Munawwa ta yi saurin kallon shi ido cikin ido, zuciyarta sai aikin gudu take yi da sauri da sauri. Abin da ta hango cikin k'wayar idon shi ya sa ta yi saurin janye nata idanuwan, hawayenta bai daina sauka ba ta saka hannu ta share fuskarta, sannan ta aro jarumta ta kalle shi ba tare da ta bari sun had'a idanuwa ba ta ce,
"Aliyu ko? Me ya sa za ka yi saurin yanke jink'ai har ka furta wannan magana? Anya ko da gaske kake son ta kuwa? Ni dai na san shi so idan ya shiga. . .