Skip to content
Part 15 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

Bayan mun ɗan yi ‘yar doguwar tafiya sai muka iso bakin wannan doguwar hasumiya da na hango tun farkon zuwana sashen ƙabilar maƙera da ke birnin Sahara. Kai tsaye Shamadara ta yi mana jogora muka wuce ciki. A wani babban gida muka tsinci kanmu mai sassa da yawa, ga kuma ɗakuna nan birjik iya ganinka. Gida ne amma ya kai girman unguwa, ga kayan alatu nan iri-iri, babu wanda zai ce a tsakiyar sahara za a iya samun gida mai girma da kyawu irin na wannan. A tsakiyar gidan kuma wata babbar rumfa ce mai siffar kan zaki wadda aka yi mata rufi da wani irin kwano wanda ban taɓa ganin irin shi ba a kyawu. Ga kuma wasu irin kujeru masu tsananin kyau da yawa duk an jera su a kusa da wani ƙaton teburi na farin ƙarfe. Ga kujeru nan masu yawa sun zagaye teburin. Daga nan sai aka nuna wa kowa ɗakinsa domin ya shiga ya kimtsa, ya rage saura ni kaɗai da Shamadara a tsaye. Hannuwana na ga ta ta ja kamar wani jariri har sai da muka je ƙofar wani babban ɗaki sannan ta dafa kafaɗuna ta ce,

“Ya kai ɗana, ka yi sani cewa duk da irin fushi da na yi da mahaifinka, hakan bai taɓa sa ni na fidda rai da cewa watarana zai dawo ba. Ko lokacin da Sanafaratu ta faɗa min cewa ya rasu, a can ƙasan raina ban karaya ba, ban kuma fidda rai ba. Wannan dalili ne ya sa kullum sai na sa an share ɗakinshi an shirya kamar yadda aka saba. Ina ganin cewa kai ka fi cancanta da ka mallake shi tunda yanzu ba ya raye.”

Har na buɗe baki zan yi musu sai na ga ta sa hannu ɗaya ta tura ƙofar, nan take ta buɗe sannan ta yi min alamar in shiga da ɗayan hannun nata. Cikin sanyin jiki na yi Bismillah sannan na shiga da ƙafar dama. Ƙamshin da ya doki hancina ne ya fara tabbatar min da cewa lallai ɗakin mahaifina ne, domin ƙamshin turaren shi ne, kuma ban taɓa jin irin ƙamshin shi a jikin kowa ba face shi. Ɗakin a tsafatace yake kamar yadda ta faɗa, ƙasan ɗakin kuma a lulluɓe yake da irin dardumar da na gani a wancan ɗakin da na farka na ganni a ciki tun da fari. Sai dai ita wannan dardumar babu zanen komai a jikin ta, kuma kalar ta kore ne saɓanin wancan da yake mai ruwan ƙasa. Sai a wannan lokaci ne na ankara da cewa kusan komai da ke ɗakin kalar shi kore ne. Ga takardu nan tuli a shirye kamar za su yi magana, ga kuma wani ɗan ƙaramin teburi da kujera a tsakiyar ɗakin. Kujerar irin mai lilon nan ce da tsofaffi ke son zama a kai wani lokaci. Daga bangon hagu na ɗakin kuma wata ƙofa ce da aka yi mata baƙin fenti. A bangon dama na ɗakin kuma wata ƙofar ce ita ma, sai dai ita farin fenti ne a jikinta. Kai tsaye na nufi mai farin fentin na buɗe da Bismillah.

 A wata sabuwar duniyar na tsinci kaina. Domin kusan komai da ke cikin ɗakin fari ne, tun daga dardumar da ke ƙasa da bangon ɗakin har zuwa mayafin da aka shimfiɗa akan matsakaicin gadon da ke ɗakin. Babu wasu abubuwa sosai a ɗakin, daga wannan gado sai wani ɗan kabad wanda da alamu kayan sawa ake ajiyewa a ciki sai wani ɗan ƙaramin teburi wanda ke ɗauke da man shafawa da turaruka sai kuma darduma da carbi a gefe. Nan fa na ci gaba da kallon wannan ɗaki ina jin kusancin da ke tsakanina da su na ƙaruwa da duk tsawon lokacin da nake ci gaba da kallon su. Gaba ɗaya kallon wannan ɗaki da kuma irin kusancin da nake ji da su ya sa hankalina ya tafi wani waje can daban. Domin ji nake kamar mahaifina yana kusa da ni ne a wannan lokacin. Hankalina ya yi nisa sosai cikin tunani har na ma manta da inda nake. 

Kamar daga sama sai na ji an ce, 

“Ɗakin ya yi ko?” 

Firgigit na waiga a tsorace, amma sai na ga ashe Fa’iza ce tsaye a bakin ƙofar tana kallona cike da murmushi. Wata ajiyar zuciya na saki tare da dafe ƙirjina. Ita kuwa me za ta yi in ba dariya ba. Can kuma sai ta tsagaita da dariyar sannan ta dube ni ta ce, 

“Babban Yaya ba ƙaramin burge ni ka yi ba ɗazu da ka yi wa mutum goma sha biyun nan dukan tsiya. Ba don kana wari ba da sai na rungume ka saboda farinciki.”

Cikin alamun rashin fahimta na kalle ta sannan na ce, 

“Wari kuma?” 

Dafa goshinta ta yi cikin alamun gajiya da tambayoyina sannan ta nuna ni da yatsanta tana mai zagaya dukkan jikina da shi. Ko da na kai dubana na kalli jikina da kyau, sai na ga duk na ɓaci da wannan abu da aka yi ta watsa min ɗazu. Sam na manta ma da shi a jikina saboda hankalina yana tare da abubuwan da na gani a cikin wannan ɗaki. Cikin sanyin jiki na shinshina hannuna, ai kuwa wani irin wari na ji, ba shiri na kau da kaina gefe. Fa’iza kuwa sai ta sake fashewa da dariya. Bayan ta yi mai isarta sai ta ce da ni, 

“Ɗaki mai baƙar ƙofar nan shi ne banɗaki, akwai komai da za ka buƙata a ciki. Ka shiga ka yi wanka ka sake kaya, in ka gama ka fito akwai zama da za a yi.” 

Har na buɗe baki da nufin amsa mata amma sai na ga ta wuce. Ganin hakan ya sa na koma da baya na buɗe wannan ɗaki mai baƙar ƙofa. Kamar yadda ta faɗa, komai da mutum ke buƙata akwai a cikin banɗakin. Babban abin da ya fi ba ni mamaki shi ne, komai da ke cikin banɗakin sak yake da irin ainahin nawa na gida. Man wanke baki ne kawai ya bambanta. Ga kuma fanfo nan mai fitar da ruwa wanda na kasa fahimtar yadda aka yi har hakan ta faru a cikin tsakiyar sahara. 

Wanka na fara yi tukunna, sannan na yi alwala na ɗaura tawul a jikina sannan na nufin wannan ɗaki mai farar ƙofa. Buɗe wannan kabad na yi domin in saka wasu kayan. Kaya ne na gani masu yawan gaske, an jera su layi-layi. Layin manyan kaya daban, layin ƙanana daban, har da su suit da wasu ma waɗanda ban san sunayensu ba. Na dai zaɓi wasu fararen kaya masu shigen ɗinkin Pakistan na saka. Bisa mamaki, sai na ji sun yi min daidai kamar da ma can nawa ne. Daga nan sai na yi sallar La’asar. Bayan na idar da sallar ne sai kuma na duƙufa wajen yin addu’o’i da neman taimakon Allah akan ya shiga cikin lamarina. Domin a daidai wannan lokaci, na yi wa kaina alƙawarin daina ɗaukar abubuwan duk da suka faru da wasa, abin ya fi ƙarfin mafarki ko wasa. Abubuwan nan da gaske suke faruwa, ya zama dole in tunkare su da gaske nima. Da wannan tunani a raina na fito daga ɗakin na nufi inda wannan ƙatuwar rumfa take. Mutane na gani da yawa a rumfar. Shamadara, Imran, Sadiya, Fa’iza da Sanafaratu duk suna zaune akan wani. Sai kuma wasu mata su uku da ban san ko su waye ba. Amma duk da yawan nasu ko rabin kujerun da ke zagaye da teburin ba su cika ba. 

Bayan na yi musu sallama mun kuma gaisa, sai Shamadara ta umurce ni da in zauna a wata kujera da ke ƙarshen teburin, da alama akanta mahaifina yake zama. Domin ita kaɗai ce ke kallon teburin gaba ɗaya. Ba tare da shakkar komai ba na zauna tare da yin bismillah. 

Kowa da ke wurin sai haba-haba yake yi da ni face wata mace guda ɗaya wadda tun da na zo wurin ta ɗaure fuska tare da ƙura min ido kawai ba tare da ta ce komai ba, ko da na gaishe su ma ba ta amsa ba. Can sai na ga an kawo mana abinci kala-kala. Kwanukan abinci ga su nan birjik kamar ana liyafa a gidan sarauta. Wasu ma ban ko taɓa ganin irinsu ba. Mamana shamadara ta ce in yi mana addu’a kafin mu fara cin abincin. Ba tare da shakkar komai ba na karanta Fatiha da Ayatul Kursiyyu tare da roƙon Allah ya sa mana albarka a cikin wannan abinci da za mu ci kuma ya tsare mu daga muguwar yunwa. Da alama sun ji daɗin wannan addu’a da na yi, don na ga sai murmushi suke yi. Daga nan sai muka fara cin abincin. Abincin mutanen Birnin Sahara ba dai daɗi ba, sun ƙware matuƙa wajen iya sarrafa sinadaran girki. 

Tun da muka fara cin abincin babu wanda ya ce ƙala.Bayan mun kammala cin abincin kowa ya natsa, sai Mamana Shamadara ta fara magana cike da da farinciki da annushuwa kamar haka, 

“Da fari dai, ina miƙa godiya ta ga ababen bauta da suka dawo min da ɗana gida, kuma su ka ba ni damar fahimtarsa kafin in halaka shi… Ko kuma shi ya halaka ni…” 

Ta faɗa tare da ƙyafta min ido. Kowa da ke wurin ya fashe da dariya face wannan mace wadda ta ɗaure fuska. Murmushi kawai na yi ba tare da na ce komai ba. Hakan ya sa Shamadara ta ci gaba da magana da cewa, 

“Sannan ina mai ƙara gode musu bisa tseratar da rayuwata da suka yi a yau sakamakon harin da aka kawo mana. Godiya ta tabbata ga ababen bauta.”

“Godiya ta tabbata ga ababen bauta!”

Su Sanafaratu suka amsa, har kuwa da ita wannan baƙuwar mace mai ɗaure fuska. Ni dai ban ce komai ba tukunna. Daga nan sai Shamadara ta ci gaba da cewa, 

“Haidar, barka da zuwa cikin ahalinka na Birnin Sahara. Kamar yadda ka sani, sunana Shamadara kuma ni ce matar mahaifinka ta farko. Wannan da ka ke gani ita ce ɗiyata ta farko, sunanta Ashalle. Wannan kuwa ita ce ɗiyata ta biyu, sunanta Shalibai. Na san ka riga ka haɗu da ɗiyata ta uku, Sanafaratu. Wannan sunanta Baruma, ita ce ɗiyata ta huɗu, sai kuma ‘yar autata, wato Fa’iza. Muna yi maka barka da zuwa.”

Kamar haɗin baki sai na ji sun ce da ni,

“Barka da zuwa Birnin Sahara!”

Tun da ta fara maganar take nuna min kowacce daga cikinsu. Dukkansu murmushi suke yi min, amma banda wannan da aka kira da suna Ashalle wadda ita ba ta yi min barka da zuwa ba. Daga nan kuma sai ta ci gaba da magana da cewa, 

“Ya kai ɗana, ka sani cewa gaba ɗaya ‘yan’uwan mahaifinka sun mutu babu wanda ya yi saura sai shi kaɗai. Ka yi haƙuri babu wani wanda yake raye da zan iya haɗaka da shi.”

Duk da na san cewa ikon Allah ya fi da haka, na yi matuƙar mamakin jin cewa babu mutum ko ɗaya da ya rage a raye daga cikin dangin mahaifina. Mamakin ne ma ya sa na tambaye ta da cewa, 

“Mene ne sanadin mutuwarsu?” 

Shamadara ta yi ajiyar zuciya sannan ta ba ni amsa da cewa, 

“Tun daga lokacin da mahaifinka ya zama sarki ahalinsa suka fara shiga damuwa. Wannan kuwa ya faru ne sakamakon irin barazanar da ahalin su Dargazu suke yi musu. Lamarin ya ƙara ta’azzara ne yayin da muka yi aure da shi. Ni ƙanwa ce a wurin boka Wajagi, kuma ba a son ranshi na auri mahaifinka ba. Wannan dalili ne ya sa dangina suka tsane ni, har ta kai ga sun ce min in har ban rabu da mahaifinka ba sai sun tsine min.”

Ajiyar zuciya ta sauke cike da damuwa sannan ta ci gaba da cewa, 

“Ni da mahaifinka muna yi wa juna so na haƙiƙa, don haka na zaɓe shi akan ahalina. Tun daga wannan lokaci ne sai ahalina suka raba gari da ni, kuma suka haɗa kai da ahalin su Dargazu wurin ganin sun kawar da ahalin su mahaifinka. To sai dai ba abu bane mai sauƙi, domin na gaji tsafi kamar yadda mahaifinka shi ma ya gaji jarumta. Don haka sai ya zamana sun kasa cin galaba akanmu, musamman tun da sarauta na hannunmu ne. Sai dai duk da haka ba mu tsira ba, lokaci zuwa lokaci akan turo makasa su kawo mana hari, wani lokaci su gudu, wani lokaci kuma a kama su, sai dai kafin a samu damar tuhumarsu suke kashe kansu. Don haka ba mu da tabbacin daga ina suke zuwa ko kuma wanda ya aiko su, amma ni da mahaifinka mun alaƙanta hakan ga ahalin su Dargazu da kuma ahalinsa. Ƙiyayyar da ahalina ke min saboda ƙin rabuwa da mahaifinka ta kai ga ni kaina neman halaka ni suke yi a koyaushe. Ba ni da damar kai musu ziyara saboda tsoron hakan. Ina ji ina gani mahaifiyata ta kwanta ciwon ajali har ta mutu ba tare da na je mun gana ba ko sau ɗaya. Kullum Wajagi cikin neman damar halakani yake yi. Wannan ne dalilin da ya sa ka ji ɗazu na ce maka ni waɗannan tsuntsaye suka kawo wa hari ba kai ba. A irin harin da ake kawo mana ne aka dinga yi mana ɗauki ɗai-ɗai, a haka aka kashe dukkan jama’ar wannan ahali namu 

Babu yadda kakarka ba ta yi da mahaifinka ba akan ya rabu da ni ko kuma ya mayar musu da martani. Amma sai ya ce ko da ya yi hakan babu abinda zai sauya face zubar da jini na babu gaira babu dalili. Wannan shi ne sanadin mutuwarsu, ko in ce ni ce sanadin mutuwarsu. A bisa wannan dalili ne kuma nake ba ka haƙuri a karo na biyu, domin nima ba ni da ikon kai ka zuwa ga nawa ahalin domin ku gana. Mu ɗin nan da ka gani, mu kaɗai ne ahalin juna a yanzu.”

Ta ƙarasa maganar yayin da hawaye suka fara zubowa daga idanuwanta, rauni da baƙinciki cike da muryaryata. Ni kuwa a wannan lokaci mamaki da damuwa ne suka matse min zuciyata. Duk irin tashin hankalin da nake ciki bai kai irin wanda take ciki ba, ko kama ƙafafuwanta ma bai yi ba. Na kasa fahimtar dalilin da ya sa bayan duk wannan irin soyayya da mahaifina ke yi mata ya tafi ya barta. Cikin sanyin murya na ce da ita, 

“Babu buƙatar sai kin ba ni haƙuri Mama. Ba laifinki ba ne. Komai na duniyar nan da ki ka gani yana faruwa ne a bisa yadda Allah ya tsara zai faru. Idan har wannan ita ce ƙaddararsu babu wanda ya isa ya sauya musu. Kuma nima ina mai ba ki haƙuri a bisa irin halin da ki ka tsinci kanki a ciki saboda soyayyar mahaifina, ban san dalilin da ya sa ya bar ki ba ya tafi, ba zan iya goyon bayan ɗayanku in bar ɗayan ba, amma zan iya baki haƙuri idan har hakan zai samar miki da sauƙi ko yaya yake a cikin zuciyarki.”

 Ko da na gama wannan jawabi nawa, sai na ga ta share hawayenta sannan ta ce da ni a sanyaye, 

“Na gode Haidar, na gode sosai. Mahaifinta ya raine ka yadda ya kamata. Ina alfahari da shi bisa hakan.” 

“Kenan hakan na nufin kin yafe mishi laifin da ya yi miki?” 

Na tambayeta a sanyaye. 

Murmushi ta yi sannan ta kalle ni ta ce, 

“Duk irin fushin da na yi da shi, ƙaunar da nake mishi ba ta taɓa canzawa ba. Kuma a can ƙarƙashin zuciyata ina jin cewa lallai duk dalilin da zai sa ya tafi ya bar ni ba ƙaramin dalili ba ne. Na dai kasa yarda da cewa ya yi hakan ne. Amma zuwanka yanzu ya tabbatar min da cewa ba zai rasa ƙwaƙƙwaran dalilin da ya sa shi aikata hakan ba. Don haka na yafe mishi dukkan wani laifi da ya yi min. After all, it is not good to have a grude against a dead man.”

Ta ƙarasa maganar cikin harshen Turanci. Mamaki da farinciki ne suka lulluɓe ni a wannan lokaci. Godiya na yi mata sosai sannan na ce, 

“Mama, in babu damu ki ɗan yi min bayani game da waɗannan tsuntsaye masu siffar macizai da muka fafata da su ɗazu. Na kasa fahimtar yadda aka yi tsuntsaye… Ko in ce macizai masu fukafukai irin waɗannan suka wanzu a duniya. Ko a labari ban taɓa jin labarin halittu irinsu ba.”

“Uraei kenan, jam’insu kuma Uraeus. Halittu ne na tsafi. Matsafa kan iya kiransu daga bigiren tsafi domin su yi aiki guda ɗaya ne kawai. Kuma ba na ko tantamar cewa Wajagi ne ya aiko su domin su halaka ni tare da fatan kai ma za su halakaka. Ka ga ya jefi tsuntsaye biyu da dutse ɗaya kenan.”

Ta ba ni amsa. 

Sanafaratu, wacce kamar sauran tun ɗazu ba ta ce komai ba sai ta nisa tare da cewa, 

“Tabbas shi ne, domin lokacin da ku ke fafatawa tare da su ni kuma na ruga izuwa sashen da na ga sun fito. A can na ganshi tare da wasu jama’arsa mutum ashirin suna gadinsa, yayin da shi kuma yake sarrafa su da sandar tsafinsa. Nan far musu da yaƙi har sai da na ga bsyansu tukunna, shi kuma ya tsere a ta hanyar yin layar zana.”

Wannan bayani nata ya ba ni mamaki matuƙa, su kansu su Imran mamaki ne sosai a fuskokinsu. Amma su su Baruma kuwa ko ajikinsu, kamar irin hakan ya saba faruwa a kowace rana. Bayan mun ɗauki ɗan lokaci ba tare da wani ya ce komai ba, sai can na dubi Shamadara na ce, 

“Ya ke Mamana, bayan na saurari bayanin da Sanafaratu ta yi min a hanyar mu ta zuwa nan, da kuma bayanin da ki ka min yanzu. Na fahimci cewa ba wai ƙabilar maƙera ba ce kaɗai ke cikin tashin hankali, alamu na nuna cewa Birnin Sahara gaba ɗaya yana cikin wani irin yanayi da in ba ƙwaƙƙwaran mataki aka ɗauka ba, matsaloli da dama za su iya faruwa. Ban san ya za a ɓullo wa lamarin ba, amma a shirye nake da in ba da tawa gudunmawar, don haka ina buƙatar ku fahimtar da ni dukkan abubuwan da ban sani ba da kuma shirinku domin in san irin gudunmawar da ni kuma zan iya bayarwa.”

Ko da gama wannan jawabi nawa, sai na ga Shamadara ta yi murmushin jin daɗin kalamaina sannan ta ce, 

“Ya kai ɗana, ina godiya sosai a gareka da ka ɗauki wannan niyya ta taimaka mana ba tare da na roƙeka ba. Wannan hali da ka nuna ya tabbatar min da cewa ka zo ne domin ka yi abinda mu ba za mu iya ba. Amma kafin nan, ya zama wajibi in sanar da kai dokokin ahalin ƙabilar maƙera tukunna.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Birnin Sahara 14Birnin Sahara 16 >>

2 thoughts on “Birnin Sahara 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×