Skip to content
Part 8 of 24 in the Series Bakon Yanayi by Hadiza D. Auta

Munawwa ta yi saurin kallon shi ido cikin ido, zuciyarta sai aikin gudu take yi da sauri da sauri. Abin da ta hango cikin k’wayar idon shi ya sa ta yi saurin janye nata idanuwan, hawayenta bai daina sauka ba ta saka hannu ta share fuskarta, sannan ta aro jarumta ta kalle shi ba tare da ta bari sun had’a idanuwa ba ta ce,

“Aliyu ko? Me ya sa za ka yi saurin yanke jink’ai har ka furta wannan magana? Anya ko da gaske kake son ta kuwa? Ni dai na san shi so idan ya shiga zuciyar mutum ba zai yi saurin fita cikin k’ank’anin lokaci ba, sai dai idan daman can bai kai cikakken so ba. Ni ka gan ni nan ban tab’a so ba, amman jikina yana ba ni matuk’ar na dulmiya cikinsa abu ne mai wahala na cire shi farad d’aya. Domin ba cirar k’aya ba ne balle a ce da an zare shi kenan an daina jin zafinta. Saboda shi a zuciya dafi ne da shi, haka yake tamkar k’unar wuta, wacce idan tsautsayi ya sa ta k’ona mutum; to tabbas zai dad’e yana fama da jinya, kuma ko da ya warke daga baya tabon konuwar yana nan daram a jikin mutum. Don wata k’unar ma duk tsawon shekarun da mutum zai yi a duniya tambon yana nan ba zai tab’a gogewa ba.”

Basarake ya tsura mata idanuwa tamkar bai tab’a ganinta ba, saboda maganganunta sun ratsa shi sosai kuma sun k’ara mata girma da matsayi a cikin zuciyar shi. Munawwa ta d’ago ido cikin ido ta sake cewa da shi,

“Me ya sa a matsayinka na ma’abocin son ka ke ik’irarin wata ta taimake ka ta karb’i son ka? Bacin kuma ga wacce kake bala’in son a kusa da ita? Anya sanadin haka ba za ka gurgunta d’an zaman lafiyan da ya yi saura tsakanina da ‘yar uwata ba?”

Ga baki d’aya kan Basaraken ya k’ulle, ta yadda ya rasa me ya dace ya yi a lokacin, yana k’ok’arin yin magana kiran Ummi ya shigo a wayarsa. Jiikin shi yana rawa ya fiddo ‘yar wayarsa da ko murfi babu a jiki, don ya san duk mai kiran bai wuce Ummin ko Abbunsa ko kuma kakale ba, sai kuma Abokinsa na jini da hanta. Don su kawai suke da layin, sai kuma ita kanta Munawwara da ya kira ta da ita.

Yana duba wayar ya ga Ummi ce, wani farin ciki ya lullub’e shi ya kara wayar a kunnensa yana gaida ta, Munawwa ta fara taku za ta bar rumfar ya yi saurin janye wayar a kunnensa ya ce,

“Zo ki gaisa da Ummi.”

Cak! ta tsaya ba tare da ta k’ara wani taku ba, da kan shi ya k’araso wurinta yana fad’in,
“Ummi ga ‘yarki nan ku gaisa.”

Ya mik’a wa Munawwa wayar ba tare da ta kalle shi ba ta karb’i wayar ta fara gaida ta cikin ladabi, wanda daman can d’abi’arta ce girmama babba. Ummi bayan ta amsa gaisuwar ta yi ta sanya mata albarka, saboda jikinta ya ba ta surukarta ce, kuma ga dukkan alamu ba k’aramin so Basaraken yake yi mata ba, tun da har bai ji shayin had’a su ba. Don a halayyarsa da ta sani, shi ba ma’abocin kula mata ba ne balle ya so budurwar ta san da ahalinsa. Domin tun da take da shi bai tab’a haɗa ta da wata budurwarsa suka gaisa ba, shi ya sa ta saki jiki suka gaisa, cike da farin cikin nesa ta kusu zuwa kusa, ma’ana addu’ar da suke yi masa a kullum safiya ta karb’u.

Munawwa ko, a cikin jin dad’in addu’ar da Ummin ke yi mata take ta fad’in,

“Amin, Amin Ummi.”

A cikin tsantsar farin ciki Ummi tace da ita,

“Mene ne sunan ‘yar tawa?.”

Ta sunne kai ƙasa kamar tana ganinta sannan ta ce da ita,

“Sunana Munawwara!”

Ummi ta ce,
“Sannu ‘yata kin ji, ALLAH ya yi miki albarka kuma ya k’ara had’a kawunanku, ya nuna mana lokacin da muke ta dako.”

Babu shiri Munawwa ta kai kallonta gare shi, sannan cikin sanyin murya tace,
“Amin”
Saboda jin nauyin fad’ar Amin d’in a bakinta, domin a take ta ji kunyar Ummin ta lullub’e ta. Da sauri ta mik’a masa wayar ta je jikin wata mota da ke cikin rumfar ta jingina bayanta. Tana jiran ya k’are wayar ta ji me yake nufi da abin da ya yi yanzu.
Ummi kam cikin tsantsar farin ciki, wanda ya kasa b’oyuwa a kan harshenta ta ce,
“Ka kira Hajiya ka had’a ta ita su gaisa ko don a samu natsuwarta, don yau tun da safe ta tub’ure mana sai an kawo ta wurinka, dak’yar aka shawo kanta. Ga shi duka layukanka an kira babu wacce ta shiga, wannan ce kawai aka yi sa’a aka same ka”

Yana murmushin jin dad’i ya ce,

“Ai yanzu nan zan kira ta Ummi.”

Sannan suka yi sallama ya danna wa Kakale kira caraf ta d’auka tare da cewa,

“Tun da ba zabka dawo ba ai ni sai a kawobni wurinka mu zauna tare.”

Basarake ya fara dariya mai sauti sannan ya ce,

“Haba kakalena! Yanzu dai kwantar da hankalinki ga Matata nan ku gaisa.”

Babu shiri Munawwa ta kalle shi shi ma ya k’ura mata idanuwansa ya mik’a mata wayar, tareda yi mata wani kallo wanda ya saka tsigarta tashi yarrrr!
Maganar da tabji a cikin wayar ya sa ta karb’i wayar jikinta a sanyaye ta yi sallama. Cike da farin ciki kakale ta ce,

“Waton ke kika rik’e mana shi a kaduna ko? To idona idonki, tun da na ga k’wacen maigidana kike son ki yi mini ta ƙarfi, to ki sani aro ne zan ba ki, ni ce ta k’arfen ko da auren aka yi. Don kada ki d’auka ya fi sonki da ni, na ba shi damar ya k’aro aure ne kawai don na tausaya miki ba don na kasa ba. Ko yanzu da k’arfi na, amman duk da haka ga amanarsa nan na bar miki. ALLAH ya nuna mana lokacin, kuma ya sa ina da rabon ganin ‘ya’yan Aliyu a duniya.”

Munawwa cike da mamaki ta ce,

“Amin”

Kakale tana dariya ta ce,

“Miik’a wa Basaraken wayar na ji me na yi masa zai yi mini kishiya.?”

Ta k’are maganar cikin farin ciki da azarɓabi. Munawwa ta cire wayar daga kunnenta ta mik’a masa, amman fa ta kasa d’auke idanuwanta daga kansa tana yi masa kallon tuhuma. Saboda tsananin mamakin da ya cika mata zuciya sai maimaita sunan BASARAKE take yi a cikin zuciyarta. Cike da ko in kula ya karb’i wayar suka yi ta barkwancinsu da suka saba da ita, sannan ya kashe wayar, don baya son ya fad’i wani abin da zai sa Munawwa ta gano wani abu dangane da shi. Har sai lokacin da ya yi mata kama zuciyarta kamun dumu dumu sannan ya bayyana mata kansa da wane ne shi.

Ya soke wayar a cikin aljihunsa sannan ya kalle ta, wanda ita ma kanta idonta akansa suke, saboda gubar mamakin da ya shayar da ita a lokaci d’aya. Cikin sanyin muryarta ta ce dashi,
“Me kake nufi da wannan abin da ka aikata? Idan daga baya suka gano gaskiya fa me za ka ce da su? Sannan wane auren ne na ji ana fad’a? Bayan ka san ni da kai babu wata alak’a makamanciyar wannan.”

Basarake ya yi wani murmushin rashin damuwa sannan ya ce da ita,

“Duk hakan za su faru ne idan kin babni dama ranki ya dad’e.”

Munawwa ta yi masa wani kallon kama raina ni, sannan ta ce,
“Ita Munara ka yi ya ya da son nata?,l Ko kana nufin idan ba ta amince ba sai ka yi auren huce haushi da ni kenan?”

Basarake ya daburce, cikin rud’ewa da tambayoyinta ya ce,
“Matsayinki a wurina daban yake Ranki ya dad’e, da za ki ba ni dama da kin gano gaskiyar abin da na fad’a miki.”

Munawwa ta harare shi ta ce,
“Idan har a ce na ba ka dama, to ya za ka yi da son bala’in da kake yi wa ‘yar uwata a cikin zuciyarka?”

Yayi murmushinsa mai kama da yak’e ba tareda ya ce da ita k’anzil ba, Munawwa har ta fara taku a hankali da nufin barin wurin ta waigo ta ce,
“Basarake ko? To ka je ka yi nazari da kyau, idan har za ka iya had’a taura biyu a baki kuma ka tauna su a lokaci d’aya.”

Basarake ya yi murmushi sannan ya ce,
“Ranki ya dad’e takunki daban yake da na sauran mata, hak’ik’a jikina yana ba ni cewa ke alkhairi ce a wurina, alfarmar da na rok’a a wurinki tun farko ki k’ok’arta mini, na baki lokaci ki je ki yi nazari da kyau”.

Munawwa ta maka masa wata harara sannan ta juya ta fara tafiya, amman zuciyarta cike da mamakin maganganunsa, gefe d’aya kuma kuma cike take fam da jin zafin aikin da ya saka ta, na janyo masa soyayyar Munara da ya d’ora mata nauyin komai. Tunanin da ta lula ya sa ta ci karo da Mummy ba ta sani ba, saboda yanda ta shiga sak’e sak’en ta yadda za ta fuskanci Munara.

Ganin Mummy ya sa ta yi saurin fad’in,

“Sorry Mummy”

Mummy ta kalle ta da kyau tana karantar yanayinta sannan ta ce,
“Wurinki zan je, domin na ga me ya tsayar dake tun d’azu?”

Munawwa ta saki ranta tana ‘yar dariya ta ce,
” Aliyu ne ya kira ‘yan gidansu ya ba ni su muka gaisa.”

Mummy ta kalle ta da kyau ta ce,
“Anya Munawwa wannan kula ba ta yi yawa ba? Sau biyu na ga kin yi fad’a da ‘yar uwarki a kan shi, ko dai akwai wani abu da ke tsakaninku ban sani ba?”

Munawwa ta zaro idanuwa tana dariya ta ce,
“Ba fa wani abu Mummy, ai kin san ba zan b’oye miki ba idan akwai ke ce za ki riga kowa sani.”

Tana k’are maganar ta shige d’akinsu tana murmushi, Mummy ta bi ta da kallo tare da yin tagumi. Amma fa zuciyarta ta tabbatar mata da akwai wani abin da Munawwa ta ke b’oye mata, duk da ta san halin ‘yarta da kyakkyawan halayenta na kirki, amman wannan kulawar da take bai wa d’an aikinsu ya sha bambam da na saura.

Ta sauke tagumin tare da cewa,

“ALLAH ya shige mana a gaba”

Saboda jikinta ya yi sanyi sosai, saboda tana jin tsoron a ce son shi take yi.

Har Munara ta dawo daga makaranta Munawwa ba ta saki jikinta ba, zuciyarta sai kai da komo take yi. Don har ga ALLAH tana jin wani abin da ta kasa gano mene ne game da wannan d’an aikin nasu, ita dai ta san tana son ganin shi da sauraron muryar shi. Uwa uba k’wayar idanuwan shi da ko tuno yadda yake kallonta ta yi sai ta ji tsikarta ta tashi.

‘Shin me hakan yake nufi wai?’

Ta tambayi kanta yafi shurin masaki, saboda ita dai ta san ba son shi take yi ba, to amma me ya sa fatan auren da Ummin shi da Kakalensa suka yi musu ta ji shi har cikin b’argon jikinta. Saboda mugun jin dad’in fatan da suka yi mata akan auren ta da shi, ‘shin me hakan yake nufi.’

***

Da marece sakaliya Munara tana kwance tana waya da honey’nta Munawwa ta shigo d’akin ta sami wuri ta zauna, da ta ga dba ta da niyyar k’are wayar ne ta ce da ita,

“Magana na zo mu yi ni da ke fa.”

Munara ta kalle ta tare da maka mata wata uwar harara ta ci gaba da wayarta, Munawwa ta yi saurin zuwa wurinta za ta fisge wayar. Saboda jin zafin sauraron hirar da suke yi, Munara ta tashi zaune tana kallon fuskar Munawwa yadda take huci sannan ta ce,

“Honey two minutes”

Sai da ya ba ta dama sannan ta kashe wayar ta kalle ta ranta a haɗe ta ce,

“Sannu Uwata, to ina jin ki, idan kuma tsugudidin ne ya motsa to fad’i meke tafe da ke…?”

Kafin ta kai k’arshen maganar sai kiran Basarake ya sake shigowa ga wayar Munawwara, ta kai dubanta ga screen d’in wayar ta ga sunan ALIYU b’aro b’aro ya fito. Ta yi saurin danne wayar da niyyar ta datse kiran, sai ga shi ta yi kuskure ta latsa receiving kiran. Sannan tayi cooling temper d’inta ta zauna idanunta akan fuskar Munara ta fara magana tana cewa,

“Magana ce nike son mu yi a kan sabon mai aikinmu, wanda ke kin sani soyayyar da yake yi miki ce ta sa yake zama a gidan nan. Ki daure ki ba shi dama saboda walkahiI yana tsananin k’aunarki tsakanin shi da ALLAH, ga shi iyayen shi sun matsa masa a kan yayi aure. Tun da shi wannan HAIDAR d’in ya kasa zuwa gidan nan, to me zai hana ki amince wa wanda ya sadaukar da lokacinsa a kanki? Wanda ya ajiye komai ya dawo gidanku, sannan ya zauna a k’ark’ashin ikonki kina bautar da shi son ranki, kuma duk ya ji ya gani saboda soyayyarki. Don Allah ki daure ki ba shi dama ko ya ya ne, saboda mai son ka har abada ba zai zo d’aya da mak’iyinka ba. Don ba ki san inda rana za ta fad’uwa ba, watak’ila ma shi ne mijin amman kike ta faman wulak’anta sh…”

Tassssss! Munawwa ta ji saukar mari a kan fuskarta, d’aga idon da za ta yi sai ga Munara tsaye gabanta tana huci. Cikin tsananin b’acin rai ta ce da ita

“Yanzu Munara ni kika mara?”

Munara ta nuna ta da d’an yatsa ta ce,
“Ladar b’ata mini lokacin da kika yi ne, sannan kika sa na tsaya sauraron wad’annan banzayen maganganu naki marasa tushe balle makama. Wallahi kin ci sa’a ma da ban had’a miki da uban duka ba. To bari ki ji, ki je ki fad’a masa ba na son shi, mai son shi ba na k’aunarsa duniya da lahira. Kuma ni Munara ba zan tab’a son shi ba har abada, ki je na bar miki shi tun da kina son shi sai ki aure shi ai. Daman can da ke ya fi dacewa, ga shi komai namu iri d’aya ni da ke, sai ki ba shi farin cikin da ni na kasa ba shi, sannan ya daina zama k’ark’ashina ya dawo naki daga yau. Zancen ban san inda rana take fad’uwa ba, na daɗe da sani, don ita ranar za ta fad’i a kanki sai ki je ki aure shi. Amma ni kam ba zan tab’a auren matsiyacin da bai aje ba bai bai wa wani ajiya ba. Ko a kyawun halittar ma babu abin kai gida, ga shi kuturu ga bak’ar fuska. ke wallahi uwar da ta haife shi ma ALLAH ya tsine mata, tun da har ta yi sanadin zuwan shi duniya ta kawo mana mugun iri a doron k’asa….”

Basarake ya YI saurin katse wayar sannan ya danna Recording d’in maganar da ta yi. Da hanzari ya rintse idon shi tare da dafe kan shi, idanuwan shi…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Bakon Yanayi 7Bakon Yanayi 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×