A maƙalunmu na baya, mun tattauna akan abubuwan da suka zama muhimmai marubuci ya sani wajen gina farko-farkon labari, misali gina jigo, salo da makamantansu. Kafin mu ci gaba da abubuwan da suka shafi tsakiyar labari, bari mu duba wani muhimmin abu – zurfafa bincike wajen gina labari.
Kamar yadda muka sani bincike wata hanya ce da ake bi wajen neman sanin abin da ba a sani ba, ko kuma ƙara wa kai sani akan abin da ba a yi masa sani na haƙiƙa ba.
Bincike don gina labari ya ƙunshi duk wasu bayanai da marubuci zai tattaro ya tsara su ya yi amfani da su wajen gina labarin. Dolen kowanne marubuci ne ya riƙa yawaita bincike a kan dukkan abin da yake rubutawa, idan kuwa ba haka ba to tabbas zai yi danbarwa. Marubuci ya riƙa sakawa a ransa cewa rubutun da zai yi rubutu ne da kowa zai iya karantawa tun daga kan mai’ilimi da jahili, babba da kuma yaro, malamai da ɗalibai, idan kuwa haka ne dolen shi ne duk abin da zai rubuta ya tabbatar daidai ya rubuta.
Mutunci, ƙima da kuma darajar rubutun marubuci tana zubewa a ƙasa wanwar a duk lokacin da ya tafka wani gingimemen kuskure yake kuma da’awar daidai ya yi a cikin labarinsa. Kowa ya san marubuci ba likita ba ne amma kuma idan wani marubucin ya yi maka rubutu a kan aikin likita sai ka ɗauka wani shugaban likitocin duniya ne saboda tsabar binciken da ya yi wajen rubutun nasa, don haka ko likita ne ya karanta labarin ba zai taɓa ganin makusa ba a rubutun balle har ya kushe masa.
Na taɓa faɗa a wata tattaunawa da aka yi da ni cewa akwai wata marubuciya da ta taɓa yin rubutu a kan shari’a, rubutun nata ya samu karɓuwa sosai musamman a wurin mata, sai dai kuma ga duk wanda ya san ilimin shari’a ba zai taɓa ɗaukar littafin da daraja ba, don kuwa rashin bincike ya sa ta yi wa doka karantsaye, shi kansa tauraron littafin ta saka shi ya aikata laifin da hukuncinsa shi ne kisa kai tsaye a musulunce da kuma tsarin doka irin ta kundin ƙasa.
Amma saboda rashin bincike ta wanke tauraron da molanka ba tare da ta kashe shi ba, wanda hakan kuskure ne, don kuwa tana nuna wa masu karatu su ma su je su aikata irin wannan laifin ba za’a kashe su ba, za’a yi musa hukunci irin na tauraron labarinta.
Kamar yadda na faɗa marubuci zai iya zama likita da zai faɗa wa jama’arsa cuta da kuma maganin ta, marubuci zai iya zama malami da zai faɗa wa jama’arsa abin da Allah Yake so da wanda ba Ya so, marubuci zai iya zama Alƙali da zai sanar da jama’a doka da laifuffuka ya kuma sanar da su hukuncin kowanne laifi ta yadda zai zamana darasi ga wanda yake tunanin aikatawa ya fasa kada shi ma a yi masa irin hukuncin da aka yi wa tauraron labarin marubucin. Sai dai fa duk hakan zata faru ne idan marubucin ya yi bincike.
Ta hanyar bincike ne marubuci zai zama shakundum, ya zama komai da ruwanka ta yadda zai iya yin rubutu a kowanne fanni kuma rubutun ya ƙayatar da duk wanda ya karanta.
Hanyoyin yin bincike suna da yawa, kuma kowacce marubuci ya bi ta yi, to amma akwai manya-manyan hanyoyi guda uku da suke gaba da sauran waɗanda ya kamata mu tattauna a kan su yanzu.
Tuntuɓar masana
Hanya ta farko ita ce ta hanyar tuntuɓar wani masani a kan maudu’in da za ka yi rubu a kai, wannan hanyar ta fi kowacce hanya kai waye don kuwa a cikinta ba a fiya samun matsala ba tunda tattaunawa ce ta baki da baki, fuska da fuska, ka kuma tambayi duk abin da ya shige maka duhu. Idan kana so ka yi rubutu ne a kan shari’a to yana da kyau ka samu wani lauyan ko alk’ali ko kuma wani mai ilimi a kan shari’a ya yi maka bayani musamman ma akan wani hukunci da kake son yi a cikin labarin. Idan an yi tattaunawar ta waya ma hakan babu laifi.
Idan a kan wani kasuwanci za ka yi rubutu a matsayinka na marubuci, yana da kyau ka samu irin wannan ɗan kasuwar ka samu ilimin hanyar kasuwancin a wurinsa, don gudun kada ka yi rubutun da duk wanda ya san irin wannan kasuwancin zai yi maka dariya da zarar ya karanta rubutun saboda kuskuren da ka tafka.
Idan a asibiti ne ka nemi likita, idan a makaranta ne ka nemi malami ko lakcara, idan a kan tsaro ne ka nemi ɗan sanda da sauran jami’an tsaro, idan a kan tarihi ne ka nemi masanin tarihi ko tsoho da dai duk sauran wanda ka san rubutun naka ya shafe su.
Nazarin littattafai
Hanya ta biyu ita ce ta hanya bincikar wasu littattafai da suka shafi abin da za ka yi rubutunka a kai, ka duba duk wani muhimmin batu da kake so ka sani.
Nema a yanar gizo
Hanya ta uku ita ce ta yin bincike a yanar gizo (Internet) ka nemi duk abin da kake nema, yawanci kuma wannan hanyar an fi yin amfani da ita idan ana son a yi bincike na gaggawa, ko kuma binciken wani wuri da ya yi maka nisa (kamar ƙasar waje), ko kuma binciken abubuwan da ba ka da sukunin mallakarsu.
Yanayin sauyawar zamani ya sa wannan hanyar ta fi kowacce hanya sauƙi a duk hanyoyin yin bincike, domin kuwa ko nan Bakandamiya ta ishe mu abar misali. Dukkan waɗannan muƙalun tun daga jigon labari da duk sauran muhimman abubuwa da suka shafi Adabi idan marubuci ya bincika zai samu, ga shi kuma kullum ƙara ɗora sababbin abubuwa ake yi ta yadda za a ce kusan komai za a samu. Muhawara mai ma’ana wacce sai mutum ya share kwanaki yana tsarata ne idan shi zai rubuta, kawai zai sameta cikin sauƙi a shashin muhawara na Bakandamiya, banda sauran fannoni na ilimi sosai iri-iri.
Shi ya sa a wurina ba zai zama uziri ba ga marubuci ya riƙa yin rubutu karazube babu bincike, domin kuwa duk wani ilimi da yake nema idan ya bincika zai samu. Zan rufe maƙalar tamu ta yau da maganar Nelson Mandela da ya ce “Ilimi shi ne makami mafi ƙarfi ko tasirin da za a yi amfani da shi a canza duniya.” A ra’ayina marubuci shi ya fi kowa kusanci da wannan maganar, domin kuwa marubuci ne yake amfani da baiwa da iliminsa wajen canza wa duniya tunani ta hanyar rubuce-rubucensa, shi kuwa ilimi yana samuwa ne ta hanyar bincike, don haka yana da kyau mu riƙa yin bincike.
Ku duba wannan makala da ta yi nazari akan salon bayar da labari.