Basarake ya yi saurin katse wayar sannan ya danna Recording d'in maganar da ta yi. Da hanzari ya rintse idon shi tare da dafe kan shi, idanuwan shi suka yi masa jawur a cikin k'ank'anin lokaci, saboda tsananin b'acin rai.
*****
Mummy da ke k'ok'arin shigowa d'akin, wannan maganar ta Munara ta shiga kunnuwanta, a zafafe Munara ta ji saukar mari akan fuskarta. Zumbur ta juya, idanuwanta suka had'u da na Mummy, zarar ido ta dinga yi saboda yanayin da ta ga fuskar Mummyn yasa ta sha jinin jikinta. Domin zuciyarta ta tabbatar. . .