Gasar Hikayata ta BBC Hausa gasa ce ta rubutun ƙagaggun gajerun labarai wacce ake gudanar da ita duk shekara. An ƙirƙiro gasar Hikayata ta BBC Hausa ne a cikin watan Yulin 2016, kuma aka fara karɓar labaran a ranar 1 ga watan Agustan 2016. Ana gudanar da wannan gasa ne a tsakanin marubuta mata zalla, ban da maza.
Wannan wani yunkuri ne na bai wa mata damar nuna irin basirar da Allah ya hore musu wurin rubutu da kirkirar labari. Editan Sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, ya bayyana cewa, “A baya mata a nahiyar Afirka sun yi fice wurin bayar da kagaggun labarai da kuma tatsuniya da sauransu”.
Amma lamarin ya sauya, musamman a kasar Hausa, tun bayan wanzuwar karatun boko. Wannan gasa za ta taimaka wurin bunkasa rubutu a tsakanin mata da rage irin giɓin da ke tsakaninsu da maza, wanda rashin daidaito wurin samar da ilimi ya haifar.

Waɗanda aka yarda su shiga gasar
Kamar yadda aka ambata cikin gabatarwa Gasar Hikayata ta sashen Hausa na gidan rediyon BBC Hausa, gasa ce ta mata zalla babu maza, mata kaɗai aka sahalewa bajekolin basirarsu.
Me yasa mata kaɗai?
An ƙirƙiri gasar ne domin ba wa mata damar fito da damuwar da take ƙunshe a ransu, ta hanyar rubutu tare da ba su damar da za su janyo hankulan al’umma kan matsalolinsu da kuma samar da mafita a tare da su. Haka nan gasar na da nufin cike giɓin ilimi da ke tsakanin mata da maza a yankunan Hausawa na duniya.
Shin matan aure ko ‘yan mata?
Gasar Hikayata ta BBC Hausa ba ta bambance matan aure ko kuma ‘yanmata ba, an dai ware jinsin mata kaɗai domin ba su wannan dama. Sai dai kuma a kwai gejin shekarun na shiga gasar. Sai mutum ya kai shekaru 18 zai iya shiga, kuma idan ya haura 35 ba zai iya shiga ba.
Jerin sunayen gwarazan Hikayata da labaransu tun daga 2016 zuwa 2024
1. Zakarun shekarar 2016
- Mataki na ɗaya: Aisha Sabitu (Sansanin Yan Gudun Hijira)
- Mataki na biyu: Amina Hassan Abdusslam (Sai Yaushe?)
- Mataki na uku: Amina Gambo Adam Kwaru (In Da Rai)
2. Zakarun shekarar 2017
- Mataki na ɗaya: Maimuna Idris Sani Beli (Bai Kai Zuci Ba)
- Mataki na biyu: Bilkisu Sani Makaranta (Zawarcina)
- Mataki na uku Habiba Abubakar da, Hindatu Sama’ila (Sana’a)
3. Zakarun shekarar 2018
- Mataki na ɗaya: Safiya Abubakar Jibrin (‘Ya Mace)
- Mataki na biyu Sakina Lawan: (Sunanmu Ɗaya)
- Mataki na uku: Bilkisu Muhd Abubakar (Zaina)
4. Zakarun shekarar 2019
- Mataki na ɗaya: Safiya Ahmad Kaduna (Mairaici)
- Mataki na biyu: Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo (Ba Ayi Komai Ba)
- Mataki na uku: Jamila Babayo (A Juri Zuwa Rafi)
5. Zakarun shekarar 2020
- Mataki na ɗaya Maryam Umar (Rai Da Cuta)
- Mataki na biyu: Surayya Zakariyya Yahya (Numfashin Siyasata)
- Mataki na uku: Rufaida Umar Ibrahim (Farar Ƙafa)
6. Zakarun shekarar 2021
- Mataki na ɗaya Aisha Musa Dalil (Haƙkina)
- Mataki na biyu Aisha Hamisu Maraɗi (Butulci)
- Mataki na uku Zulaihat Alhassan (Ramat)
7. Zakarun shekarar 2022
- Mataki na ɗaya: Amira Souly Maraɗi (Garar Biki)
- Mataki na biyu: Hassana Labaran (Haihuwar Guzuma)
- Mataki na uku: Maryam Muhd (Al’ummata)
8. Zakarun shekarar 2023
- Mataki na ɗaya: Aisha Adamu Hussaini (Rina A Kaba)
- Mataki na biyu:Aisha Abdullahi Yabo (Baƙin Kishi)
- Mataki na uku: Aisha Abdullahi Jos (Tuwon Ƙasa)
9. Zakarun shekarar 2024
- Mataki na ɗaya: Hajara Ahmad Hussain (Amon ‘Yanci)
- Mataki na biyu: Amrah Auwal Mashi (Kura A Rumbu)
- Mataki na uku: Zainab Chibaɗo (Tsale Ɗaya)

Jigogin laraban da suka yi nasara daga 2016 zuwa 2024
Shekarar 2016
1 – Gudun hijira
2 – Lalata yara da ba su ƙwayoyi
3 – Rashin ilimi
Shekarar 2017
1 – Fatalwa da ƙawance da kuma kishi
2 – Zawarci
3 – Sana’a
Shekarar 2018
1 – Jinkirin aure
2 – Fariya da kyawu
3 – Ɓatan miji/Soyayya/Alƙawari
Shekarar 2019
1 – Maraici
2 – Haihuwar ‘ya’ya mata
3 – Fyaɗe
Shekarar 2020
1 – Korona
2 – Siyasar mace
3 – Farar ƙafar
Shekarar 2021
1 – Fyaɗe
2 – Garkuwa da mutane
3 – Fyaɗe
Shekarar 2022
1 – Garar biki
2 – Burin auren mai kuɗi
3 – Siyasar mace
Shekarar 2023
1 – Maganin mata
2 – Kishi
3 – Auren miji ɗan son banza
Shekarar 2024
1 – Zanga-Zanga.
2 – Cin amanar aure da garkuwa da mutane.
3 – Garkuwa da Mutane.

Wasu gasanni makamantan BBC Hausa Hikayata
Gasar Gusau Institute
Gasar Gusau gasa ce ta rubutun ƙagaggun labaran zube da aka samar a tsakanin marubuta maza da mata. A gudanar da ita a kowace shekara, inda Alkalai kan bi diddigi wajen zaɓar labarai uku da suka fi cancanta domin ba su shaidar karramawa da kuma ɗan abin da zai ƙara musu ƙarfin gwiwa da karsashin rubutu. Bayan mutane uku akan ware mutane goma a ba su shaidar shiga gasar (satifiket).
Gasar Gajerun Labarun ta Leadership Hausa
Ita ma jaridar Leadership Hausa ta bi sahun takwarorinta wajen ƙirƙiro gasar rubutun ƙagaggun labaran. An kirkiro gasar ne albarkacin ranar masoya ta duniya da Hukumar kula da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta fitar da 14, ga watan Febarairun kowacce shekara a matsayin ranar masoya ta duniya. An dai fara wannan gasa ne a watan Fabrairun 2025. Ita dai wannan gasa ta rubutun ƙagaggun gajerun labaran soyayya ce zalla kamar yadda jaridar Leadership ɗin ta bayyana.
Gasar Arc. Ahmad Musa Dangiwa
Gasar rubutun ƙagaggun gajerun labarai ta Arc. Ahmad Musa Dangiwa, gasa ta shekaru-shekara wacce ke ba marubuta maza da mata dama su barje gumi wajen samar da nagartattun labarai.Wannan gasa wata dama ce da za ta taimaka wajen bunkasa rubutaccen adabin Hausa da ya danganci gajerun labaran zube na Hausa, a karkashin jagorancin Arc. Ahmad Dangiwa, bisa manufofin babban bankin bayar da lamuni don gina gidaje na Kasa.
Gasar Hukumar Tace Fina-finai Da Ɗab’i ta Kano
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano ta shirya gasar rubutun ƙagaggun gajerun labarai ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Abba El-Mustapha, a karon farko a 2024. Ana sa ran gasar za ta ci gaba da gudana duk shekara domin ƙarfafa gwiwar marubuta.
Tsokacin masana game da gasar
Akwai wasu matsololi da suka yi wa gasar ƙawanya waɗanda suke haifar da cece-kuce da korafe-korafe daban-daban musamman a shekarun farko-farko na ƙirƙirar gasar daga mabambantan mutanen da suka haɗa da masana harkokin addinin Musulunci da masu sharhi da nazarin duniyar adabin Hausa har ma da marubutan Hausa maza. Ga ra’ayoyin kowane rukuni game da gasar:
Masana addinin Musulunci
Waɗannan rukunin mutane sun rika jefa ayar tambaya da zargi kan BBC Hausa, a cewarsu gidan rediyon ya kirkiro da wannan gasa ga mata zalla ne don zuga mata da gurɓata musu tunani domin su rika yin kafaɗa da kafaɗa da maza a matsayin masu ’yancin bai-ɗaya. Yayin da wasu suka zafafa da cewa ta hanyar wannan gasa, ana son a tunzura mata su rika gudun kishiya da haihuwar ’ya’ya da yawa da sauransu. Wasu kuwa sun tafi a kan fahimtar cewa ta hanyar wannan gasa, BBC Hausa na yin leken asiri ne, ta yadda suke tattara bayanai suna aika wa Birtaniya, domin amfani da su nan gaba wajen cim ma mummunar manufa game da al’ummar Hausa da addinin Musulunci.
Masu sharhi kan adabin Hausa
Wasu daga cikin masana adabin Hausa sun yi korafin cewa don me BBC Hausa ta zaɓi nau’in rubutun zube kawai a wannan gasa, bayan akwai sauran rukunan adabi rubutu da ya kamata a faɗaɗa su, hasali ma shi ɓangaren zube yana da wadatattun rubuce-rubuce? Har ila yau sun ƙara jefa ayar tambaya ga BBC Hausa cewa, shin me ya sa tun tsawon shekarun da aka ɗauka ana aiwatar da gasar, amma ba a taɓa wallafa littafi ko ɗaya daga ɗimbin labarun da aka tattara ba?
Wasu daga cikin wannan rukuni da suka yi nazari da bibiyar gasar tun a farko-farko, sun yi amannar cewa ba don kishin harshen Hausa aka kirkiro gasar ba, sai don wata manufa ɓoyayya. Sun kafa hujja da cewa, a yayin bikin karrama zakarun gasar, BBC Hausa ba ta amfani da harshen Hausa yadda ya kamata a yayin gudanar da bikin tun daga farko har karshe. Ta yaya sashen Hausa zai shirya gasar rubutun Hausa, ya kira taro amma ba za a yi amfani da Hausa zalla ba?
A cewar masu kishin Adabin Hausa, ya kamata BBC Hausa ta riƙa canja nau’in gasar zuwa Wasan Kwaikwayo da Waƙe, ba Zube kadai ba. Kuma ya kamata a rika wallafa fitattu daga cikin labarun da aka tattara zuwa littafi. Domin mutane za su samu abin karantawa yayin da manyan makarantu da ƙanana za su samu abin nazari. Daga ƙarshe kuma ya kamata a rika amfani da harshen Hausa zalla a dukkan abin da ya shafi gasar, wanda haka zai ƙara ƙima da darajar harshen a idon duniya.
Marubuta maza
Wasu daga cikin marubuta maza sun yi ta kumfar baki da tayar da jijiyar wuya, suna korafin cewa don me babbar kafa ta duniya kamar BBC Hausa za ta nuna masu wariyar jinsi? Ta ya ya za ta fito da babbar gasar da ta shafi fasaha, ilimi, fikira, ƙirƙira amma ta zab’i Mata kaɗai, ta hana Maza tsunduma a fafata da su? A cewar irin waɗannan marubuta maza, duniya gabaɗayanta tana tafiya ne bisa cuɗanya tsakanin maza da mata, don haka duk wani abu da za a yi, musamman ma da ya shafi harkar ilimi da faɗakarwa, ya zama wajibi ya ƙunshi dukkan jinsin biyu. Wato idan an ba mata dama, to su ma maza ya kamata a ba su tasu damar. Don haka ya kamata a ce wannan gasa an buɗe ta ga maza da mata, kowa ya nuna tasa fasahar.
Game da wannan buƙata ta marubuta maza, ɗaya daga cikin editocin Sashen Hausa na BBC ya taɓa shaida wa wakilin jaridar Aminiya cewa, ɗaya daga cikin manufar BBC Hausa dangane da wannan gasa da aka keɓance ta ga mata shi ne domin janyo hankalin mata da matasa su rika sauraren tasharsu, a bincikensu, sun gano cewa wannan duniyar ta zamani, matasa da mata ne suka fi yawa.
Kammalawa
Babu shakka wannan gasar ta haifar da cigaba ta fuskoki da daban-daban kama daga bunƙasa adabin ta hanyar samar da ingantattun labarai waɗanda suka haska ɓoyayyun matsalolin mata da matasa, inganta rayuwar gwarazan ta hanyar samun ayyukan yi da ci gaba da karatunsu, wasu sun samu guraben karo karatu a jami’o’i, wasu sun samu ayyukan yi a cikin ma’aikatun gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu, yayin da wasu suka mallaki jari suka kafa sana’o’i daban-daban.
Ƙalubalen da ke tattare da gasar kuma, akwai bukatar sashen Hausa na BBC ɗin su kalle tare da magance su, musamman taƙaita gasar ga jinsi ɗaya (mata). Lallai akwai bukatar faɗaɗa gasar zuwa kan maza domin samar da ƙarin ilimi da hanyoyin warware matsalolin rayuwa har ma da bunƙasa harshen Hausa. Har ila yau akwai bukatar a riƙa taɓa sauran rukunonin adabin wato wasan kwaikwayo da waƙe.
Manazarta
BBC News Hausa. (2016, July 26). Gasar Hikayata ta mata zalla. BBC Hausa
Fagge, K. Y. (2020, July 6). Gasar rubutattun gajerun labaran Hausa ta Arch. Ahmad Musa Dangiwa
Malumfashi, B.Y. (2019, May 31). Tsokaci da sharhi game da Hikayar Mata. Aminiya