A ci gaba da tattaunawa da Hikaya ke yi da shahararrun marubuta, a wannan karon mun tattauna da marubuciya Sanah Matazu inda ta haska mana abubuwa da dama da suka shafi rubutu da kuma rayuwarta. Ga yadda hirar ta kasance:
Tambaya: Da farko dai za mu so jin cikakken sunanki da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki.
Amsa: Cikakken Sunana shi ne Hassana Sulaiman Isma’il. An haife ni a shekarar 1993. Ni haifafiyar jihar Kano ce, ƙaramar hukumar Gwale a unguwar Goron Dutse. Ina da aure da yarinya guda ɗaya. Ina zaune ne a unguwar Northwest ta wurin Kabuga. Matakin karatu kuma ina karantar Hausa Education a Jami’ar Bayero.
Tambaya: A wace shekara ki ka fara rubutu? Kuma me ya ja hankalinki har ki ka fara rubutun?
Amsa: Na soma rubutu ne a shekarar 2015, sai dai ɗaukar niyyar fara rubutuna ta ɗokantu ne a raina tun ina aji shida na ƙaramar makarantar primary. Abubuwa da dama sun ja hankalina game da rubutu, sai dai babban abin da ya mayar da ni marubuciya shi ne yawaitar karance-karance mabambanta.
Tambaya: Zuwa yanzun littattafai nawa ki ka rubuta? Kuma za mu so mu ji sunayensu.
Litattafaina sun kai guda 22 wasu sun ɓata ina neman su wasu kuma na buga su, wasu kuma suna kan manhajoji mabambanta, yayinda waɗansu daga ciki suke ɓuƙatar gyare-gyare. Ga su daki-daki:
- Shi Ne Burina
- Rabi’atul Adawiyya
- Sanadin Bodin
- Yanar Gizo
- Gimbiya Zajlat
- ‘Yar Kurma
- ‘Yar Mafiya
- Ƙiyayya Ce Ko Son Zuciya?
- Mahaifiya Ce!
- Matar Saddik
- Fitsarin Fako
- Sarkakiya (Labarin Rayuwar Najwa)
- Kurman Dutse
Sai kuma waɗanda nake kan gyara labaran da ƙa’idojin rubutun cikin su, ga su kamar:
- Kaidinsu
- Yarda Ce Sila
- ‘Ƴar Fulani Ce
Sai waɗanda nake son bugawa, su ne kamar haka:
- Wata Mace
- Idan Ka Daka Ta Bado
- Kuskuren Wasu
Akwai kuma gajeru, su ne kamar haka:
- Lefan Aro
- Nadamar Rayuwata
- Hannunka Mai Sanda
Tambaya: Wanne littafi ki ka fi so a duk cikin litattafan da ki ka rubuta, kuma me ya sa?
Amsa: Na fi son Rayuwar Najwa.
Saboda wahalar da na sha wurin rubuta shi, kasancewar labarin ya shafu jinnu har tsorata ni aka soma yi akan rubutun.
Tambaya: Shin kina da Maigida ko Uwargida a harkar rubutu?
Amsa: Ba ni da ko ɗaya, sai dai zan iya cewa akwai waɗanda nake ƙoƙarin koyo daga garesu ta fannin abin da ya shige mini duhu. Kamar Muttaƙa A Hassan da kuma Jibrin Adamu Rano.
Tambaya: Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa da ya fi burge ki?
Amsa: Suna da dama gaskiya. Na marubuta yanar gizo da kuma masu bugawa, amma zan iya bugar ƙirji in ce duk litattafan Belli suna burge ni.
Tambaya: Shin kin taɓa shiga wata gasa? Idan eh ne amsar, shin ko kin taɓa yin nasara? Sannan wasu irin nasarori ki ka samu a rayuwa game da harkar rubutu?
Amsa: Na taɓa shiga gassani ba gasa ɗaya ba. Alhamdullilah a duniyar rubutu na taka nasarori da dama waɗanda har gobe ina alfahari da su a rayuwata. Babban nasarata ta farko ita zamana marubuciyar kanta. Domin burina ne.
Nasarorin da na samu kuwa ga su kamar haka:
• Gasar Tsangayar Marubuta ta ranar 30/12/2018. Gasa ta farko dana soma ci kenan a duniyar rubutu wadda aka karramani a gidan Hisbah na Kano. Wadda na karɓi kambun na uku.
• Gasar Marubuta Group Chat 4/4/2019. Gasa ta biyu dana sake ci a duniyar rubutu ita ma ta uku na zo. Na samu kyautar kuɗi naira 5000.
• Gasar Mujjalar Zauren Marubuta 18/8/2019. Gasa ta uku da na ci ita ce ta Mujallar Zauren Marubuta wadda na zo ta huɗu. Na sami kyautar kuɗi 3000.
• Gasar Gusau Institute 1/12/2021. Sai gasa ta huɗu da na ci ita ce kuma mafi ƙololuwar daraja wato gasar Gusau. Inda na samu zama zakara/kaza na lashe kuɗi naira dubu ɗari biyu da hamsin da bugaggen littafi guda goma na labarin dana rubuta wanda aka buga. Ina alfahari da gasar saboda a kaina mata suka soma karɓo kambun na ɗaya a gasar tsawon shekara biyar da soma gudanar da gasar.
• B.B.C Hausa: Sai kuma gasar da ta biyo bayan ta Gusau wato BBC Hikayata wadda na samu shiga goman farko a shekarar 2020.
Shiga ashirin da biyar ɗin farko ma babbar nasara ce ballantana kuma goman farko, wannan babbar nasara ce a gare ni tabbas domin har gida aka aiko min certificate daga Abuja.
Sau uku ina shiga sahun marubuta 25 na BBC Hausa, sau uku ina shiga Top 10 na BBC Hausa. Ina fatan kuma na shiga cikin ukun da suke da nasara idan rai ya kai mu da kuma rabo.
• The Nigeria Prize: Ita ma gasa ce da ake yi da bugaggen littafi, na samu zama ta uku a tsakanin jihohin da suka shiga gasar karon farko. Sai dai kuma su na ɗaya kaɗai suke ba wa kyauta. Shekarar da ta gabata ma na shiga ban kai matakin da suke muradi ba. Na sake komawa a 2024 shi ma dai haka. A taƙaice dai,
2021 na zo ta uku
2022 na zo ta uku
2023 na zo ta biyu.
Ina fatan a 2024 na haye siraɗin nasarar wannam gasar. Domin har yanzu ban kai matakin da suke so ba saboda su na ɗaya kaɗai suke ɗauka su ba shi kyauta. Sai dai na ji sun ce za su gyara nan gaba.
• Exquisite Competition 6/3/2022. Gasa ce ‘yar ƙarama da na samu hayewa matakin ta uku.
• Gasar yaƙi ta Mayaƙiya 2022. Na samu zuwa ta biyu a gasar rubutun.
• Gasar Kyauta Fundation ta Ilkima 2023. Na zo ta biyu a gasar.
Tambaya: To idan za ki yi rubutu, shin ki kan tsara komai da komai ne kafin ki fara ko kuwa kai tsaye ki ke farawa?
Amsa: A baya bana tsara rubutu gaskiya, kawai idan rubutu ya zo mini ina somawa ko da ban gano ƙarshen sa ba. Sai dai yanzu yadda muke ƙara tsunduma a harkar rubutu muna ƙara mu’amalantar Adabi da kuma masana. Na kan tsara ɗin idan damar hakan ta samu ko da ban sama masa ƙarshe ba. Domin wani labarin shi yake yin ƙarshensa da kansa.
Tambaya: Ya ki ke yi idan wani tunani sabo ya zo miki game da wani rubutu na daban alhalin kina tsakiyar rubuta wani. Ki kan saki wancan ne ki yi wannan sabon ko kuma sai kin gama da wanda ki ka fara?
Amsa: Bana wannan gangancin ina dai rubuta tunanin na sakaya shi zuwa lokacin da zan buƙaci aiwatar da shi.
Tambaya: Ki kan ɗauki kamar tsawon wane lokaci kina bincike kafin ki fara rubutu, kuma daga nan yakan ɗauke ki tsawon wani lokaci kafin ki kammala rubutun littafin?
Amsa: Gaskiyar magana a baya ma ni bana soma sakin littafi a yanar gizo sai na kammalashi gaba ɗaya, saboda bana so na ga ana nema. Kuma har yanzu na fi rinjaye akan wannan tsarin, sai dai yanzu duba da yanayi da sauye-sauyen hidimar rayuwa, hidimar gida da karatu ga kuma matsalar wutar Nepa ba zan iya cewa kai tsaye ina kammala rubutu a lokaci kaza ba. Amma ina ƙoƙari matuƙa wurin ganin ban ƙure haƙurin mabiyana ba.
Batun bincike kuma abu ne da ya zama wajibi ga duk marubucin da yake son rubuta abin da yake fatan ko da bayan ransa a ɗaga a yaba, duk rubutun da babu bincike shirme ne. Ina ƙoƙari matuƙa wurin ganin na binciki matsalar da na ɗora alƙalami a kanta kafin fitar da ita ga masu karatu.
Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen samun jigon labarinki?
Amsa: Jigo a rubutu kawai zuwa yake yi, domin wani jigon ma kana tafe a hanya kake samunsa. Wani kuma wata hira ce za ta ɗauki hankalinka har ka saƙa zaren labari ka samar da jigon da kake jin ya zauna maka. Wani kuma wani ne zai zo maka da matsalarsa da buƙatar ka yi rubutu akai.
Tambaya: Wacce hanya ki ke bi wajen fitar da halayen taurarinki tare da ba su sunan da ya dace da su?
Amsa: Tunani tare da nazari wurin tantance ɗabi’ar da ta kamaci a sakaɗa a jikin sunan wane. Domin akwai sunayen da suke da ƙimar da ba kowace ɗabi’a ake manna musu ba.
Tambaya: Shin ko kin taɓa amfani da wani ɓangare na tarihin rayuwarki a cikin rubutunki?
Amsa: Na taɓa.
Tambaya: Wanne littafi ne ya fi ba ki wahala daga cikin dukkan litattafan da ki ka taɓa rubutawa?
Amsa: Rayuwar Najwa
Tambaya: Wanne irin ƙalubale ki ka fuskanta a harkar rubutu, kuma ta wacce hanya ki ka bi har ki ka tsallake ƙalubalen?
Amsa: Ƙalubale kam babu.
Tambaya: A duk cikin taurarin labaran da ki ka rubuta wanne ki ka fi so, kuma me ya sa?
Amsa: Taurarin da nake so gaskiya ba ɗaya ba ne,
Shukuriyya ta cikin labarin Yarda Ce Sila, saboda gwagwarmayar rayuwarta a matsayinta na ‘yar gudun hijira.
Najwa saboda wahalhalun da ta fuskanta domin ita labarinta kusan gaba ɗaya ma gaskiya ne. Sai kuma Halimatu ta cikin labarin Fitsarin Faƙo.
Tambaya: Akan samu wani lokaci da kan marubuci ke cushewa har ya kasa rubuta komai. Shin kin taɓa shiga irin wannan yanayin? Kuma ta wace hanya ki ka bi wurin magance hakan?
Amsa: Gaskiya ban taɓa ba, amma na kan ga masu irin matsalar nan na tambayar masana. Sai dai na kan ware na zomaye ne na kwashi rumbun ilmin da ake ba su domin na san zai yi mini amfani tunda yau gareka ne gobe ga ɗan uwanka.
Tambaya: Mene ne abin da ki ka fi so game da rubutu?
Amsa: Ɗebe kewa tare da faɗaɗa tunani da kuma sauya tunanin shi kansa daga wani bigire zuwa wani bigiren da ba ma rayuwata ba.
Tambaya: Me ki kan yi a duk lokacin da ki ke da sarari?
Amsa: Na kan yi karatu. Na kan yi gyaran labarai na da suke buƙatar gyara.
Tambaya: Wace karin magana ki ka fi so? Kuma me ya sa?
Amsa: Ba kowa ne yake gane ɗingishin kwaɗo ba. Sai kuma Kiki makaka zakara mai neman suna ba da hatsi ka ci tsakuwa. Saboda suna ba ni nishaɗi tare da bayyana ma’anarsu a bigiren da na ajiye su.
Tambaya: A naki ra’ayin, tsakanin rubutun online da bugun littafi na hannu wanne ya fi? Kuma me ya sa?
Amsa: Kowanne da amfaninsa, kowanne kuma da lokacinsa. Buga littafi na ba marubuci ƙimar zama cikakken marubucin da wasu ke hasasshen bai kai ba. Sai dai kuma rubutu a yanar gizo abu ne da yake tafiya da zamani. Allah kuma shi ne zamani, don haka dole ƙanwar naƙi a amshi zamani yadda ya zo matuƙar ba zai taɓa mutuntaka ba.
Tambaya: Wanne tasiri marubuta suke da shi a cikin al’umma?
Amsa: Babbar magana. Tasirin marubuta a cikin al’umma abu ne da za mu iya kwana muna magana akai ba mu gama ba, sai dai a taƙaice zan iya cewa marubuta haske ne, kuma idaniya ne ga rayuwar al’umma.
Tambaya: Shin ko akwai wani labarin da ki ke rubutawa a yanzu haka da masoyanki za su yi tsumayin fitowarsa?
Amsa: Tabbasa akwai shi – Kundin Sanah. Wani kundi ne mai ɗauke da wasu muhimman abubuwa guda 30 wanda nake fatan ya dinga fita duk shekara da izinin Allah. Na kammala.shi har da cover ɗinsa bayar da aikin sa ne ya rage. Sai kuma Turken Jaki.
Tambaya: Wane ne tauraronki a cikin marubuta?
Amsa: Tauraro na shi ne mai ƙoƙarin samar da ci gaba a rayuwar marubuta kowaye shi.
Tambaya: Tsakanin Fim da littafi wannene ya fi saurin isar da saƙo?
Amsa: Fim.
Tambaya: Wacce irin shawara za ki iya ba wa sabbin marubuta masu tasowa?
Amsa: Su ji tsoro Allah. Su kyautata alƙalamin su. Su kaifafa tunaninsu. Tare da cire ganda waurin yin bincike kafin gudanar da rubutu. Uwa uba faɗaɗa saninsu kan Adabi da mu’amalantar masanan da suka dace.
Tambaya: Mene ne burinki a harkar rubutu?
Amsa: Samar da ci gaba tsakanin marubuta ta fuskar warware duk matsalolin da za su taso mana a iya kanmu. Wala ta fanin rayuwa ko kuma fannin rubutu. A taƙaice ina da buri kan gina wata gidauniya da za ta zamo madogara ga ɗaukacin marubuta musamman marubuta Online irina.
Tambaya: Me za ki iya cewa game da Hikaya?
Amsa: Bakandamiya! Sha kundum kenan. Sha gwagarmaya, zan iya cewa ban taɓa ganin manhaja mai ƙoƙarinta ba. Musamman wurin gudanar da aiyukanta cike da ƙarfin gwiwa ba tare da ginshira ba. Gaskiya ina jinjina musu matuƙa da gaske. Aiyuka cikin inganci tare da zaƙwaƙuran ma’aikata masu sanin ya kamata.
Wani abu mai jan hankali shi ne yadda suke ƙoƙarin buɗe account a kowa ce kafar sadarwa domin duniya ta dama da su, gaskiya ba kowa zai iya wannan ba duba da cewar aikin aiki ne na gaske. Muna fatan Allah Ya ci gaba da dafa musu tare da ƙarfafa musu gwiwar gudanar da duk wani abu da ya kamata.
Amin. Mun gode sosai.
An yi wannan hira da Sanah Matazu ne a ranar 19 ga watan Maris, 2024.
Tsara tambayoyi da gabatarwa: Jamilu Abdulrahman (Haiman Raees)