Skip to content
Part 1 of 16 in the Series Ko Wace Kwarya by Sadik Abubakar

Bismillahir Rahmanir Raheem.

“Gafara dai! Gafara dai boka!” Cikin tsananin tsawa da ƙaraji bokan ya ce, “Su waye nan? Ku dakata kada ku sake motsawa ko da taku guda ne.”

Cak! Matan suka tsaya ba wacce ta ɗara daga wajen wanda ya kasance gindin wata itaciyar tumfafiya ne. Mintuna kamar biyar suna tsaye, cikin garjin rana mai tsananin zafi, yayin da shi kuma bokan sai iface-iface da siddabaru yake irin nasu na ‘yan tsibbu.

Zuwa can ya kurma wani ihu mai matuƙar razanarwa, wanda saboda tsananin firgici, matan biyu suka ƙanƙame juna kamar ɗaya za ta shige cikin ɗaya.

“Ku juya ku ƙaraso da baya da baya.” Bokan ya faɗa bayan sun dawo hayyacinsu. A tsorace suka juya da baya suka isa gindin wata itaciyar kuka mai tsananin tsayi da kuma faɗi. Zallar rassan itatuwa ne a jikinta amma babu ganye koda ƙwalli ɗaya.
“Me ke tafe da ku?” Bokan ya tambaye su.

Guda daga cikinsu ta kada baki cikin yanayin tsoro ta ce, “Boka da ma wannan aminiyata ce, tana da yarinya ne ta kawo munzalin. Tana da manema amma sai dai ta nace akan wani yaro.”

“Dakata haka! An riga an sanar da mu komai. Me take so a yi wa yaron? Mu kauda shi daga doron ƙasa ko kuma a raba su?”

Gabaɗayansu suka zaro idanu cikin sigar firgici suka ce, “A’a boka, ba hallaka shi za a yi ba, kawai dai a raba tsakaninsu. Muna so a cire son sa daga zuciyarta a maye mata gurbinsa da wani Alhaji ɗan arziki.”

Boka ya saki wani irin ihu haɗe da dariya sannan ya ce, “An gama!” Ya muskuta ɓangaren hagunsa ya ɗauko ƙullin magani guda biyu ya miƙa musu tare da cewa, “Wannan baƙin za a riƙa zubawa cikin abincin yarinyar ɗayan kuma a ruwan wankanta za a riƙa zubawa, safe da yamma za a riƙa yi. Idan aka fara ba dainawa sai maganin ya ƙare, a kula sosai idan aka kuskure duk abin da ya biyo baya babu ruwana.” Ya ƙarasa maganar da sakin wata muguwar dariya.

“To boka za a kiyaye mun gode!” Ta faɗa tare da ajiye wasu dunƙulallun kuɗaɗe da aƙalla za su kai dubu goma.

“Za ku iya tafiya!” Bokan ya faɗa, suka miƙe sun fara takawa ke nan taku ɗaya biyu kafin su yi na uku, ya sake daka musu tsawa tare da cewa, “Ku juya da baya sai kun yi taku goma sannan ku koma tafiya daidai.”

Hakan nan suka juya a razane suna tafiya da bayan har suka yi adaɗin takun da ya umarce su sannan suka juya daidai.

*****

Umma Saratu ke nan da ƙawarta Yahanasu, wacce ta yi mata jagora zuwa wajen boka kamar yadda muka ji. Watau ita dai Umma Saratu tana da budurwar ‘ya wacce ta kawo munzalin aure, ana kiran ta Zaliha.

Ta kasance kyakkyawar yarinya mai kyawun halitta da diri, ga kunya sannan tana da farin jini, wanda babu shakka waɗannan siffofin nata sun isa su tara mata samari masu yawan gaske.

To sai dai kasancewar ta mai kunya da kuma tarbiyyar da Allah Ya kange ta da ita, sam ta ƙi yarda ta mayar da ƙofar gidan nasu dandalin taɗi, duk kuwa da matsin lambar da take fuskanta daga wajen mazan da kuma mahaifiyarta. Mutum daya tal take kulawa wanda ta amince da shi. Watau wani malamin maƙarantar Islamiyyarsu ne ana kiran sa Abdullahi.

Babu shakka wannan ɗan tahaliki shi ya fi dacewa da ita, domin duk cikin waɗanda suka nuna suna son ta babu kamarsa ta fuskar nutsuwa. Bugu da ƙari shi ɗin ma ba baya wajen kyau. Kyakkyawa ne irin ajin farkon nan, ‘yammatan da dama ke kawo masa caffa, amma shi ma ya tsayar da ƙafarsa cak a kanta.

To sai dai wannan tsaftatacciyar soyayya da ke son wanzuwa a tsakanin waɗannan masoya, ta fara samun cikas da tasgaro ta ɓangaren Umma, watau ita mahaifiyar budurwar. Daidai da minti ɗaya ba ta kaunar Abdullahi, tun lokacin da ta fahimci hulɗar soyayya ta ƙullu a tsakaninsu. Daga nan ta fara neman hanya da dalilin da za ta yi musu farraƙu.

Da farko dai ta fara da yiwa yarinyar hannunka mai sanda, sai dai ba ta fahimci abin da uwar ke nufi ba. Tafi-tafi ta fito fili take faɗa mata ta ƙyale shi, ta nemi wani mai maiko cikin samarin nata. To daga nan ne al’amura suka fara sauyawa tsakaninta da ‘yar tata.

A wata ranar Juma’a da dare, guda cikin maneman Zaliha, da ke amsa suna Alhaji Saminu, wanda ba saurayi ba ne, matansa uku ya zo ƙofar gidan su zance. Ya aika a kira ta, yaron ya shigo ya ce, “Wai ana sallama da Zaliha.”

Tana zaune kuwa a tsakar gida tana tilawar karatun Ƙur’ani, ta dakata ta amsa masa da cewa, “Ka je ka ce in ji wa?”

Yaro ya juyo ya fito, ba jimawa ya koma cikin gidan ya ce, “Wai in ji Alhaji Saminu.”

“Ka je ka ce masa ta yi barci.” Zaliha ta faɗa. Kafin yaron ya juya Umma ta yi fit ta fito daga falo tare da cewa, “Kai yaro je ka ce masa tana zuwa ka ji.” Ta faɗa tare da ƙarasa fitowa ta yi kan Zaliha da faɗa, “Yau na ji shashanci da sakarcin banza, mutumin kirki ya aiko kiran ki saboda rashin mutumci ki ce wai a ce kin yi barci? Ke kun ji ni da ‘Ya do Allah! To maza ki tashi ki kintsa ki fita kafin na saɓa miki. Shi ke nan babu wanda za ki saurara sai wannan almajirin yaron da shi ma ta kansa yake yi. Na yi miki nuni akan ki rabu da shi ɓata miki lokaci zai yi, amma ba ki fahimta ba. Ke kwatakwata ma ba tsarar aurenki ba ne, bai dace da ke ba sam. Ba shi da kuɗin da zai iya auren ki bare har ya iya riƙe ki.”

Wani irin raɗaɗin zafi Zaliha ta ji yana dira a tsakiyar zuciyarta sakamakon jin waɗannan kalamai marasa kangado. Gimtsewa ta yi kawai ta miƙe alatilas ta zura hijabinta har ƙasa ta fito domin cika umarnin uwar tata.

Alhaji Saminu tsaye yake jingine jikin motarsa baƙa wuluk ƙirar Honda Anaconda. Ta isa wajen tare da yin sallama. Cikin murmushi ya amsa da cewa, “Ranki ya daɗe!”

Tun daga sallamar da ta yi masa, ba ta sake buɗa bakinta ta ce da shi uffan ba, haka ya ƙaraci surutansa kimanin mintuna biyar. Da ya fahimci ba ta da niyyar kula shi sai ya ce, “Bari na wuce ko, na ga kamar barci ya fara kama ki. Ga wannan ko!” Ya faɗa tare da miƙa mata wasu damman kuɗaɗe masu yawa. Ko kallon su ba ta yi ba ta ce, “Na gode.” Ta juya ta nufi gida ta bar shi nan tsaye riƙe da kuɗi a hannu.

Shigar ta zaure ta yi kaciɓus da Umma, har firgita ta yi, domin ba ta yi tsammanin akwai mutum a zauren ba. Ta ɗan kaikaita ta wuce ciki. Ita kuwa Umma wani ƙududun baƙin ciki ne ya turnuƙe mata zuciya, kamar ta kai mata duka amma sai ta ƙyale ta. Yau ta ga samu ta ga rashi! Arziki yana bin su har gida amma Zaliha na son yi mata ƙafar ungulu, babu shakka sai ta tashi tsaye a kanta.

Cikin gidan ta nufo zuciyarta a zafafe, Zaliha kuwa ta ƙule can cikin ɗakinta ta kwanta. Ranta cike da fargaba domin ta tabbata Umma laɓewa ta yi tana kallon su, kuma babu shakka yau faɗa dai sai ta Allah, wai gwari ta sayi maita.

“Kina ina shashasha munafuka, fito nan! Wallahi ba ki isa ba ki yi mini wannan lalatar a nan gidan, wannan mutumin shi ne mijinki shi za ki aura. Don haka tun muna shaidar juna ni da ke ki shiga taitayinki, ba na son rashin mutumci, ki rabu da wancan sakaran.” Kwararaton da Umma ta fara yi ke nan, alatilas Zaliha ta fito tana cewa, “Umma don Allah ki yi haƙuri…”

Ta katse ta da cewa, “Na ƙi yin haƙurin, wannan ai shashancin banza ne. Na ga shi ma mahaifinki faure miki gindi yake, ya ki tsayawa ya yi miki faɗa, to matuƙar kina son kanki da arziki ki rabu da wancan yaron. Wannan Alhajin shi ne mijinki, shi ne ya dace da ke.” Tana faɗa ta shige ɗaki ta bar Zaliha durƙushe.
“Innalillahi Wa Inna Iaihirr Raji’un! Allahumma Ajirni Fi Musibati Wakhlifni Khairan Minha!” Zaliha ta faɗa sannan ta miƙe ta nufi ɗakinta.

Zama ta yi ta shiga tunani. “Shin wane irin al’amari ne yake son kunno kai gidan nan? Me yasa Umma take son fifita dukiya sama da kwanciyar hankali? Ya Allah ka ganar da ita.” A ranta ta yi wannan zance kafin ta sake miƙewa ta ɗauro alwala ta fara nafilolin daren da ta saba yi.

A wannan dare ta yi tsayuwa sosai fiye da yadda ta saba yi, sannan ta yi addu’a sosai da neman taimakon Allah akan ya shigo cikin lamarin nata.

Bayan ta gama wani irin barci marar daɗi ya ɗauke ta, babu jimawa aka fara kiran sallar Asuba, nan ta miƙe. Bayan sallar gari ya fara haske, ta yi shirin makaranta ta wuce abinta.
Misalin ƙarfe bakwai na safe (7:00am) ta dawo daga makarantar. Lokacin Umma ta gama haɗa abincin karin kumallo.

Yanayin Umman ba kamar yadda ta saba ganin ta ba, sam ta ƙi sakar mata fuska. Abin da ya sa ita ma yarinyar yanayinta ya sauya, duk ta bi ta takure a wuri ɗaya. Haka nan ta ɗauki abincinta ta ɗan yatsina sama-sama. ƙarfe takwas saura kaɗan ta gama shirin makarantar boko.

To a can ma makarantar yanayin ta babu sukuni da walwala kamar kullum. Kallon ɗaya za ka yi mata ka fahimci akwai damuwa tattare da ita. Ƙawarta ce wacce ke amsa suna Safiyya Auwalu, ta dube ta ce, “Lafiya kuwa yau na gan ki babu walwala?”

Murmushi mai cike da takaici ta yi sannan ta ce, “Ba komai, jikin nawa ne dai nake jin sa ba daɗi sosai.”

“Ayya sannu fa! Ai ni da ganin ki na fahimci ba lafiya ba.”

Ɗaya ƙawar tata mai suna Hamida Ibrahim ta ce, “To me yake damun ki ne, ko za mu je asibitin makaranta ki karɓi magani?”

Zaliha ta sake yin murmushi ta ce, “Lah! Ba komai fa, ba sai na sha magani ba. Da na koma gida na ɗan yi barci shi ke nan.”

“To shike nan Allah Ya sawwaƙe.” Safiyya ce ta faɗi haka, wanda rufe bakinta ke da wuya sai sautin ƙararrawa ya fara tashi, alamar lokacin tara ya yi.

A gida kuwa hantsi na ɗagawa Umma ta shirya ta tafi gidan wata aminiyarta mai suna Yahanasu, kasancewar ta taɓa ba ta labarin wani hatsabibin boka, wanda suke cewa aikinsa kamar yankan wuƙa. Domin ita ma Yahanasun ta taɓa fafatawa da wata ‘yarta akan wanda za ta aura, kwatankwacin abin da ke shirin faruwa ne tsakanin Zaliha da mahaifiyarta.

Bayan sun gaisa ta zayyane mata duk abin da ke wakana. Ta yi shiru, zuwa can ta nisa tare da cewa, “Wai ni me yasa yaran nan ba sa nema wa kansu walwala da jin daɗi ne? Sun fi kaunar su jefa kansu cikin wahala, wajen da za su riƙa yarfarwa. To ki rabu da ita, wanda ya yi mini aiki akan Balaraba, wajensa kawai za mu je. Za a ɗauke hankalinta daga kan shi wancan faƙirin!”

Umma ta sauke aziyar zuciya ta ce, “Ai na sha alwashin sai na raba ta da shi, domin wani mutumin arziki ne ɗan mutumci, duk cikin samarin nata babu mai ƙwari sama da shi. Jiya da ya zo, ba ki ga maƙudan kuɗaɗen da ya ba wa yarinyar nan ba, amma ko kallon su ba ta yi bare ta karɓa. Haka ta shigo mini hannu na dukan cinya.”

Yahanasu ta zaro idanu cike da ɓacin rai ta ce, “Amma lallai Zaliha abin nata ya fasƙara. Kwantar da hankalinki, boka sha yanzu magani yanzu zai lanƙwasa mana ita. Yanzu ki dubi daular da Balarabar take ciki, saboda rashin kunya ita da kanta take ce mini ashe gata na yi mata da na hana ta auren Faisal Bobo, ban da ƙarya babu abin da ya ajiye.”

“Sosai ma, yo ban da shashashai ne su, wa ya ƙi ɗaki da ƙwan jimina?”

Sun jima sosai suna tattaunawa kan batun nasu na son abin duniya, daga ƙarshe suka tsayar da rana da lokacin da za su je wajen bokan.
*****

Wace Ce Zaliha?

Kamar yadda aka ji tun da farko, Zaliha yarinya ce budurwa wacce shekarunta na haihuwa ba za su wuce goma sha bakwai ba (17). Kyawu babu irin wanda ba ta haɗa ba, kama daga kyawun halitta da diri da kuma uwa uba kyawun hali. ‘Ya ce ga Malam Sirajo, wanda ya kasance ma’aikacin gwamnati da ke aiki a ƙarƙashin ma’aikatar samar da ruwan sha.

Umma Saratu ce mahaifiyarta, mace ce mai son abin duniya da son yin rayuwa ta masu farcen susa. Duk da cewa ba sa cikin rayuwa ta ƙunci, suna da abin rufin asirinsu. Komai cikin wadata suke yi, amma hakan bai hana ta nuna tsananin son masu gidan rana ba. Hakan ne ma yasa take son mayar da ‘yar tata tamkar HAJA, ta hanyar da ba ta dace ba sam! Hanya mafi muni da mutum kan rasa imaninsa, kuma a ƙarshe ya yi nadama. To Allah Ya kyauta Ya kuma ganar da iyaye masu irin bahagon tunanin.

Cigaba Labari.

A kan hanyarsu ta komowa gida ne, Umma ta ce da Yahanasu, “Watau ba a karɓar maganin gizo ke sakar ba, inda matsalar take shi ne ta yarda ta yi amfani da shi, sannan ina jin tsoron ta riƙa yin addu’o’in da ba lallai ba ne maganin ya yi tasiri a jikinta.”
“Haba don Allah! Bari wannan maganar, ita din banza. Ki zuba mata maganin a ruwan wanka ta shiga ta yi, ki jira ta har ta fito ki gani, dolenta ta yi.”

“To shike nan Allah Ya sa ta yi ɗin.”
Suna isowa unguwa suka rabu, kowa ya nufi gidansa. Har lokaci ba a tashi daga maƙaranta ba, nan da Umma ta haɗa abinci rana. Shinkafa dafa-duka ta yi ruwa-ruwa, domin ta ɓatar da maganin a ciki yadda Zaliha ba za ta gane ba. Mintuna ƙalilan da sauke abincin Zaliha ta dawo.

Zaune Umma take a falo tana cin abinci. “‘Yan makarantar bokoko, an sha rana an sha yunwa.” Cikin fara’a da zolaya Umma ta yi wannan magana. Hakan ya ba wa Zaliha matuƙar mamaki, ya ya ita ta bar gida suna zaman doya da manja, yanzu kuma ta same ta cikin fara’a da nishaɗi, har ‘yar waƙar zolaya take mata? Abin da ya kewaye mata zuciya ke nan, sai kawai ita ma saki ranta, ta yi murmushi ta ce, “Ai kam dai yau ana rana wallahi.”

“To sannu, ga abincinki nan sai a fara ta kansa tukunna.”

Ta ɗan yatsina fuska tare da cewa, “Umma ba na jin zan iya cin abincin nan ma, kaina ne ke ɗan sara mini kaɗan. Kunun tsamiya nake sha’awa.”
“Kamar ya ya ba za ki iya cin abinci ba? Ai ranar da kika shigo ce ta saka miki ciwon kan, ki ci abincin sai ki sha magani. Sannu Allah Ya sawwaƙe!”
“Amin, amma Umma kunun dai nake so, abincin nan ba zai ciyu ba. Da ma dai taliya ce ƙila na iya ci ko kaɗan ce.”
Wani irin mamaki ne ya ya dabaibaye zuciyar Umma, yarinya kamar mai aiki da ruhanai, “Ba ta taɓa yi mini gardamar cin abinci ba sai yau, komai na ba ta karɓa take kai tsaye ta ci. Yau ta yi tutsu!”

Cikin zuciyarta ta yi wannan maganar kafin ta ce, “To za ki iya zuwa ki sayo kunun? Kafin ki dawo sai na dafa miki taliyar ko?”

“E zan iya mana ai ciwon ba sosai ba ne, amma ki bar taliyar ma kawai. Kanun ya ishe ni.”

“Zaliha ba na son iyashege fa, ya ya za ki tafi makaranta tun safe ki kwaso yunwa, amma ki ce ba za ki ci abinci ba sai ruwan kunu, yo kunu abinci ne?”

Cikin murmushi ta ce, “Allah kuwa Umma ba na sha’awar komai sai kunun, idan ina so zan ci, ai ba mu taɓa yin hakan da ke ba.”

“To shike nan ai, idan ba ki ci yanzu ba, kin ci da dare, kuma tuwo ne dai.”
Dariya ta yi sosai sannan ta ce, “Umma ke nan! Kin manta ne, ai na fi son tuwon ma. Ni da a ce shi kika yi yanzun ma da ba a ji kanmu ba. Bari a jima ki gani, tuwon shinkafa na musamman zan yi mana.”

Murmushi Umma ta yi a zahiri, amma a ranta takaicin Zaliha ne ya kamata. ‘Anya kuwa za a yi nasara akan yarinyar? Anya kuwa maganin boka zai yi aiki? Ko gwadawa ma ta ƙi yi. Idan kin san wata ai ba ki san wata ba ‘yar nan!’

Haka nan ta haƙura alatilas ta ƙyale ta, domin ba ta son ta matsa mata har ta gano akwai dalilin da yasa take son sai ta ci abincin, kasancewar yarinyar na da shegen wayo da saurin fahimtar mutane.

Ko Wace Kwarya 2 >>

1 thought on “Ko Wace Kwarya 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.