Inspector Sani jami’in dan sanda ne mai bincike akan manyan laifuka wanda duk sarkakiyar da yake cikin case indai yazo hannunsa to yazo karshe.
Zaune yake a gidansa yana nazarin wani case da ya daure masa kai wanda ya tanadi duk wasu hujjoji da yake ganin sun isa ace yakama mai laifin amma kuma hakan ya gagare.
Kofa yaji an kwankwasa ya dago kai ya ce shigo, abokin aikinsa ne wato kofur Abba ya shigo ya gaishe shi irin gaisuwa tasu ta yan sanda. Sanan ya samu guri ya zauna suka fara magana kamar haka.
Inspector sani “Duk da cewa hujjoji sun nuna wannan matar ce ta aikata wannan kisan amma zuciyata ta kasa yadda cewa itace ta aikata.”
Kofur Abba Haba yallabai munsamu warin dan kunnen makashiyar sannan munsamu gashin ta a hannun wanda aka kashe kuma binciken likitoci ya nuna gashinta ne sannan ga zanen hannunta a jikin wukar da akayi kisan.”
“Ta yiwu duk abinda kuke zaton kun samu din ba samu kukayi ba baku akayi”
Cikin mamaki suka juyo da dubansu izuwa ga mai maganar yayinda shikima ko juyowa bayyiba ya kallesu yacigaba da abinda ya keyi.
Muneef ne da ga Inspector Sani wanda baida akinda ya wuce karance karancen littafi musamman ma littafan da suka shafi shari,a da kuma aikata laifuka yanzun ma dai abinda yakeyi kenan dan da suka juyo rike suka ganshi da littafi yana aikin karatu.
Muneef yaro ne da baiwuce shekara goma sha biyar ba ya kasance yanada kaifin basira ga iya tsara magana ga dabaru iri iri wanda yawanci ya koyesu ne acikin irin littafan da yake karantawa.
Inspector sani ya kalli muneef sannan yace masa me kake nufi da an bamu ne ba mun samu ba?
Muneef ya taso daga inda yake zaune sannan ya fara bayani kamar haka,
“Na tashi jiya ina neman littafinda zan Karanta ban samu ba kasancewar na karance duk littatafaina halan yaaa nazo ina neman littafi adakinka ban samu ba dan suma duk na karance su shine naga file din wannan case din nakuma dauka na karanta.
a nawa fahimtar duk wannan abunuwa da kuka samu an ajiyesu ne dan ku samesu sannan ku gudanar da bincike akansu ku kama wannan matar da kuka kama yayinda shikuma asalin makashin zai zama ya wanke kansa.
kunyi duba akan kowacce makama da aka baku amma kuma akwai asalin makamar da yakamata ace kun duba wanda shine baku duba ba.
kasancewar ranar da akayi wannan kisan anyi ruwa ansamu shatin takalmin makashin wanda takalmi ne sau ciki kuma girmansa yakai number arba,in da biyar sannan kuma idan akayi duba da nitsewar takalmin acikin kasa nauyin mai sanye da takalmin zaikai kg 50 zuwa sama sannan kasancewar sukan da akayiwa wanda aka kashe ya kasance ta barin dama ina kyautata zaton makashin bahago ne sannan makashin ku ba mace bace namiji ne.”
A lokacin da Muneef ya zo nan a zancensa sai su Inspector Sani suka cika da mamaki ta yadda karamin yaro kamar Muneef zai iya gano abinda shi bai gano ba dukda kwarewarsa a fannin bincike.
Bayan shudewar wasu yan dakiku yana nazari sai Inspector Sani ya maida kallonsa zuwa ga Kofur Abba yana mai cewa indai kuwa hakane tabbas makashin yanada mutukar kusanci da wanda ake zargi ta yadda ya samu wadannan abuwawa har ya ajiyesu a inda muka samu sannan zamuyi bincike ne a sirrince kuma sai munyi shi da kulawa duk yan uwanta da makusantanta ina so akawomin bayanansu da aka dauka dan makashin zai iya kasancewa kowa.
Bayan wani dan lokaci kofur abba ya hado duk bayanan yan uwanta ya kawowa Inspector Abba ya karba ya fara dubawa ko zai samu wata makama a cikin bayanan da suka bayar.
Baisamu wata makama ba wanda hakan ya tilastashi komawa gurinsu domin ya sake yi musu tambayoyi domin yanaji a jikinsa cewa makashin zai iya kasancewa a cikin yan uwan wacce ake zargi da aikata kisan daya bayan daya ya ringa binsu yana musu tambayoyi har akazo kan mijinta. Inspector Sani ya tambaye shi, “Yaya sunan ka kuma mane ne alakarka da wacce ake zargi da aikata wannan kisan?” Saikuwa ya bashi amsa da cewa, “Sunana Ibrahim kuma ni mijinta ne.” Inspector Sani ya kara tambayarsa ya ce, “Shin akwai wani ko wata abokin fadan matarka a cikin danginta da yan uwa?”
Ibrahim ya yi ajiyar zuciya sannan ya fara da cewa, “Gaskiya a iya sanina da ita bantaba ganin abokin fadanta ba koda kuwa a cikin jama’ar gari ballantana cikin yan uwa. Sai dai akwai bayananda nake so nazo na baka dama wanda nake ganin zasu taimaka a cikin wannan binciken akwai wani tsohon saurayinta wanda da shi suke soyayya kafin na hadu da ita. Bayan kuma Allah ya yi ba shine mijintaba ya yi mana barazanar koda munyi aure zai kuntata mana ta yadda sai munyi da nasani to agaskiya a baya ban dau maganarsa da muhimmanci ba saboda na dauka kawai zafin kishine yasa ya fadi hakan amma bayan faruwar wannan lamarin nima na fara nawa binciken na sirri kuma na samu labarin a satin da abin zai faru anganshi yana yawan bibiyar ta kuma wani makoci na ma ya tabbatarmin da cewa har gidana ya ga shigarsa.
Yallabai duk da cewa ranarda akayi kisan bana gari amma na tabbata bayadda za’ayi matata tafita karfe uku na dare ta aikata kisan kai ita kadai.” Koda ya zo daidai nan azancensa sai Inspector Sani y ace da shi, “Yaya sunansa kuma a ina yake zaune?”
Yana fada masa kuwa ya tura da jami’ai suka taho masa da shi bayan anzo dashi sai Inspector Sani ya fara masa tambayoyi kamar haka, “Yaya sunanka?” Nan take ya amsa masa da cewa, “Sunana Aliyu.” Ya ce masa, “Mene ne alakarka da Halima Abubakar Aliyu?” Ya nuna alamun razana sannan ya ce “Yallabai tsohuwar budurwata ce.” “Kasan da cewa ana tuhumarta da aikata kisan kai.” “Eh nasani.” ya fada a tsorace. “To mene ne yake hadaka da ita bayan kasan ta yi aure?” “Yallabai tunda ta yi aure bankara koda kiranta ba a waya.”
Inspector Sani ya kalleshi cikin fushi ya ce, “Karka kawo mana maganar banza anan kadauka yan sanda basusan abinda sukeyi ba ne ko asatinda akai kisan anganka kana yawan sintiri ta inda take kuma akwai bayanin da ma muka samu kan cewa ko aranar da akayi kisan anganka kazo har gidan da take aure alhali kuma me gidanta bayanan saboda haka katsaya kaimana bayani kokuma inada hanyoyinda zanbi na tatsi bayanai daga bakinka.”
Koda yaji haka sai ya tsorata yafara da cewa, “Yallabai tunda Halima ta yi aure bansake jin koda labarinta ba sai asatinda abin zai faru tafara yimin text tana cewa tana cikin damuwa tana bukatar taimako tun bana kulawa har dai na fara jin tausayinta na kuma fara bibiyar naga abinda ke faruwa da abin ya tsananta sai na yanke shawarar naje gidan kai tsaye amma abin mamaki da naje bataji dadin ma ganina ba hasalima korata tayi kamar ba itace me neman taimakona ba.” Nan da nan inspector sani yasa aka kulle shi dan sam bai yadda da bayanansa ba ya dawo gida ya kunna recording din bayanan da yadauka na yan uwanta yana kara nazartarsu.
Muneef yana zaune a gefe yana aikinsa na karatun littafi sai kawai ya ajiye ya fara sauraron tambayoyinda ake yi da kuma amsoshinda ake bayarwa har dai akazo kan bayanan da mijinta wato Ibrahim ya bayar yana cikin saurara har akazo gurinda yake cewa,
“Yallabai duk da cewa ranar da akayi kisan bana gari amma na tabbata bayadda za ayi matata ta fita karfe uku na dare ta aikata kisan kai ita kadai.” Sai kawai nan take Muneef yace da babansa ya akayi yasan daidai lokacinda akayi kisan bayan ko a bayanin yan sanda babu nan take hankalin Inspector Sani ya dawo gurin baitsaya ba shi amsa ba ya tashi ya fice daga gidan nan ya kira Kofur Abba a waya yace masa akawomin mijin Halima office kafin na karaso aikuwa hakan akayi yana zuwa ya isk eshi a zaune.
Ibrahim ya ce, “Yallabai ansamu wani abu ne a dangane da case din matata?” Bai kulashi sai takarda da biro ya mika masa ya ce, “Rubuta sunanka a nan.” Bai yi musu ba ya karba ya rubuta. Sannan Inspector Sani ya kalleshi ransa a bace ya ce masa me yasa ka kasheta ya bude baki zai yi magana ya da katar da shi yace nasan cewa kaine ka yi amfani da wayar matarka kake turawa tsohon saurayinta da sakonnin neman taimako kan cewa tana cikin matsala saboda kawai a ganshi yana bibiyar matarka dan ya zama abin zargi kuma a gurin da akayi kisan an samu shatin takalmi wanda ya yi daidai da takalminka da kabari a waje sannan kuma muna zargin makashin bahago ne shiyasa na nemi ka rubuta sunanka anan kuma hakan ya tabbatar min da cewa kai din bahago ne sannan babu wanda yasan cewa karfe uku ne na dare a kayi kisan amma sai gashi kai kafada saboda haka karka batamin lokaci kawai amsarda nake so naji shine meyasa ka kasheta kuma kayi ka karkatarda zargi kan matarka?”
Nan take ya fara bayani da cewa, “Yallabai matata tana kikirar wata software wacce tun kafin a kammalata manyan kamfanoni sun nuna suna bukatarta kuma nima dalilin hakan na aureta badan ina sonta ba saboda ina so nazama sananne a duniya inaso nayi kudi nayi iya bakin kokarina nasa ta maida komai da sunana ina jiran ranar kaddamarwa a kaddamar da software da sunana bukatata ta biya nabarta na koma wata kasar na fara sabuwar rayuwa da budurwata a lokacin da abin ya faru nagayamata bana gari amma ina gidan budurwarnan tawa shine adaren da karfe uku sabani ya shiga tsakaninmu wanda ta yi yunkurin tonamin asiri agurin matata nikuma na kasheta sannan na ajiye duk abinda nake ganin zaisa azargi matata ta yadda da an kamata shikenan na jefi tsuntsu biyu da dutse daya zan kaddamarda software na fara sabuwar rayuwa,”
Nantake aka kamashi aka mika shi kotu aka yanke masa hukunci sannan kotu ta wanke Halima daga laifin da ake zarginta da shi.
Inspector Sani ya dawo gida cikin farin cikin kawo karshen case din da ya mutukar wahalarda shi. un kafin ya zauna sai jin kira yayi a waya ana nemansa a office cikin gaggawa yana zuwa aka mika masa wani file aka ce ana bukatar ka kawo karshen wannan case da gaggawa dan abin ya shafi gwamnati kuma kaine ka dai bana kokwanto kan cewa zaka iya kuma anaso ka aiwatar da shi cikin sirri.
Fatan alheri.
Godiya nake oga
sahunku muke bi