Munara ta bi kayan da kallo zuciyarta a cike da jin zafin abunda Munawwa tayi mata a gaban Mummy, don tasan daman tayi ne don Mummyn rayi mata fad'a, shiyasa tayi banza da ita bata ce da ita k'anzil ba taci gaba da cin abuncinta, Mummy ta kalli Mubawwa fuskarta cike da mamaki tace, "Me ke faruwa ne? daga ina wad'anan ababen suka fito ne."
Munawwa ta tashi zata bar falon tace da Mummy, "Ga mai kayan nan Mummy nima bansan ya aka YI ta fidda su ba."
Tana k'are maganar ta shige d'akinsu saboda. . .
Masha Allah