Tun muna yara ƙanana ake karanta mana labarin da ke littafin Iliya Ɗan Mai Ƙarfi wanda Malam Ahmadu Ingawa ya rubuta kuma kamfanin Gaskiya Corporation ya soma wallafawa a 1951. An ci gaba da wallafa a littafin ƙarƙashin kamfanin NNPC a shekarun 1976 da 1980s har zuwa wannan lokaci da muke ciki ana ci gaba da wallafa shi.
Littafin na ƙunshe da labarun nishaɗi na jarumtaka da ƙuru da soyayya da ban al’ajabi da kuma ban tausayi. Marubucin littafin na Hausa, ya bayyana cewar ya rubuta shi ne domin mai karatu ya samu abokin hira daga hiƙayoyin mutanen da suka shuɗe.
Littafin na ba da labarin wani mutum ne mai suna Iliya wanda iyayensa talakawa suka haife shi a gidan gona. Bayan ya isa yaye, sai ciwon shan Inna ya kama shi. Ya zamana ba ya ko iya motsawa daga gadon da yake. Wata rana sai baƙi suka ziyarci gidan, alhali iyayensa ba sa nan. Da suka nemi ya ba su ruwa ko wani abinci sai ya nuna musu cewar ba shi da lafiya. Don haka suka yi masa addu’a a cikin abin sha. Nan take da ya sha jikinsa yayi kyau har ya miƙe tsaye.
Mutanen nan suka umarce shi da ya tafi zuwa birnin Ƙib domin kawar musu da wani mugun dodo mai suna Gogaji. Bayan ya aiwatar da wannan aikin, sai kuma ya shiga duniya yayi ta bugawa da masu ƙin gaskiya, da ma shi ɗan gwagwarmaya ne. Haka dai har zuwa lokacin da yaƙi ya tasowa mutanen Birnin Ƙib, sarki Waldima, wanda ya sa aka binne shi a wani rami amma matarsa watau Sarauniya ta yi dabara ta haƙa rami tana kai masa abinci a ɓoye. Lokacin da Waldima ya ga yaƙi ya doso su gadan-gadan, sai ya rasa inda zai sa kansa. Ya shiga ɗaki yayi ta rusa kuka. Ganin haka Sarauniya ta shawarce shi da ya sa a tono Iliya ko da ransa ya taimaka musu. Bayan jayayya tsakaninsu, sai Sarki Waldima ya amince aka tono Iliya. Abin mamaki, sai ga shi nan kwance kan gado lafiya lau. Har ma ya ƙara ƙiba da haske.
Sarki Waldima ya nemi afuwar Iliya sannan ya sanar da shi halin da Birnin Ƙib ke ciki. Iliya ya ɗebi askarawa goma suka shiga cikin dubunnan abokan gaba, cikin ƙanƙanin lokaci suka karkashe su. Sai dai babu jima sai abokanen gabar suka tashi tangaram kamar ba su aka karkashe ba. Ganin haka askarawan nan goma suka koma fagen daga, amma Iliya bai shiga ba. Sai ya tafi can kan dutse shi da dokinsa Ƙwalele, ya zurfafa cikin tunani da dogon nazari har bai san lokacin da ransa ya fita ba aka mai da shi dutse.
Marubucin ya ƙarƙare labarinsa da cewar, “ko yanzu idan ka je Birnin Ƙib za ka iske Iliya da dokinsa a cikin siffar dutse.”
Tsittsigen littafin
Bisa binciken da muka yi, littafin Iliya Ɗan Maiƙarfi na da asali daga tatsuniyoyi da labaru na mutanen Rasha. Masu nazari sun bayyana cewar labarin Iliya daga wata tsohuwar tatsuniya ce mai suna Bylina. Ita wannan tatsuniya, ana rera ta ne kamar waƙa, a ciki ake ambaton manyan gwarazan ƙasar Rasha da irin gwagwarmayar da suka yi a zamaninsu. Yawanci labarun da ke ciki suna cike da kururutawa da zuzutawa da kambamawa. Wasu labarun ma ba su faru ba, haka dai ake rera su domin nishaɗi.
Tatsuniyar Iliya ta Belina, tana bayyana cewar ya kasance ɗaya daga manyan dakarun da aka taɓa yi a yankin wanda ake kira ‘Bogati’ (bogatyr), watau jarumin mutum mai iya gwabzawa da dubunnan dakaru kuma ya karya su.
Aka ce, lokacin da aka haife shi ya samu karaya a ƙashin bayansa, don haka ba ya iya tafiya ko’ina. A haka har ya shekara 32 a duniya. Wata rana wasu masu yawon wa’azi suka kawo ziyara garinsu mai suna Morum. Lokacin kuwa wasu arna da ake kira Tugar sun tarwatsa garin sun kama na kamawa sun kashe na kashewa. Raunana da tsofaffi irin su Iliya da iyayensa ne kaɗai suka rage. Su ma ba sa nan suna gona suna ta aiki.
Baƙin suka iske Iliya shi kaɗai zaune a kusa da ɗakin girki yana shan ɗumi. Bayan sun fahimci irin naƙasar da yake da ita sai suka ba shi wani ruwa ya sha. Nan take ya miƙe tsaye. Suka cigaba da zazzaga masa ƙarfi har ya zama yana jin kansa kamar shi ne Sibyatogo (Svyatogor, shi ne watau Wargaji a littafin Iliya ɗan Maiƙarfi). Shi Sibyatogo saboda tsananin ƙarfin da yayi masa yawa har ƙasa ba ta iya ɗaukar sa. Saboda haka, sai ya hau kan tsauni ya ba wa wasu matafita takobinsa. Yayi musu wasiyyar su ba wa wani da zai gaje shi nan gaba. Shi kuma nan take ya zama dutse.
A wata faɗar kuma, aka ce matafiyan sun gargaɗi Iliya da kada ya kuskura yayi faɗa da wani mai suna Sibyatogo. Wai shi kaɗai ne duk duniya zai iya galaba akansa. Sai dai zuciya ta fisgi Iliya ya tarar da shi yana barci ya kabra masa takobi sau uku amma bai ko yi motsi ba. Can dai sai ya miƙa hannu ya kamo Iliya ya jefa cikin aljihunsa. Nan fa Iliya ya ji kamar an jefa shi wata rijiya mai zurfi. Don haka ya nemi afuwa suka shirya. Suna tafiya sai suka ga wani ƙaton akwati. Iliya ya shiga ciki ya kwanta amma ko kamu ɗaya bai cika ba. Sai Sibyatogo ya shiga. Nan da nan akwati ya rufe da shi. Da ya ga lallai ba zai kuɓuta ba, sai ya jefowa Iliya takobinsa sannan ya huro masa dukkan ƙarfinsa. An ce wasu mutane a ƙasar Belarus da Ukrain da sauran yankunan tsohuwar Rasha yanzu haka suna bautar akwatin Sibyatogo. Sunan addinin nasu Rodnovery.
Mu dawo zancen mu. Lokacin da ya ji ƙarfi yayi masa yawa, sai matafiyan nan da suka warkar da shi suka yi masa umarnin ya tafi wajen Sarki Vladimir Krasnoye Solnyshko mai mulkin Kiev domin ya ceci al’ummar daga sharrin wani dodo mai suna Idolishche Poganoye wanda yake kashe mutane da ihunsa.
A birnin Kiev aka naɗa shi sarautar shugaban askarawa. Ya zamana suna kare Rashawa daga harin abokan gaba. A cikin wannan arangamar wata rana mayaƙa suka kawo hari, suka kama wata ‘yar sarauta mai suna Vassilisa. Ilya ya hau tare da sauran abokansa, Dobrynya Nikitich da Alyosha Popovich. Anan suka yi nasara suka halaka mutane da yawa. Sai kuma soyayya ta ƙullu tsakanin Iliya da gimbiya Vassilisa. Bayan wani lokaci ta yi ciki. Sai dai Iliya ba shi da lokacin da zai zauna cigaba da kula da ita. Don haka ya yi wasiyyar idan namiji ne ta sa masa suna Sokolnichek. Watau ‘Falcon’ da turanci.
Wata rana Sarki Tugar mai suna Tsar Kalin ya fusata ya shirya wani gagarumin yaƙi domin murƙushe birnin Kiev. Ya sa musu sharaɗin su biya shi harajin zinariya zambar dubu bakwai idan suna son kansu da arziki. Lokacin kuwa Ilya sun ɓata da Sarki Viladimir har ya sa an ɗaure shi tsawon shekara goma ba ci ba sha a kurkuku sakamakon wani sharri da waziri Mishatychka ya ƙulla masa.
Sarki Viladimir ya sa a duba ko Iliya na da rai, sai aka gan shi cikin ƙoshin lafiya, ga abinci nan iri-iri gabansa. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon wani adikon sihiri da matarsa ta taɓa ba shi. Cikin hanzari Sarki Viladimir ya nemi afuwa. Iliya ya yafe masa. Aka shiga shirin yaƙi.
Can gefe guda kuma Sarki Tsar ya kama sarauniya Vassilisa tare da ɗanta. Har ma ya koyawa ɗan nata yaƙi ya zama gagara gasa. A fitowa ta farko sai ya aiko shi domin ya yaƙi Iliya. Bai sani ba ashe shi ne mahaifinsa na gaskiya. Bayan sun yi karon battar ƙarfe ne Iliya ya gane shi ta hanyar zoben da ya gani a hannunsa. Yaro ya gane mahaifinsa da irin shaidar da mahaifiyarsa ta sanar da shi. Nan da nan suka shirya. Suka tunkari abokin gabarsu watau Sarki Tsar.
An kai ruwa rana da bata kashi sosai har Iliya da ɗansa da taimakon wani masassaƙi mai suna Razumey suka karya rundunar Tsar kuma suka kashe shi. Sarki Viladimir da mutanen Kiev suka yi ta murna. Nan take Sarki Viladimir ya yi masa tayin matsayin waziri a fadarsa, amma Iliya ya ƙi karɓa. Ya zaɓi ya koma gidan gona shi da matarsa su ci duniyarsu. Ya danƙawa ɗansa Sokolnichek takobin Sibyatogo domin shi ma ya cigaba da gwagwarmaya kamar yadda ubansa yayi.
Tatsuniyar ta ƙare da cewar Iliya ya cigaba da zama da iyalinsa yana taɓa noma yana taɓa yaƙi har wata rana da tsufa ya cimmasa ya gina wani katafaren ɗakin bauta (coci) a garin Pechersk Lavra da ke birnin Kiev. Ya cigaba da wa’azi har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Tasirin tatsuniyar Iliya
Tatsuniyar Iliya ta yi tasiri sosai a sassan duniya musamman wuraren da ake son motsa jarumtaka ko soyayya ko taimakon al’umma. Ƙasar Rasha ta gina wani jirgi mai suna Skorsky Ilya Morumet wanda take taƙama da shi a yaƙin duniya na ɗaya. Haka nan a Amerika an yi wani fim a 1956 wanda ake kira Ilya Morumets of Morum. Littafin Iliya ɗan Maiƙarfi na daga cikin manyan ayyukan da ake ambatawa cewar suna da asali daga wannan tatsuniyar.
Masu binciken tarihi a Rasha da kewaye suna ta tono abubuwa da dama da suke cewa suna da alaƙa da wani ɓangare na abin da tatsuniyar ke ambatawa. Misali, a shekarar 1988, wasu ƙwararru masu binciken tarihi suka tono wani ƙashin baya a yankin Kiev. Suka yi aune-aune suka ce mamallakin ƙashin mutum ne dogo ƙaƙƙarfa, kuma da alama yayi fama da ciwon ƙashin baya a lokacin da yake yaro ƙarami. Sai dai ba su ambaci sunan kowa ba, amma sai mutane suka tafi akan cewar Iliya na ƙauyen Morum ne.
Kai oga mun gode sosai da wannan
Muna matukar godiya da wannan tsokaci, a matsayina na ɗalibin Ilimi a Harshen Hausa, gaskiya na ƙaru sosai…
09035820560
Ina da wasu shawarwari akan wannan da ire-iren su. Ku tuntubeni a email.