Skip to content
Part 21 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Ta k’ara sunne kanta tare da zubowar wani hawayen da ba ta san ko na mene ne ba. Cikin tashin hankali ya ce,

“Subhanallah! Me aka yi da zafi haka, har ya saka ki kuka Munawwara? Idan har ni na yi laifin ina neman yafiya kaina bisa wuya, tun kafin hukuncin kisa ya hau kan Nuradden!.”

Munawwa ta share hawayenta kanta a sunkuye ta ce, “Ba komai” sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce,

“Yau ga ni a gabanki Munawwara, na zo da ƙoƙon barana a kan ki ba ni soyayyarki.”

Munawwara ta d’ago fuskarta suka kalli juna ido cikin ido tace da shi,

“Ka yi hak’uri an riga ka tuni, don har an yi mini miji, ka yafe mini, na yi maka laifi tun farko da ban sanar da kai gaskiya ba. Abin da duk ka ba ni komai yana nan yadda ka kawo shi, idan ka tashi ka tafi da abinka gabaɗaya na gode Allah ya ba da ladar niyya!”

Ta yunk’ura za ta tashi; sai ga sallamar Munara da k’aton tire sai wani shu’umin murmushi take yi. Saboda ta jiyo abin da Munawwara ta fad’a, kuma har a ranta ta ji dad’in hakan, musamman da ta d’ora idodanuwanta a kan Nuradden. Sosai ta yaba da tsarinsa, tana ajiye tiren ta zauna tana gayar da shi tare da fara zuzzuba masa abincin. Nuradden yana murmushi tare da k’ara k’ule kallonsa ga Munara, saboda yana son ya gano bambancin da suke da shi, amman duk iya nacin shi ya kasa gano bambancin nasu, don shi idan ban da ya gansu su biyu wuri ɗaya; da sai ya ga kamar ma duka mutum d’aya ce ba biyu ba. Abin da ya bambanta su a lokacin kawai suturar da ke sanye jikinsu. Munawwa da ke tsaye bakin k’ofa rik’e da labule fuska ba walwala ta ce,

“Ni zan shiga daga ciki, ALLAH ya sauke ka lafiya.”

Tana k’are fad’ar haka ta fice fitt, Munara ta bi ta da kallon takaici sannan ta dawo da kallonta a kansa ta ce,

“Don ALLAH ka yi hak’uri, wani matsiyaci ne take so, wanda ko cikin matsiyatan shi ne number one.”

Nuradden ya ji zafin zagin da ta yi wa abokinsa har tsakiyar ransa, amman ya yi k’ok’arin dannewa ya zaro kud’i a aljihunsa ya ajiye gabanta sannan ya ce,

“Na saka ki ki zamo sarkin yak’ina, ina son ki janyo mini ra’ayinta a hankali har ta yarda da ni.”

Munara ta kai kallonta ga kud’in sannan ta ce,

“Da ka bar abinka don wannan kangararriyar abin da duk ka ji ta fad’a; to da wuya a iya tanƙwara ta a kansa, tun da ta nuna ba ta sonka sai dai ka yi hak’uri ka je ka nemi wata. Saboda son wancan mutumin ya riga da ya rufe mata ido ruf ba ya ganin kowa sai fuskarsa ta dodanni.”

Nuradden ya mik’e tsaye saboda yana jin y kamar ya make ta a wurin, cikin damuwar da ta bayyana kan fuskarsa ya ce,

“Ni zan tafi, sai kuma wani lokacin idan na dawo.”

Har ya kai bakin k’ofa ya juyo ya ce,

“Bani account d’inta idan kin sani”

Munara ta dinga karanto masa yana lodawa a wayarsa, sannan ya mayar da wayar aljihunsa ya fita yana gyara zaman babbar rigarsa, Munara ta bi shi da kallo a ranta ta ce,

‘Very awesome gentleman’

Saboda ya burge ta sosai, ta tashi tsam ta koma cikin gida. Inda ta tarar da Daddy da Mummy kad’ai a falo, jikinta yana rawa ta ce,

“Daddy ya ce zai tafi”

Daddy ya ƙwala wa Munawwa kira dake d’akinsu, ta fito afujajan idonta a kansa, tana zuwa ya ce da ita,

“Je ki ki raka shi.”

Munawwa ta fito ranta a jagule ta nufi k’ofar gidansu, tana lek’awa sai ga ta da fitowa gaba d’aya, saboda farin ciki da ya lulleɓe mata zuciya. Saboda ganin sahibul k’albinta Basarake, da ke zaune a kan wani dutsi yana k’ok’arin kiranta a waya.
Kai tsaye ta nufi wurinshi fuskarta a washe saboda farin cikin da ya lullub’e mata zuciya, yana duk’e ya ji alamun tsayuwar mutum a kansa, da sauri ya d’ago idonsa ya yi tozali da kyakkyawar fuskarta tana murmushi, a take shi ma farin ciki ya lullub’e tasa zuciyar. Cikin natsuwa ya mik’e tsaye yana k’are mata kallo, saboda shigar da ta yi ta burge shi sosai, a hankali ya bud’a bakinsa ya ce,

“My beautiful.”

Munawwa ta rufe fuskarta da tafukan hannuwanta, ya bi yatsunta da kallo, jan lallen da aka yi mata ya k’ayatar da shi matuk’a, a hankali ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce,

“Yau kunyata ake ji kenan? Salon kada na samu saki jikin da za a yi mini sannu da zuwa, ballantana na samu ace mini ya hanya.”

Munawwa ta sauke hannuwanta tana murmushi tare da wasa da ‘yan yatsunta ta ce,

“Ba haka ba ne ba.”

Ya yi saurin fad’in, “To mene ne?”

Za ta yi magana kenan suka tsinkayo muryar Munara tana fad’in,

“Amman dai wannan mutumin an yi k’unatacce, wallahi ALLAH ya wadaran wata rashin zuciya! Yanzu duk korar da Daddy ya yi maka bai isa ya sa ka daina zuwa gidan nan ba, sai ka kwaso kutaren kafafuwanka ka dawo? To ALLAH ya kyauta, amma wallahi an yi asarar kud’in tara, kuma an yada zuciya kare ya cenye!”

Ta k’are maganar tare da buga tsaki ta nufi inda Nuradden, wanda har lokacin yake jingine da motar da suka zo da ita, sai dai sab’anin d’azu ba wayar yake latsa ba. Rungume yake da hannuwansa biyu yana kallon su Basarake, maganganun da ya ji Munara ta fad’i sun b’ata masa rai sosai, ta yadda b’acin ran ya bayyana kansa a kan fuskarsa. Yanayin da ta ga fuskar tasai ne ya sa ta shiga taitayinta tare da k’ara jin haushin Munawwa da ta biye Basaraken, don ita a tsammaninta ganin da ya yi musu ne ya sa shi b’acin rai. Cikin muryar rarrashi ta fara magana,

“Ka yi hak’uri don ALLAH, WALLAHI haka muke fama da ita, na rasa me ta gani a jikin wancan matsiyacin har take kula sa ta nemi barin ka.”

Nuradden ransa ya k’ara baci, ya furzar da iska a bakinsa cikin kakkausar murya ya ce,

“Wane ne shi?”

Munara ta kai kallonta gare su sannan ta ce,
“Waye shi fa, ban da k’aton matsiyacin da a kallo d’aya za ka hango tsabar talaucin da ya gada iyaye da kakanninsa.”

Nuradden ya yi mata wani kallo har sai da hantar cikinta ta kad’a, fuskarsa a tsuke ya ce,

“Miye dangantakar su?”

Munara ta yatsina fuska sannan ta yi mere ta ce,
“Shi ne dai wanda nake fad’a maka tana so, ita ko kunya ma ba ta ji.”

Ta k’are maganar tare da yin tsaki, Nuradden cikin fushi ya gyara zaman rigarsa, ya yi cikinta kamar zai dake ta da sauri ta ja baya. Kai-tsaye ya wuce ta ya nufi inda suke tsaye suna hira, domin gabaɗaya hankalinsu ya d’auku sosai sun nutsa cikin nuna wa juna k’auna, sai ganin mutum suka yi a kansu. Cikin kakkausar murya mai cike da fushi Nuradden ya kalle ta ya ce,
“Wane ne shi da har kika ba shi fuskar da ni kika kasa ba ni irinta tun a zuwana na farko gidanku? Na kuma kika zab’i wulakanta ni a kansa”

Munawwa ta yi wani murmushin tura haushi ta ce,
“Shi ne mijin da zan aura, ko ka manta na sanar da kai an tsayar mini da miji?”

Nuradden ya zaro ido a cikin rawar baki ya ce,

“Miji fa kika ce? Wannan shi ne mijin? Ai ni na za ta mai wanki da gugar gidanku ne, to ke Munawwara in dai wannan ne me na sama ya ci ballantana jefo mini? Ki yi wa kanki karatun ta natsu, ki zo inda za ki huta ki ji dad’i iyayenki da ‘yan uwanki su ji dad’in su ma. Sannan ki ci arzik’i har ki yi wa wani hanyar samu, idan kin amince da ni zan jiyar dake dad’in da ke cikin duniyar nan gabaɗaya. Domin zan ajiye ki cikin k’aton gida, hajji duk shekara, umrah duk bayan wata d’aya, sutura sai kin zab’a, mota sai wacce kika ga damar hawa, Don haka ina ba ki shawara ki amince da ni ki mori kurciyarki.”

Ya k’are maganar yana wata dariyar shakiyanci, Munawwa ta yi d’an murmushi ta kalli Basarake ta kalli Nuradden sannan tace,
“Ni kud’i ba su ne gabana ba, ka ga wannan; to shi ne cikar muradin zuciyata idan har na aure shi. Ina maka fatar samun mace tagari, amman dai ni kam na riga da na yi wa kaina zab’in da ruwa da iska ba za su canza tsayuwata a kan ra’ayina ba.”

Nuradden ya gyara tsayuwar shi tare da gyara zaman babbar rigarsa ya ce,
“Mahaifina siyar da gwalagwalai ne sana’arsa, ni ma ita ce tawa sana’ar, zan yi ta baki su ki yi ta ado har sai kince a barsu haka nan sun wadace ki. Don haka kada ki bari ƙurciya ta cuce ki, saboda yanzu an daina aure don soyayya, muradi kawai ki samu inda hankalinki zai kwanta, ki ji dad’i iyayenki su ji.”

Munawwa ta b’ata fuska sannan ta ce,
“Ni dai hak’uri kawai zan ba ka gaskiya, saboda na riga da na yi wa zuciyata zab’in mijin da zai zamo abokin rayuwata.”

Nuradden cikin fushi ya fara magana a sama yana cewa,
“Yanzu a kan wannan k’aramin mutum za ki wulakanta ni? To ki sani ko kina so ko bakya so sai na aure ki, kai kuma daga yau na sake ganin k’afarka a k’ofar gidan nan sai nasa an ɓatar mini da kai a garin nan!”

Yana k’are surutan ya saka hannu aljihu ya ciro bandur d’in 1k sababbi fil ya cilla masa a jiki, sannan ya ce,
“Ka je ka ji da kanka, tun kafin fushina ya sauka gare ka da ahalinka gabaɗaya!”

Yana k’are fadar maganar ya wuce fuuu ya fad’a mota, Munara ta yi saurin bin bayansa ta fara ba shi hak’uri ko kallo ba ta ishe shi ba ya sa direba ya ja motar suka bar k’ofar gidan, tare da bad’a mata k’ura a jiki. Cikin zafin nama ta shige gida da guda, Munawwa tana ganin haka hankalinta ya tashi, saboda sanin Daddy yana gida. Cikin sauru ta ce da Basarake,

“Ka yi hak’uri ka je za mu yi waya, saboda Daddy yana gida ba na son ya zo ya same ka a nan, ka d’auki kuɗinka ka je za su yi maka amfani.”

Basarake ya saka hannu a aljihu ya k’are wa kud’in kallon sannan ya duk’a ya tattara su wuri ɗaya, ya taso ya mik’a mata ta k’i karb’a. Ya jayo gefen gyalen da ke sanye jikinta ya zuba kud’in ya k’ulle, sannan ya ce,

“Idan ya zo ki mayar masa da kuɗinsa, kuma ki ce masa na gode.”

Ya juya cikin fushi, har ya fara tafiya ta kira sunan shi a hankali ta ce,

“Aliyu!”

Ya tsaya ba tare da ya waigo ba, cikin sanyayyiyar muryarta ta ce,
“Ka turo iyayenka su zo nema maka aure na, ni na amince zan aure ka a duk yanayin da zan same ka.”

Basarake ya yi saurin juyowa a hankali ya dawo kusa da ita ya tsaya, ido cikin ido ya ce da ita,
“Za ki iya auren talakan da bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba? Za ki iya auren maraya wanda iyayen shi ko a baya ba wasu bane ballantana yanzu? Za ki iya auren wanda a kullum safiya sai ya tafi nema sannnan ya samo abincin da zai ba ki a kowace rana?”

Cikin dakiya ta yi kundunbalar fad’in,

“Arzik’i da rashi duka na ALLAH ne, don haka idan har ka shirya aure na; to ka turo iyayenka su zo gidanmu.”

Basarake wani farin ciki lullub’e masa zuciya, yana k’ok’arin yin magana sai ga Daddy ya fito kamar an jefo shi, yana k’yalla ido ya hango Munawwa tsaye da Basarake cikin sauri ya isa gare su, babu b’ata lokaci ya d’aga hannu ya zabga mata mari, sannan ya ba ta umurni a kan ta shiga gida ko ya tattaka ta.

Sai da Munawwa ta shige gida sannan ya dawo da kallonsa ga Basarake bakinsa yana kumfa sabiloda bala’i ya ce,

“Duk na k’ara ganin k’afarka a ƙofar gidan nan; sai na had’a ka da ‘yan sanda sun lallasa mini kai wallahi!”

Basarake yayi saurin duƙawa ƙasa ya dafa k’afar shi yana cewa,

“Don ALLAH maigida ka yi hak’uri, wallahi da gaske nake son ta, ita ma tana so na, don ALLAH ka bar mu mu yi aure.”

Cikin zafin nama Daddy ya fincike k’afar shi tare da ja baya kad’an, yana yi masa kallon wulak’anci ya ce,

“Aure! Aure fa kace? Duk ta rasa wa za ta aura sai kai? To bari ka ji wannan yaron da ka gani shi ne na bai wa ita, kuma shi ne wanda za a d’aura wa aure da ita nan da d’an lokaci. Saboda haka ka taimaki kanka ka d’auke k’afarka daga gidan nan, tun kafin ka tsokalo fushin masu kud’i su ɓatar da kai a banza ni babu ruwana.”

Basarake ya mik’e tsaye tare da kakkab’e k’asar da ke hannunsa, sannan ya fara tafiya zai bar wurun ba tare da ya ce da Daddy komai ba. Har ya yi taku d’aya biyu zuwa uku Daddy ya d’aga murya ya ce masa,

“ka tallafi talaucinka kada ka bari zuciyarka ta yaudare ka ka yi jayayya da masu kud’i, don wannan yaro da zan aura wa Munawwara d’an gidan Mustapha mai Gwal ne, saboda haka ka je ka nemo daidai kai. Ƙ’warya ta bi k’warya kawai, don idan ta hau akushi ba za ta moru ba.”

Yana k’are fad’ar maganganun ya yi fuuu ya shige gida, tare da bugo ‘yar k’aramar k’ofar da k’arfi. Baba Isah yana ganin Daddy ya shige ya lek’o wajen, ga mamakin shi ya hango Ali tsaye d’an nesa da gidan kad’an kamar an dasa shi, da sauri ya fito fuskarsa a washe ya ce,

“A’a Ali saukar yaushe?”

Basarake ya shanye damuwar shi, cikin sauri ya fad’ad’a fuskarsa da fara’a ya ce,
“Yau na diro Baba, ban dad’e da shigowa garin ba shine na ce bari na zo na gaisa da ku.”

Baba isah ya k’araso wurin shi yana ta farincikin ganin shi, Aliyu ya rusuna ya gayar da shi cikin ladabi, Baba Isa ya ce da shi,
“Ya ka baro mutanen garin naku? Da fatar dai kowa lafiya?.”

Basarake yana ‘yar dariya ya ce,

“Kowa lafiya Baba, duka suna gaida ku.”

Yana maganar ya saka hannunsa aljihu ya ciro akwatin ‘yan hannu da zobensu ya mik’a wa Baban, cikin mamaki ya saka hannu ya karb’a sannan ya ce,

“sak’on wa ye?”

Basarake yana Murmushi ya ce,

“Munawwara na siyowa Baba, sai ga shi Daddy bai bari na ba ta ba, don ALLAH ka ba ta tsarabarta ce.”

Ya saka hannu aljihu ya mik’a wa Baba Isah kuɗi ya ce,
“Ga shi Baba kai ma ka sayi…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 20Bakon Yanayi 22 >>

1 thought on “Bakon Yanayi 21”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×