"Dokoki kuma?"
Na tambaya cike da mamaki. Da alama mutanen Birnin Sahara ba sa gajiya da zaƙule-zaƙule.
"Ƙabilar maƙera gaba ɗayanta ta dogara ne akan waɗannan dokoki da zan sanar da kai. Abin da ake so ga kowane ɗan ƙabilar maƙera shi ne ya yi ƙoƙarin ganin ya kiyaye waɗannan dokoki bakin iyawarsa."
Shamadra ce ta yi min wannan bayani.
Shiru na yi na ɗan wani lokaci ina tunani, kafin daga baya na ce,
"Shikenan Mama sanar da ni waɗannan dokoki in ji su."
Har ta bu. . .
Masha Allah