunansa? Kuma mene ne sunan mahaifinshi? Kuma mene ne sana’ar shi?”

D’anliti ya yi hanzarin faɗin,

“Rigiji gabji! To a gaskiya ni sunansa kawai na sani, amma ban san sunan Babansa ba, don saboda ya ce mini shi ba d’an garin nan ba ne, wani aiki ne ya kawo shi garin nan. Haka ma ni ban san sana’arsa ba, abu d’aya ne na sani yana da kirki sosai. Sannan a fahimtar da nayi shi mutum ne mai son ibada, don watarana ma shi yake ja mana jam’in SALLAH a wannan masallacin”

Munawwa ta kai kallonta ga wani d’an fili da aka zagaye da duwarwatsu, inda yake yi mata nuni da hannu sannan ta dawo da kallonta gare shi ta ce,

“Mene ne sunan shi?”

Kai tsaye d’anliti yace “Aliyu.”

Kirjin munawwa ya buga dam-dam! Saboda sunan Aliyunta da ta ji ya kira a hankali ta ce, “Anya ba Nuradden sunan shi ba kuwa?”

D’anliti ya shiga tunani na d’an lokaci sannan ya ce,

“Aliyu ne sunan shi gaskiya, sai dai idan ba wanda kike nufi ba ne.”

Munawwa ta fara tafiya sannan ta ce,

“OK nagode sosai da lokacin da ka ba ni.”

Ta juya ta fara tafiya har takai wurin napep d’in da ke tsaye tana jiran ta, D’anliti ya d’aga murya ya ce,

“Ba ki faɗa mini sunanki ba Hajiya!”

Tayi murmushi mai sauti kai tsaye ta ce,

“Munawwara!”

Tana k’are fad’a ta shige napep d’in suka bar wurin, zuciyarta sai sak’e-sak’e take yi mata a kan cewa,

‘Waton dai ba shi ba ne Nuradden d’in? Oh ALLAH! Shi kuma wannan mutumin wai a ina ma ya gan ni nikam?’

Sukuku take har aka tashi School ta dawo gida, Mummy ma da ta ji ba shi ba ne ta shiga rud’u tare da zullumin zuwan ranar, Domin tun daren ranar da ya ce zai zo suke ta addu’ar ALLAH ya sa ya zo, kada ya ce kuma wani uzuri ya rik’e shi. Ranar ta kasance Alhamis, tun da safe Nuradden ta turo mata text a kan ta dubi zuwan shi.

*****

Basarake kam a daddafe ya yi kwana uku Abuja ya baro garin tare da Abokinsa Nuradden suka yo Kaduna, kai tsaye suka nufi hotel d’in da yake sauka, bayan sun ci sun sha Nuradden ya yi shigar manyan Alhazawa. Domin ko shaddar dake jikinsa ba k’aramin mai kud’i ba ne zai saka ta, don agogonsa ma kawai zai yi 50k balle takalman da ke k’afarshi da hula.

Nuradden fa ya fito tamkar wata d’an daren goma sha biyu, fuskarsa sai shek’i take yi, don ko fatarsa kaɗai aka kalla a take za k’a gano hutun da ya ratsa jikin shi, duk da shi ba fari ba ne kamar Basarake, haka kuma bai kai basarake kyau; amma ko kad’an babu maraina a halittar shi komai ya ji babu kushe.

Sab’anin Basarake da ya yi shigar da ya saba idan zai je gidansu Munara, waton dai wani k’aramin yadi ne mai sauk’in kud’i amma yasha guga sosai, kuma ya yi masa kyau a jikinsa, saboda ire-iren kayan da yake sakawa kenan idan zai je gidan, don takanas ya sa aka d’inka masa su don kawai ya cika manufar da yake ƙoƙarin kai wa ga ci.

A cikin wata arniyar mota sabuwa suka shiga, direba ya ja su suka tafi. Basarake kam ana kaiwa wurin d’an liti aka ajiye shi, sannan su suka wuce kai tsaye sai gidan su Daddy.

Munawwa kam tun lokacin da ya ce zai zo madadin ta ji farin ciki sai kuma ta koma fad’uwar gaba, saboda ita dai har zuciyarta ba ta jin wata murna ballantana d’okin ganin shi, fatarta kawai ya zo ya tafi da kayan shi ko da za ta samu natsuwa da kwanciyar hankali.

Mummy ce ke ta farin ciki da zuwan shi, yayin da Munara take ta yi musu kallon uku saura kwabo, tana wani mere idan ta ga Mummy ta wuce tana ta kiciniyar had’a abin tarbon bak’on, Munawwa kam ita har da guzurin tsaki take samu gare ta idan sun had’a ido ko sunyi clashing.

Ko da k’arfe d’aya na rana ta yi suna kitchen suna aiki, Mummy tace da Munawwra ta je ta yi wanka. Haka ta tafi zuciya babu dad’i ta yi wanka ta yi SALLAH tare da yin shirinta normal kamar yadda ta saba, Mummy tana ganin shirin da ta yi ta ba ta umirnin ta je ta sake kaya. Sannan ta je ta saka wani boil wanda aka yi wa aikin fonis ya sha dinkin doguwar riga, tana cikin shirin ne wani text ya shigo yana sanar da ita nan da minti biyar ta zuba idon ganin shi.

Gabanta ya k’ire ya fad’i dam-dam! Ta fito daga d’akin nasu ta nufi kitchen inda take tsammanin Mummy tana can, Munara da ke falo kwance tana kallo da remote a hannunta tana canza tashoshi, ta bi bayanta da kallo sannan ta buga wani uban tsaki. Munawwa ta yi kamar ba ta ji ta ba, Mummy tana ganinta ta fara murmushin jin dad’i ta ce,

“Ko ke fa! Yanzu ba ga shi kin k’ara fitowa ba.”

Munawwa ta yi murmushi tana wasa da ‘yan yatsunta da suka sha jan lalle, saboda Mummy ta matsa dole sai da taje aka yi mata shi tare da zuwa saloon aka wanko mata kanta. Munawwa tana k’ok’arin yin magana sai ga sallamar Malam Isah a bakin k’ofar falon, yana sanar da su bak’on ya iso, kirjinta ya k’ara bugawa da sauri da sauri, Mummy ta ce da shi ya kai shi d’akin bak’i dake cikin compound d’in gidan, sannan ta kalli Munawwa ta ce je ki ki k’ara shiryawa bari na je na sanar da Daddynku.

Gudu-gudu sauri-sauri ta haye sama zuciyarta cike da farin ciki da jin dad’in, bakinta a washe take sanar da Daddy zuwan shi, banza ya yi da ita kamar ba zai ce komai ba sannan ya ce,

“To na ji! Ko kuma sai kin saka ni a gaba kin kai ni wurin shi?”

Mummy ranta a jagule ta ce,

“ALLAH ya ba ka hak’uri.”

Sannan ta fito zuciyarta cike da jin zafin bak’ank’anun maganar da yake sakar mata tun ranar da ya ga wannan motar, kamar su suka rok’a aka ba su.

Sai da ya kwashi minti biyar a zaune bai motsa ba sannan ya tashi ya sauko ya nufi wani d’aki da zai kai shi kai tsaye cikin d’akin bak’in, tun daga k’amshin turaren Nuradden da ya jiyo ya san lalle wannan ba k’aramin mutum ba ne, tunaninsa ya kwance a lokacin da idanuwansa suka yi tozali da Nuradden da ya hakimce a kan kujera sai shan k’amshi yake yi yana latsa tsadaddar wayarsa sabuwa dal, Daddy ya shigo da sallama Nuradden ya amsa cikin gadara-gadara, Daddy ya zauna ba tare da ya ga aibin abin da Nuradden ya yi ba, saboda yadda ya yi masa kwarjini a ido sosai kuma ta tabbatar da ba ɗan gidan ƙananun mutane ba ne.

Bayan sun gaisa Nuradden ya fara magana cikin wata isa-isa ya ce,

“Ni sunana Muhamnadu Nuradden Alhaji Mustapha mai gwal”

Da sauri Daddy ya kai kallonsa ga Nuradden cikin d’inbin mamaki ya ce,

“Kana nufin d’an gidan Mustapha mai gwal ne kai?”

Nuradden ya k’ara tabbatar masa a cikin rawar baki mai cike tantama Daddy yace,

“Na hannun daman Alhaji Dikko mai Gwal fa?”

Nuradden ya d’aga masa kai fuskarsa cike da izza ya ce,
“Na ga ‘yarka Munawwara! Kuma na ji ina sonta da aure, naso na zo kafin zuwan sak’ona, sai ga shi tafiya ta kama ni, saƙon neman da kake yi mini ya sa na dawo ƙasar. Domin na karbi kiranka na ajiye komai na zo, fatan dai ba wata matsala ce ta cisgo ba?”

Daddy jikinsa yana tsumar farin ciki ya ce,

“Ba wata matsala, kawai dai ina son na san wane ne yake son ‘yata, don wannan kyauta da ka yi mata ta ba ni tsoro matuƙa. Shi ya sa na ce ka zo na ji ta bakinka, saboda mu fita daga kokwanton da muke yi a kanka da sakon duka, don da na san kai ne; da ba zan tayar da hankalina ba. Amma yanzu shi kenan hankalina ya kwanta, in dai Munawwara ce ka d’auka ma kamar an yi auren ku an gama, saboda na ba ka ita kyauta duk lokacin da kake so ka zo kawai a d’aura muku aure.”

Nuradden ya yi murmushin gefen baki sannan ya ce,

“Da sauri haka?”

Daddy ya gyara zamansa sannan ya ce,

“Waye bai san ALHAJI Dikko da Alhaji Mustapha a fad’in Nigeria ba? Ai Mahaifinka sananne ne a faɗin wannan nahiya tamu, kuma kowa ya shaida su mutanen kirki ne, to me za a jira? Ai burin kowane Uba ya aura wa ‘yarsa miji nagari d’an gidan Mutunci, kuma Munawwara ta samu tun da har Allah ya haɗa ta da kai.”

Nuradden ya ji dad’in yabon iyayensu da ya ji Daddy ya yi har cikin ransa, a cikin muryarsa mai cike da izza ya sake cewa,

“Eh duk haka ne zancenka, amma ina son a fara bincikar yarinyar idan har tana so na, na amince a bata dama a hannunta ba tare da an tirsasa mata aure na ba.”

Daddy ya ce, “Ko a musulunci ni ne ya fi dacewa da na nemo mata mijin aure a matsayinta na budurwa, kuma ai ita ce ta kawo ka ba mu muka kawo ka, muka ce dole sai kai za ta aura ba. Don haka ina ganin wannan ba matsala ba ce, ka je kawai ka shiryo a duk lokacin da ka tashi ni zan aura maka ita.”

Nuradden ya gyara zamansa sannan ya ce, “Na gode sosai da wannan karamci, ALLAH ya sanya alkhairi a cikin lamarin.”

Daddy ya ce “Amin” tare da mik’ewa tsaye yana cewa,

“Bari na je na turo maka ita.”

Yana k’ok’arin fita d’akin Nuradden ya ce, “Ranka ya dad’e account d’inka nake so ka ba ni, bakin daddy har rawa yake yi wurin fad’o masa account details sannan ya fita da farinciki kamar ya take kan jariri. Jikinsa har rawa yake yi ya isa wurin su Mummy da ke falo, ya kalli Munawwa cike da jin dad’in da ya mamaye zuciyarsa ya ce,

“Tashi ki je! kKe yake jira! ALLAH ya yi miki albarka…”

Kafin ya iyar da maganarsa ya ji shigowar alert da sauri ya fiddo wayar da ke aljihunsa yana dubawa ya zaro ido waje, su Mummy suka bi shi da Kallo Munara ta yi saurin fad’in,

“Daddy lafiya?”

Daddy ya d’ago fuska cike da murna ya ce,

“200k, mai neman auren Munawwara ya turo mini yanzun nan.”

Ga baki d’aya suka zaro ido, Munawwa da ke k’ok’arin barin wurin tana jin maganar k’irjinta ya tsananta bugawar da yake yi, Munara dafe da gaba ta ce, “200k fa Daddy,? Cab! Ah lalle Munawwa kura ta samu nama a ɓagas.”

Mummy ta maka mata harara, Daddy ya zauna bakinsa yana rawa ya ce,

“D’an gidan Mustapha mai Gwal ne ashe, ai ba banza ba, kai da ganin wata kyauta ka san sai gidan girma.”

Mummy da Munara suka k’ara zaro ido tare da had’a baki wurin fad’in,

“Mustapha mai Gwal fa?”

Yana girgizar Kafafuwa ya ce,

“Shifa na hannun daman ALHAJI Dikko. Mai gwal, wanda a tarihi ma an ce shi ne silar arzik’insa saboda abokai ne na k’ud da k’ud. Don shi Dikkon an ce shi kansa bai san iya adadin dukiyarshi ba, wanda a tarihin masu kud’in Nigeria idan bai zo na biyu ba to dole ya zama na Uku.”

Mummy tayi shiru kamar ruwa ya ci ta, Munara kam sai zancen zuci take yi,

‘Ina ma ni ce, don ita wannan sokuwar ba sanin kan duniya ta yi ba.’

Munawwara kam tana k’ara kusantar d’akin bak’in gabanta yana k’ara fad’uwar da yake yi, ta d’an ja lokaci a k’ofar d’akin sannan ta yaye labulen d’akin ta shiga da makalalliyar sallamarta a baki, kanta a k’asa ta samu kujera ta zauna, ranta a had’e ta fara gayar da shi kamar ba ta so, Nuradden kam yana d’ora idonsa a kanta ya ji k’irjinsa ya buga dam-dam! Musamman yadda ta motsa lab’b’anta wurin gayar da shi ya burges hi matuk’a. A hankali ya ce,

“Munawwara laifin me na yi daga zuwana? Na ga ko kallo na ba a son yi, ballantana a had’a idanuwa da ni!”

Ta k’ara sunne kanta tare da zubowar wani hawayen da ba ta san ko na mene ne ba.

<< Bakon Yanayi 19Bakon Yanayi 21 >>

2 thoughts on “Bakon Yanayi 20”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×