Bayan mun ɗan yi 'yar doguwar tafiya sai muka iso bakin wannan doguwar hasumiya da na hango tun farkon zuwana sashen ƙabilar maƙera da ke birnin Sahara. Kai tsaye Shamadara ta yi mana jogora muka wuce ciki. A wani babban gida muka tsinci kanmu mai sassa da yawa, ga kuma ɗakuna nan birjik iya ganinka. Gida ne amma ya kai girman unguwa, ga kayan alatu nan iri-iri, babu wanda zai ce a tsakiyar sahara za a iya samun gida mai girma da kyawu irin na wannan. A tsakiyar gidan kuma wata babbar rumfa ce mai siffar kan zaki. . .
I’M. so proud of being a member of this group.
That’s really nice. Thank you very much.