Skip to content

Bita akan rubutun gajeren labari 1

An gabatar da wannan makala ne da farko a matsayin bita akan rubutun gajeren labari wacce taskar Bakandandamiya ta shiryawa marubuta daga ranar 15 – 20 ga watan Yuni na shekarar 2020. Wanda ya gabatar da bitar shi ne marubucin littafin Tekun Labarai, Danladi Z. Haruna.

Ku latsa nan don karanta cikakken bayani game da hadafi da kuma maudu’an bitar.

Don ganin cewa mutane sun kara amfanuwa da wannan bita mai ilmantarwa, Bakandamiya ta hada bitar wuri guda a cikin makala kamar haka:

RANA TA FARKO

Darasi na 1

Gabatarwa

Rubutun gajeren labari na bukatar kaifafa tunani tare da dunkule ma’ana ta hanya mai sauki da mai karatu zai fahimta. Kuma daga irin yadda ka aiwatar da gajeren labari ne ake tsammanin zai kayatar ko akasin haka ga labarin littafi. Don haka abu ne mai kyau kwarai ka nakalci yadda ake rubuta gajeren labari mai ma’ana.

Idan aka ce gajeren labari, ana nufin duk wani labari da yake da farko tsakiya da karshe amma yawan adadin kalmominsa ba su kai ya zama littafi sukutum guda ba. Yawanci littafin labari na Hausa yana farawa daga shafuka 80 zuwa sama. Don haka za mu iya daukar duk labarin da tsawonsa bai kai shafi 80 ba, a matsayin gajeren labari.

Sai dai gajerun labarun da ake bukata domin shiga gasa, an karkasa su zuwa rukuni kamar haka:

A Gargajiyance (Traditional): kalmomi 1,500-5000
Takaitaccen labari (Flash Fiction): Kalmomi 500-1,000 words
Gajeriyar Tatsuniya (Micro Fiction): Kalmomi 50 – 500.

Mafi yawa an fi saka gasa akan kalmomi 1000 zuwa 3000. Don haka wajibi ne marubuci ya tsara labarinsa daga farko har karshe ba tare da ya tsallake adadin kalmomin da ake bukata ba. Idan aka samu gazawa ko zarcewar haka, yana jawowa a cire labarin komai dadi ko ma’anar da yayi.

Dasari na 2

Abin tambaya, shin ta yaya za mu iya gane labarinmu ya kai adadin kalmomin da ake bukata?

Wannan tambaya ce mai muhimmanci, domin da irin rubutun da muke yi ne ake auna yawan kalmomin da muka rubuta. Na’urar kwamfuta da wayoyinmu na Android da Apples, suna da manhajar yin rubutu wadda ke kirga duk kalmar da muka rubuta. Hakan na yiwuwa ne wajen kirga adadin tazarar kalmomin da muka bayar watau space.

A bisa wannan ma’auni, idan muka rubuta kalmar ‘Abinda’ ba daidai take da ‘abin da’ ba. Domin ta farko kalma daya ce a hade, ta biyu kuma kalmomi biyu ne a rarrabe.

Kenan wajibi ne mu san dokokin rubutu musamman na hadewa da rabewa. Wannan ne zai ba mu adadin kalmomin da muke bukata ba tare da alkalai sun ci gyaranmu ba.

Kaidojin rubutu suna da matukar muhimmanci wajen fayyace azancin labari. Don haka alkalai ke ware maki na musamman ga duk labarin da ya cika ka’idojin rubutu sosai.

Sashen Hausa na BBC ya maida hankali sosai wajen cika ka’idojin rubutu. Kuma ba kasafai suke kula rubutun da bai cika ka’idoji sosai ba musamman rubutun da aka yi watsi da kalmomin hadewa da rabawa.

Amfanin ka’idojin rubutu

Daya daga amfanin ka’idojin rubutun Hausa shi ne isar da sako kamar yadda kake buri a cikin ranka. Domin akwai kalmomi da haɗe su ko rabe su ke jawo wata fassarar ma’ana ta daban. Matukar ka nakalci yadda ake rubuta kalma, to wajibi ne kuma ka gane cewar raba ta zai ba da karuwar adadin kalmomi kuma hade ta zai kawo raguwar adadin kalmomi har ma da ma’ana.

Za mu kawo misalin yadda hadewa da rabewar kalma ke sauya ma’anar jumla.

Darasi na 3

Bari mu dauki misali.

Malam Faruk Lawan Da’u ya kawo misalin wasu jumloli da yadda hadewa da rabewa ya jawo sauya ma’anarsu da kuma adadinsu.

Yi nazarin wadannan jumloli a tsanake ka fada mana abin da kowacce jumla ke nufi da kuma abin da ya bambanta ta da sauran:

1. Ta je fadama
2. Ta jefa dama
3. Taje fa dama
4. Ta je fa da ma
5. Tajefa dama
6. Ta je fada ma
7. Taje fadama
8. Taje fada ma
9. Ta jefada ma
10. Tajefa da ma

Ina so dalibai a yi nazarin wadannan jumloli a fayyace mana abubuwa kamar haka:

a. Wadanne ne jumloli masu ma’ana. Wadanne ne marasa ma’ana?

b. A cikin jumloli masu ma’ana da aka kawo a sama, me kowacce ke nufi?

c. Kalmomi nawa ne a cikin kowacce jumla mai ma’ana?

A RUBUTA AMSAR A KASA CIKIN MINTI 10

Darasi na 4

Kammalawa

Idan aka yi kuskuren rubuta kalmar da ba ita ba ce, mai karatu zai yi maka fahimta baibai, kuma zai sauya ma’anar labarinka.

Haka kuma a wajen dangantaka, yawancin kalmomin mallaka ana hade su ne domin nuna alaka tsakanin mamallaki da abin mallaka. Misali, idan ka rubuta ‘Takalminka’, za mu fahimci takalmin mallakin tauraron da ake magana da shi ne. Amma idan ka rubuta, ‘Takalmin ka’ sai mu yi tsammanin cewar takalmin ne ya aikata wani abu wanda gaba daya ya sauya ma’anar zancen da ake yi.

Kafin mu yi sallama bari mu bayar da aikin gida.

Kowanne daga mahalarta wannan bita ya rubuto mana gajeren labari mai dauke da kalmomi 150 – 250.

Labarin ya kasance an lura da kaidojin rubutu musamman hadewa da rabewa. Sannan a ya zamana yana da mafari… Kada a damu koda bai kai karshe ba. Domin mafarin labari shi ne babban abin da ke rike makaranci har zuwa karshe.

Kenan labarin da za a turo zai iya kasancewa tsakure ne daga wani labarin. Duk wanda zai aiko sai ya wallafa a wannan zaure. Wanda ya aiko da nasa zai samu maki, wanda da shi za a yi amfani waje bada satifiket.

Idan akwai tambaya sai a yi karkashin kowanne post din da tambayar ta taso.

Ku ci gaba da karanta darasi na gaba.

Wasallamu Alaikum

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page