Ta k'ara sunne kanta tare da zubowar wani hawayen da ba ta san ko na mene ne ba. Cikin tashin hankali ya ce,
"Subhanallah! Me aka yi da zafi haka, har ya saka ki kuka Munawwara? Idan har ni na yi laifin ina neman yafiya kaina bisa wuya, tun kafin hukuncin kisa ya hau kan Nuradden!."
Munawwa ta share hawayenta kanta a sunkuye ta ce, "Ba komai" sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce,
"Yau ga ni a gabanki Munawwara, na zo da ƙoƙon barana a kan ki ba ni soyayyarki."
Munawwara ta d'ago fuskarta suka kalli. . .
Nice read