Skip to content

Kalubale biyu na fuskanta lokacin da na fara rubutu – Sadik-Abubakar

Hikaya ta tattauna da hazikin matashin marubucin nan wato Sadik Abubakar (Abban Ai’sha). A cikin tattaunawar ya bayyana yadda yake zana taswirar labarinsa a cikin kwakwalwarsa, kafin ya fara rubutun. Ga yadda tattaunawar tamu ta kasance:

Tambaya: Za mu so mu fara da jin taƙaitaccen tarihinka, idan babu damuwa.

Amsa: Assalama Alaikum! To ni dai sunana Sadik Abubukar Abdullahi (Abban Aisha). An haife ni a unguwar Gwagwarwa, cikin ƙaramar hukumar Nassarawa ranar Lahadi 01/01/1984.

Na yi karatun Primary a nan Gwagwarwa Primary School, daga nan na wuce zuwa Government College Kano (K.T.C). Bayan nan, na ɗan dakata kafin na ci gaba da karatun, sakamakon rashin kyawun jarrabawa. To daga bisani bayan sake wata jarrabawar kuma na samu admission a Kwalejin Ilimin ta Tarayya da ke Kabuga, na karanta N.C.E.

Gabanin za a rufe makarantu kuma, na fara karatun digiri a A.B.U, kodayake affiliation ne, a nan FCE Kano, ake karatun. Duk dai a fannin ilimin ne wato (B.Ed Language Arts). Wannan a dunƙule ke nan ɗan abin da ya sawwaƙa daga rayuwata.

Sadik Abubakar 1
Marubuci Sadik Abubakar

Tambaya: A wacce shekara ka fara rubutu, kuma me ya ja hankalinka har ka fara?

Amsa: To ni dai na fara rubutu ne saboda tsananin sha’awar da marubuta ke ba ni, ta yadda suke jahadi da alƙalami ba da takobi ba wajen daidaita rayuwar al’umma. Na kasance mai burin zama haka.

Na fara sha’awar rubutu tun lokacin da marigayi Yaron Malam, Abdul’aziz Sani Madakin Gini, da shi da takwarorinsa suke ganiyar rubutun littattafan yaƙe-yaƙe. A wannan lokaci babu wani littafin yaƙi da zai fito face na saye shi na karance shi cikin ƙankanen lokaci.

A wancan lokacin na fara yin rubutu irin na yaƙe-yaƙen, na kan rubuta kusan rabin littafi ko fiye na ajiye. Sai na kama wani kuma. Na ɗan yi rubuce-rubuce ba laifi a wannan ɓangare.

Daga rasuwar Yaron Malam, (Allah Ya jaddada masa rahma) sai na daina karanta irin waɗannan littattafai kwata-kwata. Bayan kamar shekara biyu zuwa uku haka, sai na koma karanta littattafan soyayya da zamantakewa irin wanda marubutan zamani suke rubutawa a yanzu.

A wannan fanni na fara karanta littattafai irin na su Sa’adatu Saminu Kankiya da Hadiza Salisu Sharif.

Tambaya: Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.

Amsa: Kawo yanzu na rubuta littafai guda shida da suka haɗa;

  1. Sahura
  2.  Matakin Nasara
  3. Ƙuda Ba Ka Haram.
  4.  Cikas
  5.  Rayuwar Talaka
  6.  Kowace Ƙwarya.

Tambaya: Wanne littafi ka fi so a duk cikin litattafan da ka rubuta, kuma me ya sa?

Amsa: Matakin Nasara.

Tambaya: Wanne littafi ne ka taɓa karantawa da ya fi burge ka?

Amsa: Jiki Magayi na Tafida John, Wusasa.

Tambaya: Shin ka taɓa shiga wata gasa, idan e ne amsar, shin ko ka taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?

Amsa: Na shiga gasanni sosai kuma na yi nasara a matakin farko da na biyu har zuwa mataki na uku. Gasar Nobel Writers ni na zama gwarzo na farko, gasar Jarumai Writers ni na zo na huɗu, gasar Mun Gani A Kasa ina cikin waɗanda suka yi nasara, da sauran gasanni dai da yawa.

Nasarorin da na samu a fannin rubutu suna da yawan gaske, kama daga abin duniya da haɗuwa da manyan mutane. A dalilin rubutu na haɗu da kamfanin Bakandamiya wanda na samu cigaba a kasancewa ta da kamfanin.

Tambaya: Idan za ka yi rubutu, kakan tsara komai da komai ne kafin ka fara ko kuwa kai tsaye kake farawa?

Amsa: Na kan tsara taswirar labarin ne a ƙwaƙwalwata kafin na fara, sai dai wani lokaci akan samu ƙarin wani ɓangare ko ragi a cikin labarin kasancewar labari mai nagarta shi ke jan marubuci.

Tambaya: Wacce hanya ka ke bi wajen samun jigon labarunka?

Amsa: Hanyoyi ne da dama, kamar bincike da tunani da kuma kallon abubuwan da ke wakana yau da kullum a cikin al’umma.

Tambaya: Ya kake yi idan wani tunani sabo ya zo maka game da wani rubutu na daban alhalin kana tsakiyar rubuta wani. Kakan saki wancan ne ka yi wannan sabon ko kuma sai ka gama da wanda ka fara?

Amsa: Rubuta jigon nake a wata takarda ko wani waje in ajiye shi, idan na kammala wanda nake tsaka da yi sai na ɗauko shi na fara.

Tambaya: Shin ka taɓa fuskantar ƙalubale tunda ka faɗa harkar rubutu?

Amsa: Ƙalubale biyu na fuskanta muhimmai a lokacin da na fara rubutu na haƙiƙa.

Na farko dai shi ne ina son jama’a su karanta labarina. Tunda a yanar gizo zan wallafa shi, ya zama dole na nemi group ɗin da zan rinƙa tura labarin. Na sha wahala kafin na samu group admins su ba ni dama na rinƙa saka labarin, wasu ma kai tsaye suka ce mini ba zai yiyu ba.

Sai ƙalubale na biyu shi ne tsarin rubutun Hausa, gaskiya ban fahimci rubutun Hausa na da wahala ba, sai da na fara sakin littattafai. Dole na koma na ɗauki littattafan Hausa na koyon ƙa’idojin rubutu.

Sadik Abubakar 2
Marubuci Sadik Abubakar

Tambaya: Wanene/wace ce wanda ya zame maka madubin da kake dubawa yayin rubutu?

Amsa: Kamar yadda na faɗa a baya, kusan dukkan marubutan da nake karanta littattafansu, su ne suka zame mini madubi. Ba wai takawa nake na je wajensu ba, aikace-aikacen da suka yi su ne kamar alƙiblata a fannin rubutu.

Tambaya: Wacce hanya ka ke bi wajen fitar da halayen taurarinka tare da ba su sunan da ya dace da su?

Amsa: Nakan duba irin rawar da nake so tauraro ya taka a labarin, sai na zaba masa suna da kuma halayyar da nake so ya nuna a cikin labarin.

Tambaya: Shin ko ka taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarka a cikin rubutunka?

Amsa: A’a

Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ka wahala daga cikin dukkan litattafan da ka taɓa rubutawa?

Amsa: Ƙuda Ba Ka Haram

Tambaya: Mafi akasarin marubuta sun fi karkata da alƙalumman rubutunsu ne a harkar soyayya, shin kai wane ɓangaren ka ɗauka?

Amsa: Babu shakka yawancin marubuta duk mun karkata ne wajen rubutun soyayya. Ni ma a fannin nake, sai dai ba gabaɗaya ba gaskiya. Duba da yadda muke da wasu jigogin da ya kamata a ce mun mayar da hankali a kansu.

Misali; matsaloli irinsu rashin hakuri da ke damun al’umma, da zaman banza ga mata wanda hakan ke janyo saɓani tsakaninsu da mazajensu. Duk waɗannan matsalolin suna buƙatar mu mayar da hankali wajen faɗakar da al’umma. Muhimmancin sana’a ga mata da hakuri duk jigogi ne da ya kamata mu yi rubutu a kai.

Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da ka rubuta wanne ka fi so, kuma me ya sa?

Amsa: Sahura, saboda tsantsar haƙurin da ta nuna a cikin labarin. Ina son mutum mai haƙuri sosai.

Tambaya: Shin wace irin nasara ko ci gaba ka taɓa samu a sanadin rubutu?

Amsa: Hakane akwai nasarori babu shakka, babbar nasara da na samu wacce ita ce maƙasudin shiga ta harkar rubutu, shi ne na ba wa al’umma gudummawa wajen warware matsalolin da ke damun su. Haƙiƙa wannan buri nawa ya cika, mutane kan tuntuɓe ni ko kira, ko SMS ko ta Whatsapp suna jinjina mini a kan abin da suka karanta a littafina, ina jin daɗin hakan.

Akwai lokacin da yarona ba shi da lafiya, sai na kwana biyu ban yi posting ba, kira da na riƙa samu ya yawaita ana tambaya ta lafiya kuwa? Da na faɗa musu abin da ya faru, wata daga cikinsu cewa ta yi na tura account number ta, kuɗi ta turo mini. Wata kuma cewa ta yi za ta zo har gida ta duba shi, na ce ta bari kawai na gode, ta yi masa addu’a. Akwai alheri da wasu suke mini, wasu katin waya za su turo maka.

To kin ga wannan duk nasarori ne, Allah ya haɗa ka da mutanen kirki wanda suke nuna damuwa idan ka shiga damuwa.

Alhamdulillahi! Mun gode Allah.

Tambaya: Mene ne abin da ka fi so game da rubutu?

Amsa: Ina son na ga cewa na fara labari na kammala shi cikin lokaci lami lafiya.

Tambaya: Me ka kan yi a duk lokacin da kake da sarari?

Amsa: Ina karatu ko bincike.

Tambaya: Wace karin magana ka fi so? Kuma me ya sa?

Amsa: Mahaƙurci mawadaci. Saboda haƙuri shi ne matakin nasara.

Tambaya: Mafi akasari yanzu marubuta sun tsunduma harkar rubutun fim, shin kai ma kana yi?

Amsa: Ban fara ba, amma ina da burin hakan sosai. Domin akwai wani shiri da BAKANDAMIYA ta fara shiri mai suna ‘DABARUN RUBUTUN FIM’ malam Danladi shi ya fara gabatar da shi a cikin watan Agusta. Daga baya sai aka dakatar da shirin aka daina yin sa. Kodayake Abu Hisham ya turo mana makamancin shirin wanda aka gabatar a shekarun baya. Muna fatan BAKANDAMIYA za ta dawo mana da wannan shiri mai matukar muhimmanci.

Tambaya: Akwai ƙungiyoyi da dama na marubuta shin kana da ƙungiyar? Ya sunan ƙungiyar?

Amsa: E, ina da kungiya, ni ne ma shugaban kungiyar wato Lafazi Writers Association.

Tambaya: Wane abu ne yake ci maka tuwo a ƙwarya game da marubuta?

Amsa: Abin da yake ci mini tuwo a ƙwarya shi ne yawaitar satar fasaha. Wannan kalubale ne babba da marubuta ke fama da shi musamman online writers. Sai ki ga marubuci ya zauna ya ɓata lokacinsa da tunaninsa wata da watanni yana kirkirar labari, amma lokaci guda sai wani ya zo ya juya masa littafin ko kuma ma ya cire sunan marubucin, shi ya saka nasa. Wannan ba daidai ba ne.

Tambaya: A naka ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?

Amsa: Online ya fi, shi ke tafiya da zamani kuma shi ne mai sauƙi ga kowane marubuci matuƙar yana da wayar zamani (smartphone).

Tambaya: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?

Amsa: Tasirin marubuta cikin al’umma ba ƙarami ba ne. Marubuta ne ke da baiwar sarrafa zukatan al’umma cikin ruwan sanyi koda kuwa al’ummar ba sa so.

Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da kake rubutawa a yanzu haka da masoyanka za su yi tsumayin fitowarsa?

Amsa: A’a.

Tambaya: Wane irin jan hankali za ka yi wa marubuta masu satar fasaha? A ganinka me yake jawo hakan?

Amsa: Duk mutumin da yake satar fasaha ba marubuci ba ne sam, ya je can ya nemi wani sunan. Jan hankalina ga irin waɗannan mutanen shi ne, su guji aikata wannan mummunan aiki. Laifi ne babba, wanda ina jin a cikin kundin dokoki na ƙasa, an bayyana cewa satar fasaha daidai yake da satar kuɗi. Kin ga kuwa idan haka ne, to kai tsaye za mu iya kiran mai irin wannan ɗabi’ar ɓarawo. Su tuba su bari, idan suna ganin babu yadda za mu yi da su, to sai mu yi wa mutum Allah Ya isa.

Abin da yake janyo satar fasaha akwai rashin baiwar ƙirƙira. Domin shi marubuci dole ya zama yana da baiwar ƙirƙirar labari. Sannan akwai rashin bincike da kuma garaje. Su irin waɗannan mutanen masu satar fasaha, ba sa zurfafa bincike yayin fara rubutu. Hakan nan kuma suna da gaggawar sakin littafi. To irin wannan ma za ki ji littafin ba ya daɗi ko kaɗan.

Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wanne ne ya fi saurin isar da saƙo?

Amsa: Fim

Tambaya: Mene ne burinka a harkar rubutu?

Amsa: Burina shi ne na rubuta abin da zai amfanar da jama’a kuma ni ma na amfana.

Tambaya: Daga ƙarshe, me za ka iya cewa game da Bakandamiya Hikaya?

Amsa: Ina mai jinjina wa wannan kafa ta Hikaya da ta zama irin ta farko a tarihin marubutan Hausa da dukkan wani abu da ya shafi adabi, ita ce kafa ta farko da ta tattare littafan Hausa ta killace su a yanar gizo. Ita ce kafar da ta raba dubban marubuta da rubutu babu ladan komai. Wato dai duk marubucin da yake rubutu a yanzu kuma ba ya samun kuɗi to shi ya so.

An yi hira da Sadiq Abubakar ne a ranar Talata, 27 ga watan Oktoba 2020; 9am – 6pm kai tsaye. An kuma ta ce tare da sabunta tambayoyin a ranar 26 ga watan Maris 2024.

Tsara tambayoyi da gabatarwa: Maryam Haruna tare da Hauwa’u Muhammad.

Tacewa da sabuntawa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page