Skip to content
Part 16 of 17 in the Series Birnin Sahara by Haiman Raees

“Dokoki kuma?”

Na tambaya cike da mamaki. Da alama mutanen Birnin Sahara ba sa gajiya da zaƙule-zaƙule. 

“Ƙabilar maƙera gaba ɗayanta ta dogara ne akan waɗannan dokoki da zan sanar da kai. Abin da ake so ga kowane ɗan ƙabilar maƙera shi ne ya yi ƙoƙarin ganin ya kiyaye waɗannan dokoki bakin iyawarsa.” 

Shamadra ce ta yi min wannan bayani. 

Shiru na yi na ɗan wani lokaci ina tunani, kafin daga baya na ce, 

“Shikenan Mama sanar da ni waɗannan dokoki in ji su.”

Har ta buɗe baki da nufin sanar da ni sai na ga Ashalle ta daki teburin ta miƙe a fusace tare da faɗin, 

“Ya isa haka Mama! Bayyanawa baƙo sirrin namu ya isa haka!” 

Mamakin wannan abu da ta yi ne ya sa ni da Sadiya da Imran muka kalli juna sannan muka zuba wa Shamadara idanuwa domin mu ji abinda za ta faɗa. Murmushi ta yi wanda ba shi da alaƙa da farinciki sannan ta ce, 

“‘Yan nan, na riga na karɓe shi a matsayin ɗa, kamar yadda shi ma ya karɓe ni a matsayin uwa, don haka ban ga dalilin da zai sa mu ɓoye mishi komai ba. Musamman idan muna so ya taimaka mana. Ko kuwa so ki ke yi mu yi mishi ƙarya?”

Ashalle ba ta haƙura ba sai ta sake yin magana a fusace da cewa, 

“Ban yarda da shi ba, ta yaya aka yi har ya shigo Birnin Sahara? Me ya sa ta duk inda aka ɓullo masa yake da abin faɗa ko kuma abinda zai yi wanda ya dace da irin abubuwan da ake buƙata a lokacin da da ake buƙata? Lallai dole akwai wani abin da yake ɓoyewa!”

Har Sanafartu ta miƙe tare da buɗe baki da nufin ta ba ta amsa sai na yi mata alama da hannu da ta zauna. Ba tare da musu ba ta koma ta zauna. Ita kuwa Ashalle sai balla min harara take yi kamar za ta rufe ni da duka. A iya rayuwata na yi karo da taƙadiran mutane iri-iri kuma nima na kasance taƙadarin, to amma yanzu abubuwa sun canza, dole ne in bi wasu abubuwan ta wata hanyar da ba wannan ba. Murmushi kawai na yi sannan na dube ta sannan na ce, 

“Ya ke Yayata, kina da damar ƙin yarda da ni bisa ra’ayi ko hujjoji irin naki. Wannan ‘yanci ne da kowa ke da shi. Amma ki tambayi kanki, shin nima kina da tabbacin na yarda da kaina game da irin abubuwan da suka faru daga lokacin da na shigo Birnin Sahara zuwa yanzu? Ko kaɗan ban gama samun nutsuwa da su ba. Ku kanku ban gama fahimtarku ba balle in aminta da ku ɗari-bisa-ɗari. Saboda aminci ko yarda ba abubuwa ba ne da ake iya samun su lokaci guda, hakan na buƙatar fahimta, ita kuma fahimtar tana buƙatar lokaci. Wannan shi ya sa Mama ke min bayanin abubuwan da ya kamata in sani. Kema na san a naki fahimtar abinda ki ke yi kenan. Bambancina da ke kawai shi ne ni na yarda da kaina, kuma fiye da komai na yarda da Allah maɗaukakin sarki da dukkan wata ƙaddara da ya ƙaddaro min. Kuma a shirye nake da in karɓi wannan ƙaddarar a kowane lokaci. Wannan shi ya sa na daina ɗaukar abubuwan a matsayin wasa na koma ɗaukar su a yadda suke. Ina fata ke ma wani ɓangare na zuciyarki zai karɓi al’amarin da ke faruwa a yadda yake ba wai a yadda ki ke tsammanin zai kasance ko ya kamata ya kasance ba.”

Na ɗan dakata domin in ba ta damar fahimtar kalamaina da kyau tukunna. Ba ta ce komai ba sai dai ta koma ta zauna. Ko da ganin haka sai na sake yin murmushi sannan na dubi Shamadara na ce, 

“Mama, duba da cewa ni ne baƙo, bari in fara yi muku bayani game da kaina tukunna kafin ku ci gaba da yi min naku bayanin. Ina ganin hakan zai taimaka mana wajen fahimtar juna.”

Murmushi kawai Shamadara ta yi sannan ta ba ni damar yin bayani. Nan fa na fara yi musu bayanin dukkan rayuwata tun daga lokacin da na yi wayo har zuwa haɗuwata Nadiya da kuma yadda aka yi har na tsinci kaina a Birnin Sahara. Bayan na kammala yi musu bayani ne sai na umurci Sadiya da ta bayyana mana yadda ita kuma ta zo birnin Sahara, domin nima ban sani ba. 

Sadiya, wadda har yanzu ba ta ce komai ba sai ta yi gyaran murya sannan ta fara bayani da cewa, 

“Ni ma dai kusan yadda lamarin ya faru da kai haka ya faru da ni. Na gama cin abinci kenan sai mama ta ce in shiga ɗaki in ɗauko mata kuɗi a cikin jaka za ta aike ni kasuwa. Shiga ta ɗakin kenan kawai sai na ji an kira sunana kamar daga sama. Ina amsawa sai kawai na ji an yi sama da ni. Farkawa kawai na yi na ganni a gaban wani tsohon mutum yana riƙe da wata jar tukunya, ga kuma gunkin baba Hammadi a gabansa yana ambaton sunanka da Baba Hammadi. Kafin in yi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai na ga ya ɗebo wani irin baƙin ruwa daga cikin wannan tukunya ya watso min a jikina. Daga nan ban san me ke faruwa ba sai dai farkawa na yi na ganni ɗaure cikin sarƙa. Daga nan kuma sai aka jawo ni aka taho da ni wannan wuri inda Sarauniya Nadiya ta same ka.”

Shiru kawai na yi ina tunani game da kalaman Sadiya. Yanzu kam na tabbatar da cewa akwai sharrin Aljanu a cikin wannan lamarin. Sai dai maganar da ta faɗa game da wannan tsoho ne ya tsaya min a rai. Kafin kowa ya ce wani abu sai na dubi Sadiya na ce, 

“Sadiya, tsohon da ki ka gani ya yi kama da boka Wajagi?” 

Girgiza kai ta yi sannan ta ce, 

“A’a ba su yi kama ba. Wajagi baƙar fata gare shi, shi kuma wancan tsohon farin fata ne.” 

Nan fa wurin ya ƙara yin shiru. Kowa da irin abinda yake tunani a ranshi. Bayan mun ɗauki tsawon wani ɗan lokaci ba tare da wani ya ce komai ba sai na ce Shamadara ta faɗa min dokokin ƙabilar maƙeran in ji. Bayan ta yi ajiyar zuciya sai ta dube ni ta ce, 

“Ka da ka raina kowa, kuma ka da ka bari kowa ya raina ka.

Ka da ka wulaƙanta kowa, kuma ka da ka bari kowa ya wulaƙantaka.

Ka da ka cutar da kowa, kuma ka da ka bari kowa ya cutar da kai.

Wanda duk ya raina wani, ya wulaƙanta ko ya cutar da wani ba tare da dalili ba, ya zubar da darajar uban da ya haife shi.

Wanda duk ya bari aka raina shi, aka wulaƙanta shi ko aka cutar da shi ba tare da haƙƙi ba, ya zubar da darajar uwar da ta haife shi.” 

Ko da na ji waɗannan dokoki sai na cika da tsananin mamaki. Tabbas waɗannan dokoki cike suke da saƙonni masu zurfin da sai mutum ya natsu da kyau ne zai iya fahimtarsu. Kusan minti goma na ɗauka ina tunani akan waɗannan dokoki kafin daga baya na ce, 

“Na gode Mama. In sha Allah zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen kiyaye su. Domin in tabbatar miki da hakan a aikace, zan so in ji dalilin da ya sa Yayata Ashalle ta farmake ni da cewa ba ta yarda da ni ba, amma ko kaɗan ba ta damu da cewa Imran yana nan ba balle ta yi magana game da shi. 

Na ƙarasa maganar tare da ƙurawa Ashalle ido da wani irin kallo da ke bayyana rashin tsoro da kafiya. Ita ma wani mugun kallon ta kafe ni da shi. A daidai wannan lokaci sai mutum ya rantse da Allah zakaru ne suke shirin yin faɗa. Ko da ganin haka sai Shamadara ta dube ni tana mai yin murmushi ta ce, 

“Da kyau Haidar, tabbas ka cika ɗan babanka. Na yarda ɗari-bisa-ɗari cewa za ka yi iya bakin ƙoƙarinka. Dangane da Imran kuma, shi ɗin ba baƙo bane. Domin mahaifinsa Maikwalanga babban aminin mahaifinka ne, mahaifiyarsa Tani kuma ƙawata ce sosai. Don haka ba mu da shakku akansa.”

Wani sabon mamaki ne ya lulluɓe ni yayin da na waiga inda Imran yake ina mishi kallon tuhuma. Cikin rawar murya ya ce da ni, 

“Ka yi haƙuri ya kai ɗan’uwana, tun a fada da na ga abinda ya faru na so in yi maka bayani, amma mamaki ya hana ni. Erm… Kuma ka ga ba mu samu damar zama ba balle mu tattauna tun daga lokacin…”

“Ka da ka damu Imran. Wannan ba abin damuwa ba ne. Na ji daɗi da ya zamanto akwai kusanci mai girma irin haka a tsakaninmu. Ina matuƙar alfahari da kai.”

Na ba shi amsa cike da murmushi. Ba tare da wani ɓata lokaci ba kuma na juya fuskata zuwa inda Mamana Shamadara take na ce da ita,

“Ya ke Mamana. Yanzu menene abin yi?” 

Don ba na buƙatar wani ɓata lokaci kuma bayan duk waɗannan bayanan da aka yi yanzu. Ganin alamun hakan a tattare da ni ya sa Shamadara da ce, 

“Idan har muna so mu fita daga cikin ƙangin kulle da ya zamo mana dole kuma mu kaucewa fuskantar rigimar da ka iya dagula komai a cikin Birnin Sahara, to akwai buƙatar ka zama sarkin birnin Sahara.”

“Tun ɗazu abin da Sanafaratu ke ta faɗa min kenan. Amma ni har yanzu ban ga dalilin da zai sa a ce sai ni ɗin ba. Da fari dai, tun da har mutanen Birnin Sahara sun yarda da Nadiya a matsayin sarauniyarsu, me zai hana su yarda da Ashalle a matsayin wata sarauniyar? In ma hakan bai yiwu ba, me zai hana mu haƙura mu bar wa su Dargazu sarautar tun da abinda suke so kenan. In muka ba su abinda suke so, shikenan mun zauna lafiya da su.”

Na ba ta amsa cike da tambaya. Ina kallon su Baruma na gyaɗa kai alamar yarda da maganar da da faɗa. Shi kuwa Imran da Sadiya shiru kawai suka yi kamar ruwa ya ci su. 

“Abin ba mai sauƙi bane kamar yadda ka ke tunani Haidar.”

Shamadara ce ta bani amsa bayan ta yi dogon Nazari. 

“To ki fahimtar da ni ta yadda zan gane Mama.”

Na ba ta amsa ba tare da wani jinkiri ba. Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana tunani kafin ta ce,

“Shawarar da ka kawo mai kyau ce, kuma in da ace zaman lafiya ake yi a birnin Sahara za ta yi aiki. Amma sai dai ba zaman lafiyar ake yi ba. Dargazu da Wajagi suna amfani ne da ƙarfin tsafi da na damtse wurin tsorata sauran ƙabilun birnin Sahara domin su goya musu baya. Da yawan mutanen wannan birni ba su so aka ba Nadiya sarautar nan ba. Amma babu yadda suka iya. Saboda su Dargazu sun mamaye komai. Kuma in da za mu buƙaci su dawo mana da sarautar gidanmu, nan ma wani rikicin ne zai ɓalle. Saboda mutanen birnin Sahara ba su yarda da jagorancin mace ba. Kuma in muka ce mun haƙura mun bar musu sarautar da komai a hannunsu, to tamkar mun miƙa musu kawunanmu ne su gille mana wuya. A matsayinka na namiji ɗaya tilo a cikin wannan ahalin kai ka fi kowa cancantar zama sarki, shi ya sa ya zama wajibi ka karɓe sarautar birnin Sahara.”

Ta ƙarasa maganar da alamun hasala a tattare da muryarta. Bayan ta gama yi min wannan bayani sai dukkanmu muka yi shiru na ɗan wani lokaci. Kowa da irin abin da yake tunani a cikin ransa. Akwai abubuwa da yawa a raina da nake so in yi magana akai, amma wani abu guda ɗaya da ya fi tsaya min a rai ne kawai na yanke shawarar yin magana akai. 

“In ba za ki damu ba Mama, akwai abinda na ke so in sani. Shin me ƙabilar maƙera suka yi da har ake ƙinmu ne? 

“Kai kuwa me ya sa ka yi wannan tambayar?” 

Shamadara ce ta yi min wannan tambayar cike da mamaki. 

“Saboda na kasa yarda da cewa tsoron Dargazu da Wajagi kaɗai zai iya sa ɗaukacin mutane masu tarin yawa irin haka su ƙyamaci wasu gungun mutane ƙalilan ba tare da wani ɓoyayyen dalili ba.”

Na ba ta amsa cike da amincewa da hasashen da na yi. Sai dai kafin ta kai ga ba ni amsa, tuni Ashalle ta sake miƙewa a fusace ta ce, 

“Ka bar wani noƙe-noƙe mana in har kai ma matsoraci ba ne ka amshi tayin da akai maka.”

“Ku haƙura da sarautar mana kai tsaye ku huta idan har ba kwaɗayin mulkin ku ke yi ba.”

Na mayar mata da amsa nutse ba tare da na motsa daga inda nake ba. 

“Me? Kwaɗayin… Ki ji fa abinda yake faɗa Umma!”

Ashalle ta faɗa tana mai duban Shamadara cike da rashin yarda da abinda na faɗa. 

“Ba haka ba ne Haidar, ko da yake na san akwai masu yi mana irin wannan kallon a cikin mutanenmu, ba kwaɗayin mulki ba ne ya sa muka dage akan wannan maganar.”

Ta ɗan yi shiru kanta a ƙasa kafin ta ɗago ta ce, 

“Tabbas akwai dalilin da ya sa mutane da yawa suka tsanemu. Wannan dalili kuwa sananne ne ga kowa. Baruma, yi masa bayanin kakanku.”

Baruma, wadda tun ɗazu ta yi shiru ta gyara zama sannan ta fara magana da cewa, 

“A lokacin da kakanmu hantsi ke kan mulki, ya yi abubuwa masu muni ƙwarai da gaske. Ya zalunci mutane da dama, ya yi wa wasu ƙwace ta ƙarfin tsiya saboda ƙarfin mulki. Wannan dalili ne ya jawo rushewar zumuncinmu da mafi yawancin ƙabilun wannan birni namu saboda babu wani sarki da ya taɓa yin haka. Zumunta da yarjejeniyar da sarki Hanka’u, wato mahaifin kakanmu hantsi ya ƙulla da mutane masu yawa duk sai da Sarki Hantsi ya wargaza su. Kafin wannan lokaci, ƙabilu ashirin daga cikin ƙabilu ashirin da shida da muke da su a birnin Sahara duk suna goyon bayan ƙabilar maƙera ne, amma a yanzu ƙabilu uku ne kawai suke zumunci da mu. Daga ƙabilar maɗinka, ƙabilar Manoma sai ƙabilar masunta. Wannan shi ya sa muka tara maƙiya sosai. Mahaifinmu ya yi yunƙurin wanke waɗannan laifuka da kura-kuran da mahaifinsa ya aikata. Sai dai bai samu cika wannan buri ba har ya bar birnin.”

Ko da Baruma ta zo nan a zancenta, sai kawai na yi kasaƙe ina kallonta tare da juya lamarin a cikin ƙwaƙwalwata. Haƙiƙa lamarin ahalin maƙera da na birnin Sahara baki ɗaya abu ne mai wuyar fahimta. Babban abin da ya fi ɗaure min kai shi ne irin yadda suka zuba min ido cike da tsammani, suna masu jiran abinda zan faɗa. Har da ita Ashalle kanta kuwa. 

“Yanzu dai idan na fahimci lamarin nan da kyau, kuna so in zama sarki ne saboda in taimaka wa ahalina su fita daga tarkon da su Wajagi da Dargazu suka saka su. Sannan in wanke laifukan da mahaifina da kakana suka yi a baya. Daga ƙarshe kuma in wanzar da zaman lafiya da lumana a birnin Sahara. Haka ne?’

Na tambaye su gaba ɗaya. Dukkansu suka amsa min da hakane a tare. Ban yi mamakin jin hakan daga gare su ba, dama na tsammaci hakan. Son haka sai na yi musu wata tambayar mai matuƙar muhimmanci da cewa, 

“Ta yaya kenan zan iya zama sarki?” 

“Ta hanyar shiga gasar neman karagar da za a yi a taron gani nan da watanni uku masu zuwa.”

Shalibai ce ta ba ni wannan amsa kai tsaye. Kallon ta na yi da kyau duba da cewa sai yanzu ta yi magana. Nazari na yi na ɗan wani lokaci sannan na ce, 

“Ku kuma wace irin gudummawa za ku ba ni wajen cimma nasarata na zama sarki a wannan birni naku mai albarka?” 

Wannan karon Shamadara ce ta ba ni amsa da cewa, 

“Ya kai ɗana, ka sani cewa a shirye muke da mu ba ka duk wata gudummawa da ka ke buƙata domin ka samu nasara. Ko ba komai nima ‘ya’yana sa samu su yi aure hankalina ya kwanta.”

Wannan maganar da ta yi ba ƙaramin girgiza ni ta yi ba. Don haka sai na tambaye ta me take nufi. Fuskarta cike da damuwa ta ce, 

“Dukkansu sun sha alwashin ba za su yi aure ba har sai ranar da sarauta ta dawo gidanmu. Wannan shi ya sa har yanzu cikinsu babu wadda ta yi aure, ba wai don ba su da masoya ba.”

Shiru kawai na yi ina tunanin dukkan abubuwan da suka faɗa min tare da jinjina girman al’amarinsu da kuma abinda suke so in yi. Tabbas yanzu na ƙara fahimtar illar rashin namiji a cikin gida. Domin na tabbata da mahaifinmu na da rai kuma yana tare da su da hakan ba za ta taɓa faruwa ba. Tausayin halin da suke ciki ne ya ƙara lulluɓe ni. Nan take na yi wa kaina alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na saita al’amuran sun koma daidai da izinin Allah. Sai dai dole in buƙaci wani muhimmin abu daga gare su kafin mu kai ga gacin muradinmu. 

Tashi na yi daga kan kujerar na nufi can ƙarshen rumfar ina mai ƙura wa sararin samaniya ido cikin tunani. Na shafe kusan mintuna talatin a tsaye ina tunani, su kuwa kamar sun san ba na so a takura min sai suka ƙyale ni. Bayan na samu matsaya a tsakanina da zuciyata ne sai na dawo garesu. Komawa na yi kan kujerar na zauna sannan na dube su da kyau na ce, 

“Na amince zan yi dukkan abubuwan da ku ke buƙata amma a bisa wasu sharuɗɗa. Sharuɗɗan kuwa su ne kamar haka; da farko dai ni Musulmi ne, don haka zan yi komai nawa ne a bisa yadda na ga ya dace da addinina ba yadda ku ko wasu za su buƙata ba. Abu na biyu. A matsayina na yarima, wanda ku ka amince da ni in wakilce ku, daga yau duk wani yanke hukunci da sauraren wasu bayanai da suka shafi wannan ahali ya dawo hannuna. Babu wanda zai aikata wani abu face sai da izinina, kuma dole ne kowa ya bi duk abinda na zartar ba tare da gardama ba. Dukkan dukiya da bayi da kuyangi da duk wani abu naku yanzu ya zama mallakina. Abu na uku, za ku taimaka min wurin zartar da sabbin tsare-tsaren da zan kawo ba tare da tirjiya ba. Abu na huɗu, za ku ba ni horon yaƙi na musamman domin tunkarar wannan gasar karawa da ke gabana. Abu na biyar kuma za ku amshi Addinin Musulunci sannan ba za ku zarge ni da komai ba ko da ban yi nasara ba.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Birnin Sahara 15Birnin Sahara 17 >>

1 thought on “Birnin Sahara 16”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×